Da Dumi Dumi

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili! Ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya. Haka ina ba ku shawarar ku rika turo sakonninku ta WhatssApp (08020968758) ko ta I-Mel, bashir@dailytrust.com Kuma ku rika sanya suna da adireshi da lambar waya a kasan sakon, idan kuma ba ku son a saka lambar wayarku a jarida, sai ku sanar. Har yanzu dai muna kara tambaya, wane gida kuke? GIDAN UWARGIDA FARIDA KO GIDAN AMARYA SARATU? Allah Ya sa mu dace. A wannan makon kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

 Umar Kano Sarkin Yakin Dausayin Kauna:

FDK, ni dai ina tare da Uwargida Farida. Ai ba ta hana shi auren ba, sai dai ta san bai yi dacen samun mata ba. Saboda tun yanzu tana jan shi zuwa wurin fati, wata rana sai ta ja shi zuwa otel; ya manta da iyalinsa a gida.

Daga Usman Sarki Oil Rafindadi Katsina (08032612292):

FDK, a gaskiya ina jin dadin sauraron wannan labari na Alhaji Baba da uwargidansa Farida da fatar Allah Ya kara gudunmawa, amin.

ADVERTISEMENT

Daga Badiyya Rabi’u  Malumfashi:

FDK, barka da warhaka, da fatar kana lafiya. Na kasance mai bibiyar wannan shiri naka shekara da shekaru. Allah Ya kara basira. Ni dai ina bayan Uwargida Farida, domin har yanzu ba mu san yaya halin Saratu yake ba.

Daga Shamsuddeen M. Sani  Suleja (08036160154):

Barka da warhaka FDK garkuwar masoya! A gaskiya zan iya cewa na fi kowa murna da jin dadin wannan labarin na Uwargida Farida, domin labarin ba ya wuce ni a kowane mako. Allah Ya saka maka da alheri. FDK, ni ina tare da Uwargida Farida dari-bisa-dari, lura da kuma samun karin hujja daga Anty, wato yayar Alhaji Baba. Bincike yayin neman aure yana da matukar tasiri sosai, ga shi kuma yana da tushe a cikin addinin Musulunci. Allah Ya hada mu da masoya nagari, amin.

Daga Wani ba suna:

Gaskiya akwai alamar gaskiya tare da Farida.

Daga Safiyanu S. Nuhu (08082262381):

FDK, Allah Ya kara basira da nisan kwana mai amfani. Gaskiya FDK muna rokon addu’a a wannan fili mai albarka, bisa wani al’amari da ya shafi kanena. Soyayya kamar wasa amma sai wahalar da shi take yi. Abin kamar a fim, sai ka ji yana kiran sunan yarinyar kuma mahaifinta ya ce ya yi mata miji. Wallahi ni dai abin ya fara tayar mini da hankali. Ina neman shawararku ’yan uwa na wannan fili mai albarka. Allah Ya daukaka Aminiya, amin.

Nasiru Kainuwa Hadeja (0810022968):

Mutunci ya fi kudi. A yau idan ka ji an rusa auren da kake shirin yi, to kai talaka ne. Wani sai biki ya zo daf sai a ce maye ne ko kuma a bankado wani mummunan hali a danganta ka da shi. Wani kuma cewa za a yi talaka ne, ba zai iya rike matar ba. Amma idan kai attajiri ne babu mai yi maka binciken kwakwaf. Ya Allah Ka azurta mu da halal, Ka yi mana tsari da talaucin da za a rika mana kallon kaskanci, amin.

 

 

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya