Aminiya

Tasirin zaben gwamnoni da za a yi gobe

Assalamu alaikum da fatan kowa yana lafiya. Hankalin mafi yawan jama’a ya karkata a kan zabubbukan da za a sake gudanarwa domin jihohi ne masu cike da yawan magoya bayan kowanne bangare. Kiranmu shi ne ya kamata hukumomi su yi adalci, mutane na da ’yancin zaben wanda suke so kuma suna da tabbacin za a ba su abin da suka zaba. Tunda dai muna cikin gwamnatin mai gaskiya ne wato mulkin Muhammadu Buhari.

Daga Abubakar Shitu Maishago Zuba da Malam Hasan Gidan Wankan Alhaji Gwani Zuba-Abuja 08032337145.

ADVERTISEMENT

Kanawa mu farfado da Jam’iyyar Aminu Kano ta PRP

Assalam Edita. Jama’ar Kano don Allah mu farfado da jam’iyar Malam Aminu Kano, wato PRP. Na so a ce a zaben Kano, an zabi Malam Salihu Sagir Takai. Domin duk wanda aka zaba cikin biyun can wato PDP ko APC daya zai ce an yi masa magudi. Zaben PRP shi ne mafita. Allah Ya sa a yi zabe lafiya.

ADVERTISEMENT

Daga Aminu Ado 250 Fagge Kano 08030636621.

Barazanar lashe zaben Gwamnan Bauchi

Hakika barazanar rasa kujerar Gwamna da Gwamnan Bauchi Muhammad A. Abubakar ke fuskanta ya ta’allaka ne bisa gajiyar mutanen Jihar Bauchi na ganin alkawuran da Gwamnan yake fitowa a kafafen watsa labarai yana dauka amma ba ya cikawa. Ina kira ga duk wanda Allah Ya ba shi wannan matsayi bayan an kammala zaben, ya kula da cika alkawurra ya kuma daina daukar alkawuran aikin da suka fi karfin tattalin arzikin jihar.

Daga Abdurrasheed Yakubu Shall 08025006360.  

Kira ga Ministan Ilimi

Assalam Edita. A ba ni fili in shawarci Ministan Ilimi cewa ya dace mu yi koyi da tsarin ilimi na Amurka wanda ya tilasta wa kowane dalibi yin darasin tarihi (history) don sanin tarihin kasa ke kara sanya kishin kasa da kaunar juna kuma a dawo da nuna majigi a makarantu, domin yaran yanzu su ga irin ayyukan arzikin da su Sardauna suka yi don ya zama kalubale gare su. Kuma mu yi koyi da tsarin ilimi na kasar China wanda ya mai da hankali kacokan kan ilimin kimiyya da kere-kere kuma ya dace a soke tsarin karatu daga-gida kada yara su shagwabe su gaza fita waje neman ilimi.

Daga Amiru Isah Bakori 07068147933.

Kira ga Gwamna Ganduje kan gina Jami’ar Musulunci

Dokta Abdullahi Ganduje Gwamnan  Kano, hakika muna yaba maka muna kara yaba maka bisa ayyuka a birni da kauye, lungu da sako a jiharmu ta Kano. Bayan haka ya Mai girma Gwamna! Mu mutanen Kano, kuma ’ya’yan Jam’iyyar APC, a matsayinka na Khadimul Islam muna bukatar Jami’ar Musulunci a Jihar Kano. Gwamnatin da ta shude filin da aka tanada don gina jami’ar ta kwace ta gina Jami’ar North-West wanda mu mutanen Kano ga abin da muke bukata amma ba shi aka yi mana ba. Allah Ya taimaki Mai girma Gwamna da masu ba shi shawara, amin.

Daga matasan APC Gandujiyya, Jihar Kano 08034515758.

Kira ga iyaye a kan tarbiyya

Salam Edita! Kira ga iyaye musamman ’yan Arewa masu goyon bayan ’ya’yansu koda sun yi marar kyau da ba sa son a kwabi ’ya’yansu, su sani babu abin da suke shukawa illa babban ukuba wanda su ko ’ya’yan za su girba wanda ba zai haifar masu da da mai ido ba. Hakika tarbiyya a Arewa tana ja baya, wani ba zai kwabi dan wani ba ko da dan kane ne wanda haka ba daidai ba ne ba kuma haka addini ya tanadar mana ba. Mu dubi abokan zamanmu na Yamma da Gabas haka suke? To hattara dai ’yan Arewa!

