Da Dumi Dumi

Tasirin ci gaban kimiyya da fasahar sadarwa ga zamantakewar dan Adam a duniya (5)

  • Kundin ‘DNA’ da kokarin magance cututtuka

Bayan hada wancan rumbun bayanan dabi’u da siffofin halittar dan Adam da aka yi a baya, nan take malaman kimiyya a bangaren likitanci da dabi’un dan Adam suka shiga dakin bincike don tantance dalilan da suke sa wadansu iyaye ke gadar wa ’ya’yansu cututtukan da suke da su, musamman cututtuka irin su ciwon suga (Diabetics) da hawan jini mai kaiwa ga ciwon zuciya (High Blood Pressure/Hypertension) da sauransu. Wannan ita ce manufar asali da ta sabbaba samar da wani fanni na musamman mai suna: “Genetic Engineering,” wato fannin sauya siffofi da dabi’un halittar dan Adam don samar da waraka ga cututtuka marasa jin magani.

Wannan yunkuri ya taimaka sosai wajen gano bangaren kwayar halittar da ke dauke da wasu halayya ko siffofi da ke iya gadar da cuta daga mahaifi ko mahaifiya zuwa zuriyarsu.  Hakan ya kai ga kokarin neman hanya ko hanyoyin da za a iya amfani da su wajen sauya wadannan bayanai masu bayar da siffofi ko dabi’ar da ke gadar da cuta ga ’ya’ya. Da farko dai wannan aiki na sauya wadannan bayanai ya ci tura. Saboda aiki ne mai dauke da hadari sosai. Fahimtar yadda wadannan bayanai suke zai taimaka wajen gano hadarin da ke tattare da wannan aiki.

Kowane dan Adam dai Allah Ya halicce shi ne da bangarori guda biyu muhimmai.  Bangaren gangar-jiki da ake iya gani da kuma bangaren ruhi, wanda har yanzu babu wanda ya san hakikaninsa da yanayin gudanuwarsa sai Allah Mahalicci.  Amma bangaren gangar-jiki Allah Ya bai wa dan Adam wata kudira ta ilimi da zai iya gano abubuwa da yanayin gudanuwarsu. Wannan ya sa muke da likitocin ido da na makogoro da na hanta da na kwakwalwa da na hakori da sauransu. Amma yadda gangar-jikin kowace halitta – ba ma dan Adam kadai ba – ke gudanuwa shi ne, akwai kwayoyin halitta (Cell) masu dimbin yawa da ke gudanar da kowane bangaren jikin dan Adam.  Misali, a kwakwalwa kadai akwai kwayoyin halitta birjik. Haka cikin jinin dan Adam da zuciyarsa da idanunsa da sauran bangarori.  Wadannan kwayoyin halitta su ne ke dauke da hakikanin bayanan yadda dukkan bangaren jikin dan Adam ke gudanuwa. Kuma ba komai ba ne illa bayanai ne da Allah Ya zuba a ciki, wadanda ke bai wa bangarorin jikin dan Adam umarnin su kasance yadda Allah ke so su kasance.  Tirkashi!

Misali, kowace kwayar halitta a cikinta akwai bangaren DNA, wanda bayaninsa ya gabata a kashi na uku.  Wannan bangare ne ke dauke da bayanan yadda bangarorin jikin dan Adam ke gudanuwa. Wadannan bayanai dai kamar wani kundi ne na tsare-tsare da ke bai wa bangarorin jiki umarnin su bayyana ko dabi’antu da wasu siffofi ko halaye. Misali, kwayar halittar da ke lura da launin fatar jikin dan Adam na dauke ne da wadannan bayanai. Idan aka samu isa ga wannan bangare na DNA, za a ci karo da wadannan bayanai da yadda suke bayyana hakikanin launin fatar dan Adam. Ka dauka DNA wani littafi ne mai haruffa biliyan shida, kuma mai dauke da babi-babi daban-daban. Su kuma kwayoyin dabi’un halitta da ke gudanar da rayuwar dan Adam (Genes), su ne babi-babin da ke cikin littafin. Don haka, idan kana son ganin bayanan da ke siffanta tsayi ko gajartar dan Adam, sai ka je babin da ke dauke da kwayar dabi’ar halittar da ke wannan aiki. Ba rubutattun bayanai ba ne irin wanda kake gani a kan takarda. Wasu bayanai ne da masana kimiyya ke iya fahimtarsu a tsarin da suke, ta amfani da manyan na’urorin kimiyyar hango abubuwa kanana da ido ba ya iya gani.

Don haka, duk abin da aka sauya daga cikin jerin wadannan bayanai da suke bayyana ko siffanta gudanuwar wani bangare na jikin dan Adam, to, nan take yanayin aikinsa zai canja. Haka idan aka yi kuskuren cirewa ko goge wani bangaren bayani ba yadda ya kamata ba, to, nan ma za a samu matsala mai girma wadda za ta iya shafar kusan dukkan jikin dan Adam. Wannan ya sa a baya a aikin sauya wadannan bayanai ya zama da tsauri, domin da zarar an yi kuskure, rayuwar dan Adam na cikin hadari, in ma bai mutu ba ke nan.

ADVERTISEMENT

A mako mai zuwa in Allah Ya so za mu dubi wani sabon tsari da wadansu masana suka gano wanda ke sawwake hanyoyin sauya bayanan da ke cikin sinadaran dabi’u da siffofin halitta, sannan in da hali mu fara bayani kan tasirin wannan hanya da irin abubuwan mamaki da al’ajabi da ake sa ran nan gaba za su samu sanadiyyar buduwar wannan sabuwar kofa ta bincike da aikin kimiyyar halitta da dabi’u.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya