✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tasirin bambance-bambancenmu a rayuwa

Jama’a masu karatun Aminiya, ina yi maku sallama kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum. Bayan haka, a yau kuma muna dauke ne da sabon maudu’i,…

Jama’a masu karatun Aminiya, ina yi maku sallama kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum. Bayan haka, a yau kuma muna dauke ne da sabon maudu’i, duk dai a cikin wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa. Babbar fa’idar da ake son tsinkaya dai ita ce, a samu hikima da dabarun yadda za a zauna cikin al’umma bisa tsari da lumana. Ta yadda za a samu tsira daga iface-ifacen miyagu da shaidanun da suka yi kaka-gida cikin al’umma da rayuwarsu.

Kamar yadda maudu’inmu na yau ya nuna, ba a taru aka zama daya ba. Ana son a bayyana wa al’umma yadda Ubangijin halitta Ya tsara halittunSa zuwa aji-aji, musamnman domin mu fahimci yadda rayuwa take, kuma domin mu yi amfani da matsayinmu da Ya aje mu, domin mu cudi juna, mu samu fa’idar rayuwa.

A rayuwa, idan aka ce an halitta mu duk iri daya, kuma jinsi daya, masu kala iri daya, to babu shakka babu yadda za a yi a samu fa’idar rayuwa a haka. Ke nan akwai fa’ida da hikima mai girma, irin yadda aka halitta mu zuwa nau’o’i daban-daban. Babban abin da zai sanya ka maida hankali har ka gane tasirinka da fa’idarka da amfaninka a rayuwar kanka shi ne, sai ka duba yanayin halittar wani dan uwanka. Daga nan ne za ka gane ko kai wane ne, kuma me Allah Ya yi maka a cikin al’umma, wanda da babu wancan da zai zame maka misali, da ba za ka gane komai ba na rayuwa.

A tsarin halittar Ubangiji, Ya halitta mutane masu idanuwa lafiyayyu, sannan kuma gefe guda Ya kadarta wasu suka zamanto makafi, marasa idanuwa. A nan, da zarar mai ido ya ga makaho, sai ya gane tasirin idanuwansu, kuma haka zai sanya ya gode wa Allah da wannan baiwa da Ya yi masa. Da babu makaho fa, ta yaya mai ido zai gane haka?

Ta yaya mutum zai gane yana da hankali idan babu mahaukaci? Babu yadda haka za ta yiwu. Ke nan shi ma mahaukaci yana da amfani a cikin al’umma, wanda da shi ake misali na bambance mai hankali da marar shi. Idan babu guragu, ta yaya masu kafafu za su gane fa’idar kafafunsu?

Idan babu jahilai, shi mai ilimi ta yaya zai gane cewa yana da wata baiwa ta musamman? Sai da jahili ne mai ilimi zai gane bambancinsa da shi. Kuma gane wannan bambancin ne zai sanya ya gane cewa ashe yana da wani matsayi na musamman a rayuwa. Dalili ke nan zai sanya ya bambanta kansa da jahili, har ya rika yin aiki cikin mutane ta amfani da iliminsa. Wanda kuma haka zai sanya al’umma ta ci gaba, domin mutane za su ga bambancin karara, inda haka za ta sanya a tashi haikan domin neman ilimi, don a guje daga jahilci da ayyukan jahilci.

Wannan al’amari na bambancin halitta, shi ke sanyawa a gane cewa Allah daya ne, amma gari ya bambanta. Haka kuma ke sanyawa a cudanyi juna domin a samu fa’idar rayuwa. Misali, kamar yadda ake samun fakirai, haka kuma ake samun attajirai. Idan aka ce kowa attajiri ne a cikin al’umma, anya al’ummar nan za ta samu dadin rayuwa kuwa? Ina ganin babu wani dadin zama da za a samu da irin wannan tsari. Dalili ke nan aka samu bambanci, domin fakiri na bukatar attajiri, kamar kuma yadda shi attajirin ke bukatar fakiri. Kan haka sai a yi bayayya a tsakani, wanda haka zai sanya a samu biyan bukatar rayuwa ta wadannan bangarori biyu.

Wannan al’amari na rayuwa zai kara tabbatar mana da cewa, kowa da ranarsa, kowa na da wani amfani a rayuwar nan ta duniya. Ke nan kowa na da dalilin kasancewarsa. Misali, idan babu kafiri, yaushe kai mai imani za ka gane kana da imanin? Ko kuwa idan babu fajiri, yaushe kamili zai gane cewa ya bambanta ta halayya da fajiri? 

Babban abin da ya kamata mu gane a rayuwa shi ne, mun bambanta da juna ta hanyoyi da dama. Idan baka da lafiya za ka gane amfanin lafiya, don haka sai ka kare lafiyarka. Sai ka ga matacce, sannan za ka tabbatar da cewa ba a dawwama a duniya, don haka sai ka yi kokarin aikin da zai cetar da kai idan ka isa wannan babban gida. Sai ka ji yunwa, sannan za ka gane amfanin abinci, wanda haka zai sanya ka mike tsaye domin neman abinci.

Rayuwa ke nan, wacce ke rikida zuwa siffofi da kaloli daban-daban. Don haka kada mu sake mu shagala da ita. Idan mun samu kawunanmu cikin wadata, to mu sani cewa akwai fakirai, kuma dole mu zauna da su. Idan mun samu kawunanmu a matsayin masu mulki, to mu tuna da cewa akwai talakawa, kuma dole muna bukatarsu, domin mu zauna tare, wanda idan babu su, to ina mulki zai yiwu, kuma wane tasiri ma mulkin zai yi?

Mu zamanto masu godiya ga dukkan yanayin da muka samu kawunanmu, domin kuwa haka rayuwar ta kasance. Mai mulki ya kalli na kasansa, attajiri ya kalli mara shi, mai lafiya ya kalli marar lafiya, babba ya kalli yaro, mai hankali ya kalli marar hankali. Kai da kake raye, sai ka kalli wanda ya mutu. Duk inda ka duba, da matsayin da kake, sai ka ga wanda bai kai ka ba. Wannan zai sanya ka samu kwanciyar hankali har ka gode wa Allah da matsayin da ka ke. 

A rayuwa, ba ka da wata hikima, ba ka da wata dubara, ba ka da wani iko, kai dai ka kasance cikin kula da lura, bisa taka-tsan-tsan da rayuwa. Idan ka yi haka, to ka tanadar wa kanka wani babban sinadarin rayuwa mai fa’ida. Da fatan za mu kasance masu cin ribar rayuwa a cikin wannan duniya da wata duniyar mai zuwa gobe. Allah Ya sanya mu dace, amin. Sai mun hadu a makon gobe, idan mai kowa Mai komai Ya kai mu!