Search
Subscribe
Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Tare da gaisuwa, bari kai-tsaye in tafi kan jibgin sakonnin da kuka aiko zuwa akwatina. Amma kafin sannan, ni FDK, ina kara ba ku hakuri saboda karancin fili, kadan daga cikinku ne ke dacewa da shiga wannan fili. A ci gaba da bibiya da hakuri:

Daga Yahaya Abdullahi Yamama (08143546257):

FDK, da fata kana lafiya amin. To, ni dai ina Gidan Saratu. Dalili kuwa shi ne, har yanzu ban ji dalilin da zai hana Alhaji Baba ya kara aure ba.

Daga Isa Usman Tumu:

FDK, ina jinjina gare ka da wannan labari na Farida mai cike da darussa a rayuwa. Allah Ya sa mu amfana da darussan da ke ciki, amin.

A. A. Yahuza (07067539862):

Ina mika gaisuwata gare ka FDK da kuma duk wanda ke bibiyar wannan filin. Ina gidan Farida.

Daga Zainab M. Ahmad:

FDK, barka da kokari. To, a gaskiya ni ina bayan Uwargida Farida saboda da tsohuwar zuma ake magani. Ina yi muku fatar alheri.

Daga Faisal Usman:

FDK, mu dai a nan Mayo-Belwa muna gidan Uwargida Farida, domin ba mu goyon bayan Alhaji Baba ya yi mata kishiya.

Daga Abdul’aziz Abuja (08027282229):

FDK, ina maka fatar alheri da duk masu bibiyar wannan shafi mai farin jinni. Ina gidan Alhaji Baba.

Nura Ahmad Meli (08129659331):

Gaisuwa ta musamman ga FDK da masu bibiyar wannan shafi mai albarka. Muna kira ga Farida ta ci gaba da addu’ar Allah Ya kare ta daga sharrin ’yar zamani kuma ta ja hankalin mijinta cikin natsuwa, ba da tashin hankali ba.

Daga Khairat Bashir Khamis Kontagora:

Ni kam kuri’ata ta gidan Saratu ce.

Daga  Alhaji Husaini Tsoho Imawa Kura:

A kullun  ina bibiyar wannan labari na Uwargida Farida da mijinta Alhaji Baba da budurwarsa Saratu. Ki yi hakuri  Uwargida Farida, kowa da halinsa zai zauna. Idan an yi  auren, in ba tsakani da Allah take son Alhaji Baba ba, wata rana ke ce za ki fito kina rabo. A yi hakuri, in Allah  Ya yi zai aure ta, sai ya aura. Shawarata ga mata da maza, a dai rike amanar juna.

Anisat Abdullahi Adamu Daura (07067716102):

FDK, ina maka  fatar alheri. Ni dai ina gidan Saratu, kamar yadda soyayyar Alhaji da Saratu ke ruruwa a zukatansu da kuma yanayin zamantakewar addini da ya ba da damar auren fiye da mace daya, yana da kyau su yi aure don za su yi zaman lafiya tare da mutunta juna, ita da kishiyarta.

Daga A.B.A Gangaren Pandogari:

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka ya kai Filfilon Dausayin Kauna (FDK)! Da fatar kana cikin koshin lafiya. Allah Ya bar mana kai, Ya sa ka fi haka, amin-summa-amin. A gaskiya ni ba bako ba ne a wurin karanta wannan shafi amma ni bako ne wurin aiko da sako, da fatar za a karbe ni hannu biyu-biyu. Allah Ya daga jaridar Aminiya, amin.

Hussain Danjari Umar Kadarko Katsina (08038810162):

FDK Allah kara yi maka addu’ar nisan kwana mai amfani. Ina neman sarautar FDK saboda amfani da karuwa da ilimi tare da zumunci da ake samu. Jama’a, mu dubi labarin kishi, mu kiyaye shi.

Daga Mahmud M. Rabi’u Garkuwan FDK Fatakwal (08153836559):

FDK, ina yi maka fatar alheri, yaya aiki? Allah Ya yi mana jagora, Ya kara basira, amin.

Daga Aliyu Korau Bajari Ibbi (07013322949):

FDK, ina goyon bayan Farida don na gamsu da hanzarin da Khadija Abdullahi Abuja ta kawo a ranar 25/10/2019. Saboda haka ina tare da Farida.

Daga Barrister Umar (07034497275):

FDK, ina mika sakon gaisuwata gare ka da dubban masoya wannan fili. Labarin Farida yana matukar burge ni, musamman labarin Malam Shagalalle. Allah Ya ba mu ikon gane gaskiya, amin. Kwanakin baya na ba ku labarin wata budurwata wacce muka bata tsawon lokaci. To yau ma labarinta ne zan kawo. Wannan lokaci ina matukar farin ciki, domin Allah Ya daidaita tsakaninmu da ita. ’Yan uwa masoya, ku taya ni da addu’a Allah Ya albarkaci soyayyarmu kuma wannan fili shi ma Allah Ya albarkace shi, amin.

Daga Siyama Daura (08067437526):

FDK mazan fama! Da fatar kana cikin koshin lafiya, muna godiya kwarai da gaske tare da fatar Allah Ya kara maka imani da alheri saboda muna karuwa da wannan fili na Dausayin Kauna. Daga karshe, ina mika sakon gaisuwa da fatar alheri ga mabiya wannan fili mai albarka,  amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin