Search
Subscribe
Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili, ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya. Haka kuma ina ba masu aiko da sakonni ta tes din waya, cewa su rika turowa ta WhatssApp (08020968758) ko ta I-Mel, bashir@dailytrust.com maimakon ta waya, domin layin sakon na waya ya samu matsala, yana hana sakonnin shigowa. Allah Ya sa mu dace. A wannan mako kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

Daga Abdul Ahmad Garki Abuja:

Barka da warhaka babban yaya, da fatar kana lafiya tare da sauran ma’abota wannan shafi na Dausayin Kauna mai albarka. Allah Ya kara basira, amin. Ni ne naku har kullum.

Daga Yusif Adam Rijiyar Lemo Kano:

FDK, ya kuke, kuna lafiya? Ni sabon dalibi ne. Ni dai sakona zuwa ga masoyana ne, wato A’isha Gombe da Isma’il Kano.

Daga Aliyu Bala:

FDK, da fatar kana lafiya. Gaskiya kana namijin kokari a kowane mako, da fatar Allah Ya ja kwana. Ya kamata Uwargida Farida ta sa ranta a inuwa, ta maida duk al’amarinta ga Ubangiji, Shi zai mata magani.

Raheenat Kofar Mazugal Kano (09036444468):

Fifilon Dausayin Kauna (FDK), ka ba ni dama in mika fatar alheri gare ka da kuma daukacin masoya wannan shafi mai albarka. Bayan haka, muna matukar jin dadi da yadda aka sake maimaita mana Labarin Uwargida Farida. Muna bibiya duk mako, don jin yadda za ta kaya. Bayan haka, zan yi amfani da wannan dama in gaida masoyana maza da mata a ko’ina suke a fadin duniya, musamman jarumina, tauraro daya mai haskaka zuciyata.

Daga Isma’il Ali Kaduna:

FDK, ni ne naka, bakon masoyi a Dausayin Kauna. Fatar alheri a gare ka. Shugaba FDK, ka ba ni dama in yabi masoya wannan gida, ina son ku sosai, bye-bye.

Daga Abdulmalik Kabir Ghude (08056717265):

Gaisuwa mai tarin yawa ga uwardakina Uwargida Aunty Farida. FDK, hakurinta ya yi mini, ta dau hanya madaidaiciya da ta riki hakuri amma ya kamata ta nuna wa duniya ita ma ’ya ce mai ’yancin zama da mijinta, sannan kuma ai kishiyar gida ba ita ce abar ki ba, kishiyar waje ce mafi cutarwa. Gaisuwa gare ki Uwargida Farida!

Daga Ahmad Yahaya G. (07062157794):

FDK, fatar alheri da dimbin godiya mai yawa. Ina yi wa abokiyata Khadija Abdullahi Abuja da sauran ma’abota bibiyar wannan shafi fatar alheri. Ni dai a gaskiya ina matukar goyon bayan Alhaji Baba da kuma amaryarsa Saratu.

Daga Sultanah S. Aliyu Sheka:

Assalamu alaikum FDK, Ni kam gaskiya ina gidan Saratu. Ina mika gaisuwata ga FDK, Allah Ya kara daukaka, Ya ba ka abin da kake nema. Muna godiya sosai.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin