✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron zaman lafiya na Kongo ya watse

Shirin kawo zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da Gwamnatin Dimokuradiyyar Jamhuriyar Kongo, ya watse, a daidai lokacin da aka kasa cimma matsaya kan irin…

Mata da yara na jiran agajin abinci a kasar KongoShirin kawo zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da Gwamnatin Dimokuradiyyar Jamhuriyar Kongo, ya watse, a daidai lokacin da aka kasa cimma matsaya kan irin afuwar da ya kamata ayi wa ’yan tawayen, sannan su ajiye makamansu, a kuma shigar da su cikin jami’an tsaro. ’Yan tawayen na M23 sun ki amincewa da yarjejeniyar da aka tsara, a cewar jakadan Majalisar dinkin duniya.
Mary Robinson, Jakadiya ta musamman ga Majalisar dinkin Duniya a Afrika ta tsakiya, ta bayyana wa majalisar tsaro ta kasar Kongo cewa Gwamnatin Kongo da ’yan tawayen M23 sun kulla yarjejeniya a kan al’amura 12, a wani kundin tabbatar da zaman lafiya da aka rattaba wa hannu, kuma sun manince “su sake yin taron a wata rana don warware bambance-bambance da ke tsakaninsu.
Shi kuwa Martin Kobler, wakilin kasar Kongo a majalisar dinkin Duniya, ya nuna takaicinsa, kan yadda aka shafe kwana hudu ba a cimma matsaya ba, amma ya ce “ina da kwarin gwiwar za a iya cike gibin da ke tsakaninmu.”
’Yan tawayen Kongo, sojoji ne daga kabilar Tutsi, wadanda suka fice daga rundunar sojan kasar, bayan sun zargi gwamnatin da cin amanarsu wajen kin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2009. Wannan yarjejeniya da aka fara a Kampala babban birnin Uganda ta tsaya cik.