✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashe-tashen hankula sun addabi Jihar Taraba

Rigingimun da suke da alaka da kabilanci da addini sun yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa tare da lalata dukiya ta miliyoyin Naira a Jihar…

   Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba    Rigingimun da suke da alaka da kabilanci da addini sun yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa tare da lalata dukiya ta miliyoyin Naira a Jihar Taraba.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa rashin zaman lafiya ya addabi kananan hukumomin Ibbi da Wukari da Gashaka da Lau da Karim Lamido, inda a cikin wata daya kacal aka samu aukuwar rikicin addini a karamar Hukumar Ibbi har sau takwas rikicin da ya jawo asarar rayuka sama da 20 tare da lalata dukiya ta miliyoyin Naira.
A yanzu haka garin Ibbi da ke kudancin jihar, sojoji ne dauke da makamai ke sintiri don hana aukuwar wani tashin hankali a garin.
Garin Ibbi da garin Wukari sun zama filayen-daga inda ake zargin kusan kowane gida a wadannan garuruwa mazaunansa na da bindiga. Kuma yawan makamai a hannun jama’a a yankin da wasu yankunan jihar ya sa ake samun yawan aukuwar tashin hankali.
Mutane da dama da walikinmu ya zanta da su sun yi zargin cewa manyan jami’an gwamnati da ’yan siyasa har ma da sarakunan gargajiya ne ke hura wutar rigima a yankin don cimma burinsu.
Wani mazaunin yankin mai suna Mista Bulus Agyo ya shaida wa wakilinmu cewa rashin hukunta masu hannun a rigingimun da suke aukuwa a yankin ne ya sa har yanzu aka kasa shawo kan matsalar.
Ya ce a garin Wukari akwai wuraren da dama da Musulmi ba zai iya shiga ba, haka akwai inda Kirista ba zai iya shiga ba, sabo da tsananin kiyayyar da ke tsakanin mabiya addinan biyu. Ya yi Allah wadai da yadda wasu ’yan siyasa da manyan jami’an gwamnati suke cusa kiyayya da gaba a tsakanin al’ummar garuruwan Wukari da Ibbi inda ya ce ya zama tilas a kawo karshe wannan lamari domin kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Mista Agyo ya ce an wayi gari wadanda suka fito ciki daya na kashe junansu domin bambancin addini a garin Wukari.
Ya ce Allah kadai ya san yawan jama’ar da aka kashe a cikin garin Wukari bayan asarar dukiyoyi.  A cewarsa in bako ya shiga Wukari zai yi tsammanin rikicin Boko Haram ne ya shafi garin “Amma a gaskiya ’yan asalin garin ne suka kashe ’yan uwansu suka lalata dukiyar ’yan uwansu da sunan fadan addini,” inji shi.
Mista Bulus Agyo ya kara da cewa wauta ce wani ya ce ba zai zauna da bako ko mabiyin wani addini ba, kamar abin da ke faruwa a garin Wukari.
Shi ma wani mazaunin garin Wukari mai suna Malam Yakubu Garba ya ce shi dan kabilar Jukun ne amma laifinsa shi ne shi Musulmi ne saboda haka ’yan uwansa Jukunawa mabiya addinin Kirista suka kashe matansa da ’ya’yansa suka kuma kone gidansa. Ya ce wadanda ke wannan aika- aika hukuma ta san su amma an kasa daukar wani mataki na hukunta su.
Malam Yakubu Garba ya ce daukacin gidajen Musulmi a garin Wukari da wuraren sana’arsu duk an kone. Kuma ya ce an tilasta wa dubban Musulmi yin hijira daga garin Wukari zuwa wasu garuruwan Jalingo da Bali da Mutum Biyu da Gembu wasu kuma na warwatse a jihohin Adamawa da Nasarawa da Gombe.
A cewarsa har yanzu gwamnatin Jihar Taraba ba ta damu da batun ’yan gudun hijirar da suka bar garin Wukari ba. “Sama da yaran Musulmi 200 ba sa zuwa makaranta a dalilin kashe iyayensu da aka yi ko kuma a dalilin kasancewar iyayen na gudun hijira.
Ya ce wannan matsala ba Wukari kawai ta shafa ba har da garin Ibbi da Chinkai da Danpar da Mala da sauran garuruwa da ke yankin Wukari inda ’yan bindiga ke cin karensu babu babbaka wajen halaka bayin Allah.
A yankin karamar Hukumar Lau da Karim Lamido an hallaka sama da mutum 20 a rigimar kabilanci da addini a tsakanin ’yan kabilar Shomo da Jolle da kuma tsakanin Shomo da Wurkum sai kuma tsakanin ’yan kabilar Mumuye a yankin karamar Hukumar Zing.
A karamar Hukumar Gashaka an kashe sama da mutum 50 a wani fada a tsakanin ’yan kabilar Ndoro da makiyaya.
Bayanai sun ce ’yan kabilar Shomo da ke da dangantaka da kabilar Jukun ne ake zargi da afka wa kabilar Jolle da Hausawa wadanda ake kira Kabawa.
Bincike ya nuna cewa ’yan kabilar Shomo sun hallaka mutum fiye da 15 a kauyukan Kabawa da Dubeli a karamar Hukumar Lau kuma suka kone kauyukan uku.
Bayan wannan ’yan kabilar Shomo sun ketare Kogin Benuwai inda suka kai hari a garuruwan kabilar Wurkum da suka hada da  Didango da Balasa suka kashe mutane masu yawa sa’annan suka kone garuruwan uku.
Wani mazaunin garin Didango mai suna Malam Dauda Didango ya ce ’yan kabilar Shomo da sojojin sa-kai na ’yan kabilar Jukun ne suka afka wa garuruwan nasu suka kashe mutane tare da kone su.
A cewarsa a ranar Juma’ar makon shekaranjiya ne ’yan kabilar Shomo suka afka wa garuruwan Wurkum suka ci gaba da barna har zuwa ranar Litinin. Ya ce mutane da dama da suka hada da matan aure da yara suka bace, yayin daruruwa suka gudu zuwa wasu yankuna a matsayin ’yan gudun hijira.
A cewar Malam Dauda dukkan rigingimun da suke auka wa Jihar Taraba wadansu ’yan siyasa ne ke haifarwa domin cimma burinsu na siyasa.
Ya ce a yau in gwamnati na so ta magance wannan matsala za ta iya amma yadda ake barin masu tayar da fitinar ba a hukunta su ne ya sa za a ci gaba da fuskantar rashin zaman lafiya a jihar.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Taraba, Alhaji Sha’aba Alkali a cikin wata sanarwa da ya bayar ya ce rundunar ’yan sandan jihar na iyakacin kokarin wajen kare rayuka da dukiyar jama’a.
Ya nemi al’aumar jihar su bayar da rahoton wani ko wadansu masu neman kawo rashin zaman lafiya a jihar tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana tayar zaune-tsaye za a hukunta shi.
Gwamnan Jihar, Mista Darius Ishaku ya fadi a wurare da dama cewa gwamnatinsa za ta maida hankali wajen kawo karshen yawan tashin hankula a jihar. Gwamnan ya kuma ce jihar za ta samu ci gaba ne kawai idan akwai zaman lafiya da kwamciyar hankali inda ya nemi al’umar jihar su ba shi zaman lafiya shi kuma ya ba su ayyukan raya kasa.