✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tasirin camfi a wajen  Hausawa cikin tarbiyyarsu

Camfi ya kunshi a bubuwa da dan Adam kan kudire shi a zuciyarsa kuma yakan gaskata shi, misali abin da ya shafi tsoro da mafarki…

Camfi ya kunshi a bubuwa da dan Adam kan kudire shi a zuciyarsa kuma yakan gaskata shi, misali abin da ya shafi tsoro da mafarki da tsuntsaye da ruwa da abubuwa da dama da dan Adam yake zamantakewa da su, camfi ya bambanta daga kabila zuwa kabila. Ita ma al’ummar Hausawa tana da nata camfin da takan yi. Koda yake addini ya haramta camfi amma za mu duba camfi a mahangar tarihi da tsohowar al’adar Hausawa. camfi ya kasu zuwa bangare da dama: kamar lafiya da arziki da rashin lafiya da aure da haihuwa da sauransu.

Za mu duba camfi a mahangar tarbiyyar Bahaushe. Wannan ya sa na yi tozali da wani rubutu a shafin Intanet, wanda kwararren marubucin nan ya makala shi a wato Lawi Yusuf Maigidan Sama.

Duk da kasancewar camfi mummunar al’ada ce amma yana tattare da wasu hikimomi da za a iya ƙaruwa da su, kodayake ba za su halatta amincewa da camfi ba. Idan aka dubi camfe-camfen Hausawa za a iya kutsa kai a laluɓo wasu isharori da suka yi na kyautata rayuwa da suka danganci tarbiyya da koyar da ɗabi’u da bunƙasa tunani da faɗakarwa da tunatarwa da tsoratarwa da nuni kan dogaro da kai. Sannan camfi kan hana mutane aikata abubuwan ƙi da neman a guje musu. Wato ke nan a wata fuskar camfi wani ƙuduri ne na tarbiyya da horo da hani da bunƙasa tunani da faɗakarwa. Cikin wannan mukala zan yi dubi kadan daga cikin ire-iren tasirin da camfi ya yi cikin tarbiyyar Hausawa.

Ma’anar Camfi

Akwai ƙirdado da yawa dangane da ma’anar wannan kalma ta “camfi,” wannan ma ya sanya, na ɗora hannuna kan waɗannan ra’ayoyi na masana.

Bunza (2006:58). Cewa ya yi “Camfi wata daɗaɗɗiyar al’ada ce da Hausawa suka tarar tun kaka da kakanni. Kuma masana da manazarta Hausa sukan yi wa camfi kallo ta fuskoki biyu, wadansu na kallon camfi, al’ada ce kawai kamar irin kowace al’ada; a ganin wadansu kuwa, abin ya wuce haka, ya kai matsayin addini daga cikin addinan gargajiyar Bahaushe.”

El-Shamy (1976) ya ce “Camfi yarda ce ko amincewa, ko yin imani da wani abu a matsayin an gaskata shi tare da abubuwan da ya ƙunsa.”

Scott (1976) kuma cewa ya yi “Camfi shi ne, yarda ko amincewa da wani abu, ko aiwatar da wani abu da aka gada, kaka da kakanni cikin duhun jahilci, saboda tsoro, ko nuna fargaba da abin da ba a amince da shi ba.”

Ɗangambo (1984:38) ya ce “Camfi shi ne mutum ya ɗauka cewa, in ya yi wani abu, ko ya ce wani abu, ko ya ji wani abu, to ya gaskanta wani abu zai faru, sakamakon haka.”

Ma’anar tarbiyya

Yahya da wasu (1992:68). Tarbiyya wata hanya ce ta kyautata rayuwar ɗan Adam da shiryar da shi zuwa ga halaye da ɗabi’u masu kyau, masu nagarta. Idan ɗan Adam zai tashi da kima da mutunci da ƙwarjini da ganin kimar abokan zamansa, sannan zai rika bai wa kowa hakkinsa daidai yadda ya kamata gwargwadon iyawa da hali, to za a iya cewa yana da tarbiyya. Tarbiyya ta haɗa da rainon jikin mutum da ransa da abubuwa kyawawa masu sa kamala.

Kamusun Hausa (2006:428) ya ambaci tarbiyya da cewa raino ne da ake yi wa yara domin tashi da halaye nagari su kuma kyamaci munanan ɗabi’u.

Funtuwa (1983:63) ya bayyana tarbiyya da cewa: “Horo ne da iyaye ko manya na gaba ke yi wa yara don su tashi da halayen kirki. Duk yaron da ya tashi babu tarbiyya, rayuwarsa na iya zama mai rauni ce, kuma ana koyon tarbiyya ce ta hanyoyi kamar faɗa da kwaɓa da hani da umarni da kwaɗaitarwa da duka sannan da sanya yara a makaranta don samun ilimi da halaye nagari.”

Misalan camfi masu nuna tarbiyya

Misalan da za su zo kadan ne daga cikin tasirin da camfi ya yi a tarbiyar Bahaushe.

Camfe-Camfe masu hani/gargaɗi

1. Idan aka doki maciji da karan rama, za a ga kafafunsa, amma za a mutu.

2. Idan yaro na cin ƙwai zai yi sata.

3. Cin kan kifi na sa dushewar basira.

3. Idan mace mai ciki ta tsallake rafi to za ta yi ɓari.

4. Ƙetarar wando na sa mata yawan mafarki

5. Kallon majigi ga mai ciki, kan sa a haifi yaro mahaukaci.

6. Yin shara da dare na kawo tsiya (talauci)

7. Idan mace mai ciki ta ɗebi ruwa a rafi da daddare aljanu za su musanya ɗanta da nasu. Da sauransu.

Idan aka dubi waɗannan misalan za a ga cewa camfin ya nuna tarbiyya ga mata ko mutane inda yake hani ga barin wasu abubuwa.

 

Mun dauko wannan rubutu ne daga www.bakandamiya.com