✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashe-tashen hankula ke haifar da koma baya –Sultan na Damagaran

Mai martaba Sultan na Damagaram, Alhaji Aboubakar Uomar Sanda, ya yi kira ga al’ummar Najeriya da Nijar da su zauna lafiya da juna a cikin…

Mai martaba Sultan na Damagaram, Alhaji Aboubakar Uomar Sanda, ya yi kira ga al’ummar Najeriya da Nijar da su zauna lafiya da juna a cikin kasashensu, inda ya ce, tashe-tashen hankula ko zubar da jini wanda ke haddasa asarar rayuka ba su kawo komai a cikin kasa sai koma baya.
“Ina so jama’a musamman matasa wadanda su ne kashin bayan al’ummar kasa, ka da su bari a yi amfani da su da su wajen wargaza kasa. A cewarsa, su gane kansu ne suke cutarwa, domin za su lalata kansu da kasarsu bayan rasa ‘yan uwa da abokan arzikin da an rabu da su har abada.
Wasu makiya ci gaban kasa ne da ke shigowa da sunan addini suna kawo rabuwar kawuna a tsakaninmu”.
Sultan na Damagaram ya tunatar da  al’ummomin kasashen biyu, cewa su ‘yan uwan juna ne, wadanda za su iya taimaka wa juna.  Ya kara da cewa,”ina tuna zaman da na yi har na tsawon shekaru uku a Abuja, ba zan manta da irin karamcin da aka yi mini ba, to amma sai ga shi ana so ta dabaru a hada mu fada da juna da sunan addini, wanda kuma babu addinin da ya yarda da fada balle kisa in ba wajen jihadi ba, wanda kuma yanzu babban jihadin da ya rage shi ne “jin tsoron Allah da bin dokokinsa.”
Ya ce, yana jin takaicin yadda ake amfani da wasu matasa marasa kishin kasa domin wargaza kasarsu ta haihuwa, a karshe ko dai a kashe su bayan an gama amfani da su, ko a kaisu gidan yari, har karshen rayuwa. “Mu dage wajen neman ilmi da rike sana’a, wannan shi ne zai taimaka wajen rage faruwar irin wadannan matsaloli ba wai kowane lokaci a ce sai gwamnati ba. An ce,’zaman lafiya ya fi zama dan sarki, ko in ce ya fi zama sarkinma, don sai da zaman lafiya sarki yake sarkin.” inji Sultan na Damagaram, Alhaji Aboubakar Uomar Sanda.