✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashar Tekun Tudu ta Kaduna za ta samar da ayyuka dubu 40- Ministan Sufuri

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Sabon Tsarin Tasoshin Teku na Tudu wato ‘Inland Dry Ports’ za su taka rawa wajen kara hakaka tattalin…

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Sabon Tsarin Tasoshin Teku na Tudu wato ‘Inland Dry Ports’ za su taka rawa wajen kara hakaka tattalin arzikin kasa a Najeriya musamman a Arewa, yayin da tashar Kaduna kadai za ta samar da ayyukan yi fiye da dubu 40.
Ministan ya fadi haka ne a yayin kaddamar da fara jigilar kwantenoni daga kasashen ketare zuwa Kaduna a ranar Talatar da ta gabata a Kaduna wanda ya samu wakilcin Daraktan Gudanarwa na Ma’aikatar, Alhaji Sani Galadanci.
Ya ce wannan nasara ta samar da tashoshin teku na tudu ta hanyar amfani da jiragen kasa, ta tabbata ne bisa kokari tare da jajircewar wannan gwamnati ta Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, don inganta harkokin sufuri da suka kunshi hada-hadar kasuwancin shige da fice a Najeriya.
A cewarsa, “tashoshin tekun na tudu wasu hanyoyi ne na saukakawa tare da inganta harkokin sufuri da ma’aikatarmu ta samar tare da hadin gwiwar Hukumar Hada-Hadar Kasuwanci Ta Jiragen Ruwa, wato ‘Nigeria Shippers Council’ don kawo karshen tulin kalubale da matsalolin da fannin sufuri ke fuskanta tsawon lokaci.
Ministan ya kuma kara da cewa, tasoshin za su taimaka wajen dakile dukkan matsalolin rashin damar riskar teku ga yankunan tudu, da kuma rage yawan cunkoso wadda a wasu lokutan ke haddasa salwantar kwantenoni da kuma yawan haduran da manyan motoci ke fuskanta kafin sada kayan da Arewa.
Ministan ya kara da cewa, tashoshin tudun ba kawai za su rage yawan tsadar sufuri ba ne, har ma da sada kayayyakin zuwa qofofin ‘yan kasuwa da rumfunansu sannan kuma su tada komakar tattalin arziki da walwala a tsakanin al’umma.
Haka shi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya ce wannan tasha ta kankama kuma daga yanzu za a riqa safarar kayayyaki daga kowane bangare na duniya zuwa Kaduna.
“Wannan rana ta bude wani sabon shafi na habakar kasuwanci da samun damarmaki ba kawai ga ‘yan kasuwa na Arewa ba, har ma da makwabtan kasashe kamar su Nijar da Chadi.”
Ya kuma kara da cewa, tsarin tekun tudun zai samar da dubban ayyukan yi tare da saukaka harkokin kasuwanci a arewacin qasar nan tare da kawo cigaban amfanin gona.
“Na yi matukar farin ciki da samuwar wannan tasha musamman saboda yadda wannan rana ta kawo karshen daruruwan kalubalen da Arewa ta daxe tana fuskanta a matsayin yanki mafi koma-baya. Don haka yau an tabbatar mana da cewa wannan tasha ta kafu kuma za a ci gaba da dauka da kuma sauke dukkan kayayyakin safarar kasuwanci zuwa ko’ina a duniya.
“Don haka muna godiya ga Gwamnatin Tarayya karqashin Shugaba Muhammadu Buhari da Ma’aikatar Sufuri da Hukumar Hada-hadar Kasuwancin teku da Hukumar Kula da kwantenoni ta tarayya.”
Shi ma a cikin nasa jawabin tun da farko, Babban Sakataren Hukumar Hada-Hadar Kasuwanci na Teku ta Najeriya, Malam Hassan Bello, ya bayyana cewa tuni wannan tashar tudu ta Kaduna ta samu amincewar fara aiki tun daga ranar 26 ga Watan Mayun 2015, sannan Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi a ranar 4 ga watan Janairun 2018, don fara aiki a matsayin muhimmiyar tasha, yau kuma Allah Ya nuna mana fara aikin tashar.
Ya ce babu raba daya-biyu wannan tasha za ta magance dukkan matsalolin da manya da kananan masu safarar kayayyaki ke fuskanta, sannan kuma tasha ce mai tabbas da ke da alhakin zirga-zirgar kwantenoni zuwa kowane sashe na duniya cikin sauqi.
“Kuma babu wani bambanci tsakanin yadda ake biyan kudin kiliya na kaya a nan Kaduna da kuma Legas, duk kuwa da yadda aka kawo kayayyakin a tsakiyar Arewa. Kuma ana zuwa da kayayyakin da suka kai nauyin tan dubu 120. Sannan a dauka daga nan a fita da su zuwa kasashen ketare”
Sannan a qarshe ya yi godiya ga Hukumar Kwastam da Babban Bankin CBN da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufai bisa gudumarsu har wannan tasha ta tabbata. Sai kuma ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su shigo don cin gajiyar tsarin.
Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa, manyan jami’an gwamnati, dukkan kwamishinonin kasuwanci na jihohin Arewa maso Yamma tare kuma da manya da qananan ‘yan kasuwa na cikin gida da waje