✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tasirin ci gaban kimiyya da fasahar sadarwa ga zamantakewar dan Adam a duniya (4)

Matashiya A kasidu ukun farko da suka gabata cikin mako hudu da suka shude, idan mai karatu bai mance ba, mun fara yin shimfida ce kan…

Matashiya

A kasidu ukun farko da suka gabata cikin mako hudu da suka shude, idan mai karatu bai mance ba, mun fara yin shimfida ce kan tasirin ci gaban da ake samu a duniyar yau a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani da dabi’u, ga ilahirin rayuwar dan Adam a duniyar yau. Mun nuna cewa akwai fannoni kamar fannin tsari da dabi’un halittar dan Adam, wato: “Genetics” da fannin Kimiyyar Sadarwar Zamani. “Information Technology” da fannin kimiyyar kwakwalwa da halayya da sauransu. Ci gaba a wadannan fannoni tare da ci gaban kere-keren na’urorin zamani, suke taka rawa wajen samar da wata sabuwar rayuwa da yanayin zamantakewa a duniyar yau.

Manufar wannan bincike namu ita ce, yunkurin gano tasirin wadannan sauye-sauye ga al’adu da addini da siyasa da kuma zamantakewar dan Adam a ko’ina yake a duniya. Ma’ana, ta la’akari da wadannan sauye-sauye da mai karatu zai karanta a jerin wadannan makalu da za su biyo baya, wani irin shugabancin siyasa za a samu nan gaba?  Wani irin kalubale ne malaman addinai, musamman na Musulunci, za su fuskanta wajen kokarin fahimtar wannan sabuwar duniya, tare da samar da fatawoyin da za su bai wa sababbin tsare-tsaren nan da hukunci na musamman, wajen halacci ko haramci ko wajabci ko karhanci da sauransu?

Muna kuma bibiyar daya daga cikin masana a fannin kimiyyar zamantakewa da halayyar rayuwar siyasa ne a duniyar yau, wato: Farfesa Francis Fukuyama, musamman cikin littafinsa mai suna: “Our Posthuman Future: Consekuences of the Biotechnology Rebolution” da wani littafinsa har wa yau mai take: “The Great Disruption: Human Nature and the Reconstitution of Social Order.” Bayan wadannan littafai, za mu bibiyi sakamakon binciken malaman kimiyyar zamanin yau kan wadannan fannoni da suka kunshi wadannan sauye-sauye da ake samu.  Da hirarrakin da ake yi da su a kafafen watsa labarai na yau.

Kafin mu ci gaba, zan so mai karatu ya fahimci cewa, dukkan bayanan da zai ci karo da su a wannan shafi kan wadannan sauye-sauye da ake samu a rayuwa wajen dabi’u da kere-kere da kimiyya, hakaitowa ce zan rika yi, ba wai hukuncin halaccinsu ko haramcinsu a addinin Musulunci zan yi ba. Domin mai karatu zai ji abubuwa ne masu ban al’ajabi, wadanda a zahirin al’adar Bahaushe da addininsa, sun saba matuka.  Wasu ma ba su yi kama da hankali ba. Kada mai karatu ya dauka don na yarda da halaccin wadannan sauye-sauye ne ya sa na kawo su.  A karshen bayanan zan rika kawo tasirin da wadannan sauye-sauye za su yi ko suke yi a wasu kasashe, wajen canja halayyar dan Adam da siyasar kasashe da kuma tsarin sadarwa da kimiyyar halitta.

The Human Genome (Rumbun Bayanan Dabi’u da Siffofin Halitta)

Ga wanda ya saba karanta wannan shafi, musamman shekaru kusan takwas da suka gabata, a jerin makalolin da muka kawo masu take: “Tsarin Dabi’u da Siffofin Halitta”, wanda da Ingilishi ake kira: “Genetics,” mun yi bayani kan cewa tuni malaman kimiyyar halitta na wannan zamani suka kididdige yawan bayanan da ke dauke da dabi’u da siffofi da halayyar dan Adam gaba daya, kamar yadda Allah Ya samar da su a cikin kwayar halitta, wato: “Human Cell.”  Wannan bincike mai suna: “The Human Genome Prohect,” wanda aka gama shi kusan shekara 15 zuwa 20 da suka gabata, ya tantance bayanai sama da biliyan shida da ke siffantawa ko bayyana yanayin halitta da dabi’ar dan Adam a jikinsa.

Misali, launin kwayar idon dan Adam da launin gashin kansa da launin fatar jikinsa da dabi’ar kyauta ko rowa ko hakuri ko juriya ko wadatuwar zuci; duk wadannan halayya da siffofi, bayanai ne da Allah Ya zuba su a cikin wannan kwayar halitta, wacce ke dauke da su kuma take fassara hakikanin dan Adam da yadda Allah Ya halicce shi, yayin da yake raye yake gudanar da rayuwarsa. Daga cikin wadannan bayanai har wa yau akwai wadanda ke kunshe da irin cututtukan da Allah Ya sa a cikin dabi’ar jini ko jikinsa, wanda kuma yake gadar wa ’ya’yansa da jikokinsa har zuwa tattaba kunnensa.

Babban dalilin samar da wannan rumbun bayanai dai shi ne don fuskantar manyan kalubalen da ke fuskantar rayuwa da lafiyar dan Adam, musamman kan cututtukan da suka addabi jinsin bil’adama irin su ciwon sankarar jini wato: “Sickle Cell Anaemia,” da cutar Kanjamau (AIDS) da sauran cututtuka makamantansu da magungunan zamani suka kasa magance su. Wannan ya sa aka fara amfani da hanyoyin kere-kere da kimiyyar zamani wajen samar da na’urorin da ake iya amfani da su wajen tantance duk wani bangare na jikin dan Adam da ke iya kamuwa da wata cuta kuma har ya harbi wani bangaren jikinsa ko zuriyarsa.

Fahimtar wadannan abubuwa ne zai taimaka wajen samar da hakikanin waraka ga wadannan cututtuka.  Tunda jikin dan Adam na gudanuwa ne cikin wani tsari mara misaltuwa.  Allah, Wanda Shi ne Mahaliccin halittu, Shi ne kadai Wanda Ya san hakikanin yadda tsari yake.

A mako mai zuwa za mu tabo bayani kan asalin kundin da ke dauke da bayanan dabi’u da siffofin halitta gaba daya da yadda masana suka nemo hanyar sauya bayanan da ke tafiyar da wadannan halayya cikin sauki.