✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Yauwa, yauwa, yauwa! Ina kuke masu ninkaya a kogin FDK, ina dauke da dimbin sakonninku. Kamar yadda na sanar a makon jiya, wadansu sun kada…

Yauwa, yauwa, yauwa! Ina kuke masu ninkaya a kogin FDK, ina dauke da dimbin sakonninku. Kamar yadda na sanar a makon jiya, wadansu sun kada kuri’unsu daidai, inda wadansu suka zabi GIDAN FARIDA, wadansu kuwa suka canki GIDAN SARATU, a yayin da wadansu ba su zabi kowane gida ba. Wadansu sun sanya sunayensu da lambar wayarsu a jikin sakonsu, wadansu babu ko daya. Don haka, ina kira ga masu aiko da sako su daure su rika rubuta sunayensu da adireshi, mai son a buga lambarsa, sai ya rubuta hade da sakon. Kai-tsaye, bari mu fara zayyano sakonnin naku:

Daga Sarauniya Ayshart Abdulhameed Gombe (07034815180):

Gaskiya FDK muna jin dadin wannan shafin kuma muna nishadantuwa da Labarin Farida. Ni dai ina Gidan Saratu Amarya.

Daga Abdulmalik Kabir Ghude:

Amincin Allah ya tabbata a gare mu gaba daya ma’abota karanta jaridar AMINIYA mai albarka. Fatan alheri ga FDK, ina mika sakon gaisuwa ga Gizago.

Daga M. D. Hidima (08027778930):

FDK, an ce mai kaza aljihu… domin kuwa wannan littafi kamar a gidana kake zaune kuma kamar a duk mako wannan fili naka ba ya wuce ni. To ka ci gaba da fadakarwa irin wannan, domin da yawa takan zama izna ga mutane. Na gode.

Daga Abdul Ahmad Garki Abuja (08093364369):

Barka dai FDK, yaya aiki da fatar kana lafiya kuma jinjina ga ma’abuta wannan shafi na Dausayin Kauna da fatar kowa lafiya. FDK, muna jin dadin wannan littafi na Uwargida Farida kuma ban dade da shigowa wannan shafi ba mai albarka. Ina gidan Uwargida Farida, Allah Ya kare ta daga sharrin Saratu, amin. Allah Ya kara basira.

Daga Bashar Garba Dukamaje Sakkwato:

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka, Shugaba FDK da fatan kana lafiya. Allah Ya sa haka, amin. Ina so a isar min da gaisuwata ga ’yar uwata, Rahamatullah Ukashat Kwantagora.

Daga Fatima Ibrahim (09027589246):

FDK, ina maka fatar alheri a koyaushe, Allah Ya kara daukaka Aminiya da kuma wannan shafin mai albarka. Na gode.

Daga Balkisu Yahuza Bauchi:

Assalamu alaikum. A gaskiya labarinka na Malam Shagalalle ya kara mini  zuhudu. Allah Ya saka maka da alheri, amin.

Daga  Al-Amin Saul Gombe (09028249639):

FDK, fatar alheri gare ka. Gaskiya mu ’yan Gombe muna matukar jin dadin wannan labari. Muna godiya kuma ka huta lafiya.

Daga Y. Y. Dantsoho Kaduna:

Ni dai ina gidan Saratu Amarya, dari-bisa-dari.

Daga Salmah Garba Chiroma (08067691489):

Assalamu alaikum, barka da wannan lokaci kuma ina mika sakon gaisuwata ga FDK. Gaskiya ina jin dadin wannan labari na Farida. Da fatar Allah Ya sa mu karu da abin da muke karantawa, amin.

Daga Muhammad Abubakar Area 11 Garki Abuja (09099130055):

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka FDK, Gaskiya ina tare da Saratu Amarya.

Daga Usamadeen S. Aliyu (08067569646)

Assalamu alaikum, ina mika gaisuwata ga FDK, ina jin dadin wannan labari na Farida. Allah Ya kara lafiya da fasaha, amin.

Daga Beauty ’Yarbaba (08033383219)

Ni ma a gaskiya abin da ke faruwa a wannan zamanin namu, abin na daure wa mutane kai, amma ni kam shawarata ita ce zaman lafiya. Mu so junanmu da soyayya da kauna. Ina fatar alheri ga Aminiya.

Daga Isma’il Ali Kaduna (07060874101):

FDK, ina yi maka fatan alheri da sauran masoyan Dausayin Kauna. Don Allah ka gaishe mini da Khadija Abdullahi. Na gode, Allah bar zumunci, amin.

Daga Abba Bade:

Assalamu alaikum, ina mika sakon gaisuwata ga dukkan mambobin wannan gida masu albarka. Gaskiya Oga mai gayya FDK kana kokari da wannan labari da kake ba mu, Allah Ya saka da alheri, amin-summa-amin.

Daga Nura Ahmad Meli (08129659331):

Assalamu alaikum FDK, ina yi maka fatar alheri da duk mai bibiyar wannan shafi mai farin jini kuma ina neman a taimaka mana da addu’a, matata ta Haifa min da namiji; da fatan Allah Ya ba su lafiya ita da jariri, amin.

Daga Murtala Aliyu Baiti Birni Kebbi (08038519577):

Assalamu alaikun FDK, ina fatar kana lafiya. Ni dai ina Gidan Saratu, kuri’ata na ba Saratu.