Daga Basiru Danbazazzagi, 08058591624.

Fatan alheri ga Gwamna Tambuwal

Assalam Editan wannan jaridar mai farin jini. Ina son ku isar min da wannan sako ga Alhaji Aminu Waziri Tambuwal Matawallen Sakkwato Ubangiji Allah Ya saka masa da alheri. Haka ina son ku isar min da wannan sako zuwa ga Alhaji Wadata Hakimi ina yi masa fatan alheri da samun hawa bisa kujerarsa. Don Allah ina rokonsa ya yafe mana muna da iyali ko Allah Ka yi wa laifi idan ka roke Shi zai yafe maka duk dai abin da za ka yi wa mutum nan duniya ce.

Daga Abubakar Ladan Minannata Rijiyar Shehu 09064337074.

Sakon taya murna ga Buhari da Sardaunan Kano

Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) Wanda Shi ne Ya amshi addu’ar talaka, Ya zaba masa abin da ya dace da shi a sa’ar da ta dace da shi. Da haka ne muke kara gode maSa da kuma roko a gare Shi da Ya ba wa Shugaba Buhari ikon kwatanta adalci a wajen gudanar da mulkinsa Allah Ya amsa mana amin. A karshe ina taya Mai girma Sardaunan Kano murnar lashe zabe da ya yi a matsayin Sanatan Kano ta Tsakiya tare da sauran ’yan majalisa baki daya, Allah Ya ba mu sa’ar lashe zaben Gwamna da ’yan majalisarmu 40 baki daya amin.

Naku ABUBAKAR TALLE Bayan Asibitin Murtala Kano 08034687931.

Sakon taya murna ga Buhari

Assalamu alaikum Edita. Ina rokon fili Aminiya don taya Shugaba Buhari murnar sake zabensa karo na biyu.

Daga Aliyu Korau Bajari 09033330197.

Tambaya ga Shugaba Buhari

Assalamu alaikum Edita. Don Allah a ba ni dama in tambayi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa me yake nufi da maganganun da ya yi cewa, wannan mulkin zai fi na baya tsauri.

Daga Imrana Lawan Gwammaja 07069034956.

Abin da ya kamata mai zabe ya duba

Assalam Edita, da fatan alheri kai da mataimakanka amin. Ina so ka ba ni dama a wannan jarida tamu mai albarka in yi kira ga ’yan Najeriya maza da mata cewa ya kamata su duba abubuwa hudu wajen zaben Gwamna da na ’yan majalisar jiha, saboda samun shugabanci nagari da wakilci. Abubuwan su ne: gaskiya, rikon amana, ilimin zamani da boko da jarumta.

Daga Lawal Muhammad 08060782035.

’Yan siyasa na amfani da alkalai

Assalam Edita, ka bani fili don in bayyana takaicina kan yadda kotuna suke gudanar da harkokinsu ta yadda  ake  amfani  da su don biyan bukatar ’yan  siyasa. In ban da biyan bukatar ’yan siyasa don me ba a soke zaben fidda-gwani na Abba ba sai da lokaci ya kure? Wannan zulunci ne kuma Allah na nan. Allah kuma zai saka masa, an ga Abba  ya karbu.

Daga Husaini T. Imawa  Kura 08165610365.

Godiya ga ’yan Najeriya kan zaben Buhari

Salam Aminiya mai albarka da fatan kuna cikin koshin lafiya. Ku ba ni dama in yi godiya ga ’yan uwana ’yan Najeriya baki daya game da sake zaben Shugaban Kasarmu Baba Buhari. Ya Allah! Ka bar mana Baba Buhari lafiya  da wannan namijin aiki da yake yi, amin summa amin.

Daga Ali Badina Alausa Ikeja Legas 09069152847.

’Yan PDP a Jihar Kano a sake fitowa zabe

Aminiya sakona ga masoyan PDP a Jihar Kano. shi ne don Allah mu kara hakuri kada mu karaya mu futo zabe ranar Asabar Allah Ya ba mu nasara. Ina rokon jama’a kada su tayar da fitina a wurin zabe.

Daga Jinin Kwankwasiya Akida, 09033322295.

’Yan PDP da tsaron akwatin zabe

Salam Aminiya. Ina kira ga PDP suna maganar a janye sojoji daga rumfar zabe, an ajiye sojoji ne saboda barayin akwati idan ku ba barayi ba ne ina ruwanku. Duk wanda ya saci akwati a harbe shi wannan daidai ne Allah Ka raba mu da kowane barawo, wasalam.

Daga Ado Dinji Kaugama Sauna, Kano 08088227962.

Ga Shugaban INEC kan zaben Kano

Salam Edita, da fatan kana nan lafiya. Ina so in yi amfani da wannan dama in mika sakon farin cikina  ga al`ummar Najeriya game da zaben Shugaban Kasa da ya gabata. Na yi farin cikin yadda aka yi zaben lafiya aka gama kuma lafiya. Da haka nake kara kira ga Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa  (INEC) don Allah a sa ido a kan zaben da za a yi a Jihar Kano. Mun fi so a ce an yi zaben tsakani da Allah. Da fatan wannan sakon zai isa zuwa ga al’umma baki daya.

Daga Nasiru Sani Birged Karamar Hukumar Nasarawa, Kano 09069985179.

Sakon jinjina

Edita a taimaka min da adireshin matar nan da ta kai mijinta kara saboda gyara rayuwar ’ya’yansu ina yaba mata kuma ya kamata gwamnati ta kula da ita domin ta zama abar koyi. Ina son in ba ta nawa taimakon (Malama Jamila Abubakar) a aiko min da lambar waya ko lambar asusun bankinta

Daga Hassan Ibrahim Warji, 08121899959.

Ta’aziyya ga Bagizage Nura A. Ahmed

Assalam Edita da fatan kana cikin koshin lafiya amin. A madadin Gizagawan Zumunci ina mika ta’aziyya ga dan uwa Bagizage  Nura Adamu Ahmed, tsohon Shugaban Gizagawan Kano kuma tsohon Shugaban Riko na Kasa na rashin mahafiyarsa Hajiya wadda ta rasu ranar Litinin da fatan Allah Ya jikanta da rahama, amin.

Daga Saminu Artillery Yelwan Shendam Jihar Filato 08032436477

e-mail: saminuartillery1@gmail.com

Kira ga masu tattaki

Edita ba ni fili in fadawa mutanen da suka yi tattakin murnar cin zaben Shugaba Buhari a 2015 musamman wanda ya tako daga Legas zuwa Abuja cewa tunda ya ci zaben 2019, ya dace su kara yin wani tattakin, yakamata su zagaye dukkan Jihohin kasar nan ba tare da sun shiga mota ba. Ina taya Maigida murna, Allah sa alheri, ‘yan takarar da suka fadi, su yi hakuri, haka zabe ya gada, su san cewa Allah na tare da masu hakuri, su zo a taru a gina kasa. Addu’armu Allah zaunar da kasa lafiya, ya bamu shugabannin kirki masu tausayi.

Daga Amiru Isah Bakori. 08084213547.

Fatan karin lafiya ga IBB

Salam Edita, Ina ma tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida, barka da zuwa da fatan Allah ya kara maka lafiya Ya tabbatar da alherinsa Ameen.

Daga Umaru Faruk Garba Makarfi. 08025160316

Kira ga Hukumar Zabe akan rage jam’iyyu

Assalam Edita, yakamata hukumar zaben Najeriya ta rage yawan jam’iyyun siyasar Najeriya domin buga hotunan jam’iyyun  barkatai nasa ka rudani na rashin saurin gane jam’iyya.

Daga A.U Shuwaki Jihar Kano 08063511757.

Jinjina ga ‘Yan Bauchi!

Assalam Edita, Ina mai yabo gami da jinjina ta musamman ga al’ummar jaha ta wato Bauchi bisa yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka yi ruwan kuri’u ga Sanata Bala Kauran Bauchi, hakika mutanen Bauchi wayayyu ne a harkar siyasa. Allah yasa hakan ya zamo mana alheri amin.

Daga Nasiru Albani Bauchi 08167155483.