Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Taskar tarihi: Misalai daga wakokin Malam Maharazu Barmu Kwasare

Dano Balarabe Bunza

Tarihin da taskar ke dauke da shi a yau shi ne na wani al’amari mai ban tsoro da tashin hankali da ya faru a ranar wata Juma’a a 1970 a cikin masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dan Shehu Usmanu Dan Fodiyo wadda ta yi daidai da 1363 Miladiyya. Akwai kuskuren rubuta kwanan watan da aka samu daga marubucin domin abin da ya fada duk da yake ba ya duniya a wannan shekarar da ya rubuta:

Shekarar dubu da dari hudu da goma sha ukku,

ADVERTISEMENT

Yau kun ji saura mu zanka zuwa masallaci.

Da zazdu mubazdiyya jaz ukku hakkan,

ADVERTISEMENT

Zaigu abin yaz zamo rikta masallaci.

 

An tabbatar da rasuwar Malam Maharazu Barmu Kwasare a 1400 Bayan Hijira wadda ta yi daidai da 1979 a cikin tarihin da ya gabata. Bayan haka kuma, an yi hira da Dokta Bello Bala Usman da ya fadi cewa, an kai su ziyarar gani da ido a masallacin a 1975, aka gwada musu tarin takalman da mutane suka bari wajen gudun ceton rai lokacin da abin ya faru, kuma 1975 ta yi daidai da 1396 Bayan Hijira. Wannan ya kara tabbatar da cewa akwai kuskuren rubuta kwanan wata da marubucin ya yi lokacin da ya rubuta wakar ba yadda ya ambaci cewa 1413 wadda ta yi daidai da 1992 ba.

Ana iya cewa al’amarin da ya faru a masallaci tamkar ko dai iska ya zo ya iske ka ba na rawa ne domin, ana cikin halin dar-dar ko da tashin hankali ne ya faru a masallacin. A daidai lokacin da abin ya faru ana cikin Yakin Basasan Najeriya da aka share shekara uku ana fafatawa wato daga 1967 zuwa 1970. A ranar wannan Juma’a ne aka samu wadansu yara mashiririta suna yawon harbin tsuntsaye cikin gari har suka iso masallacin daidai lokacin da liman ke kan mumbari yana huduba. Taron mutanen da suka zo masallacin Juma’a Sallah bai damu yaran ba. Abin da ya dauke musu hankali kawai shi ne tsuntsayen da suka gani na shiga da fita a cikin masallacin. Tsuntsayen da ke shiga da fita cikin masallacin hasbiya ne. Jama’a na zaune cikin shakkun yakin da ake yi na basasa don kada a tarar da su cikin masallaci. Saboda haka, zuwan yaran masallacin tamkar kara wa wuta man fetur ne. Wannan ya sa Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ce:

Yau shekara uku tashin hankali da yawa,

Gida da daji balle masallaci.

Hadari da haufi da ru’uba sun game mu duka,

Tsoro da shakka akwai su gare mu ajamanci.

 

A cikin baitocin da ke sama ana gano cewa Malam Mahrazu Barmu Kwasare ya rubuta wakar bayan al’amarin masallaci ya faru a shekara uku wato 1967 zuwa 1970. Ita kuma wakar Malam Maharzu ya rubuta ta a 1970 daidai.

Da isowar yaran masallaci da ganin tsuntsayen sai suka raba wa juna aikin yadda za a yi harbi. A bayyane suke magana yadda ake jin su. Don haka hankali ya rabu dangane da wa ake saurare, liman da ke huduba ko yara masu harbin tsuntsaye? Yaran sun iso masallaci kuma sun tarar da abin da suke nema wato tsuntsaye masu shiga masallaci suna fita. Da ganin haka, kowane yaro ya je ya tare kofar masallaci daya da azamar duk tsuntsun da ya fito daga cikin tsuntsayen ya harbe shi. Abin da suka rika fada wa juna bayan sun tare kofofin masallaci kamar haka:

“Kai ka tare waccan kofa ni kuma in tare wagga kai kuma, ka fake waccan duk wanda ya fito (Tsuntsu suke nufi) mu harbe shi. Ni zan harbi na gaba, ni kuma in harbi na baya. Ni ko a bar mini babbansu in ya fito in harbe shi.”

Jama’ar da ke zaune ckin masallaci suka yi tsammanin mayakan da suke shakku ne suka iso, nan da nan hankalin kowa ya tashi, aka fita batun sauraren liman balle batun sallar da sai an kammala huduba. Fadar ni zan harbe babbansu ya sanya liman ya dauka shi ake nufi ba tsuntsu ba. Wadansu da motoci suka zo wadansu da hwandodi wadansu kuma da kekuna. Wadansu sun zo da rakuma, wadansu kuma da jakai. Haka kuma, wadanda suka zo da kafafu ba a san adadinsu ba. Wadanda suka zo da ababen hawa suka fita batunsu suka kama kansu suna gudun ceton rai. Wadansu mutane ba su tsaya jiran su fita ta kofar masallaci ba, gini suka hau domin jiran fita ta kofa bata lokaci ne kuma, komai na iya faruwa kafin mutum ya fita ta kofa saboda yawan jama’a. Malam Maharazu Barmu Kwasare na cikin masallacin lokacin da abin ke faruwa. Wadansu sun dauki cewa mutuwarsu ta zo wadansu kuma sun labe a masallaci suna jiran mutuwa ta zo ta dauke su. Lokacin da ake gudun wadansu sun fadi kasa ana taka su. Wannnan ya sa Malam Maharazu ya zayyana faruwar lamarin kamar haka:

Ai in ana haka na san ana tawaye,

Wani kila sai ya yi bauli masallaci.

Ga malfuna ga rawunna ga kubuttayye,

Duka an watce da darduma masallaci.

An bar agoginne da hulluna kube,

Dan tazbaha yai dubu zangu masallaci.

An karkashe jalluna an bar gafakkinne,

Ga sanduna ga akwamayye masallaci.

Wasu hailala suka yi wasu maula wasu Tijjani,

Wasu sunka dora kira masallaci.

Wasu ko suna kira wasu ga su kwance kasa,

An turmuje su ana taki masallaci.

Wasu sun fake nan ga ginoni suna nishi,

Mutuwassu ta zaka sunka aza masallaci.

An bar dawaki da basukurai da rakumma,

Wurin gudu a baro fanda da motoci.

Wani ko shiga dai gidan kulli a ji shi daka,

In mai gida ya girshe shi su kama rikitoci.

Yaro guda ukku na su sunka cuce mu,

‘Yan akhiruz zamani na ba su gijibirci.

 

Duk wannan tashin hankali da yaran suka yi sanadin faruwarsa Malam Maharazu Kwasare bai tsine musu ba sai dai ga abin da ya ce:

Yaran ga Allah shi shiryasshe su mun roka,

Shiya na fi so hawa ginat masallaci.

 

Bayan haka, ba a samu labarin mutuwar ko mutum daya ba sai dai mutane da yawa sun jikkata. Dangane da wadanda suka ji rauni kuma, Malam Maharazu Barmu Kwasare ya roki Allah Ya ba su lafiya kamar haka:

Wadanda duk an ka jima Jalla mun roka,

Ka saukaka musu su yi ta zuwa masallaci.

 

Abin da duk ya sanya mutum ya bar abin hawan da ya zo da shi masallaci don ya tsira da rayuwarsa ba karamin abu ba ne, kuma ba abin da ke sa yin hakan sai tashin hankali mai tsananin gaske.

Masallacin na cikin masallatan da aka kawata a wancan lokaci kamar yadda Malam Maharazu Barmu Kwasare ya bayyana a cikin wasu baitocin wakarsa kamar haka:

Kaddu kakai wani zamani kawat gina,

Don sun ji an yi kawa da yawa masallaci.

Ka ta da kai bisa sai fularka ta fadi,

Da gambuna masu mamaki masallaci.

Balle cikin mimbari zainun ala zainun,

Wani har shi mance abin da shikai masallaci.

Da lasifika da fanka ga dabe laushi,

Da shimfida wadda babu iri masallaci.

Shi na ka kai wasu ba sharadin batun jima’a,

Su zo su tattare filaye masallaci.

 

Idan aka yi la’akari da abubuwan da Malam Maharaz Barmu Kwasare ya bayyana a cikin wakarsa ta masallaci babu shakka mai karatu zai aminta  cewa, tana dauke da tarihin wani al’amari babba da ya faru cikin masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dan Shehu Usmanu Danfodiyo a 1970.

Kamar yadda aka samu tarihi a cikin wasu wakokin Malam Maharazu Barmu Kwasare da aka gabatar, haka ma akwai wata waka mai dauke da tarihi a cikinta mai suna ‘Wakar Kurma’. Wannan kurma shi ne Malam Maharazu Barmu Kwasare ya sifanta a cikin wakar yana shammatarsa a kan wani dalili da za a kawo gaba kadan. Malam Maharazu ya hadu da kurman sanadiyyar zuwan da ya yi wani kauye bakunci saboda wata lalura da ta kama shi.

Malam Maharazu Barmu Kwasare na zaune kofar gidan da ya sauka kuma lokacin kalaci ya yi. Daidai lokacin da aka kawo wa Maharazu abincin dare, an yi daidai da wani kurma ya zo wurin. Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ambaci dalilin zuwansa kauyen a cikin wani baitin wakarsa kamar haka:

Na zo kauye bakunci lalura,

An kawo min tuwo an iske kurma.

 

Halin bakunci da rashin sanin halin kurma sai Malam Maharazu ya taya wa kurma abincin da aka kawo masa saboda bai dace a sami bako kuma malami da rowa ba. Haka shi ma kurma da mutum ne mai natsuwa da sai ya ce malam ya ci gaba. Idan ya dace Malam ya rage sai ya ci ragorar da Malam ya bari amma ina! Malam bai sani ba ashe tare yake da sahibul jinnu. Lokacin da Malam Maharazu ya taya wa kurma abincin da wanke hannunsa da fara cin abinci nan take ne. Ga abin da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya fada dangane da kiran da ya yi wa kurma don su ci abinci kamar haka:

Dada sai nit taya mishi dan dibara,

Sai yay yo farat yaj jefa hannu.

 

Daga nan ne abin da ya faru tsakanin kurma da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya faru. Malam Maharazu na cikin cin abinci da kurma sai ya gano kurma bai da natsuwa ko kadan. Gano haka da Maharazu ya yi sai ya cire hannunsa ya bar wa kurma shi kadai yana ci. Cire hannun da Maharazu ya yi ya zama wa kurma abin farin ciki domin, zai cika cikinsa sosai. Ga abin da Maharazu ya fada da ya sanya shi cire hannunsa ya bar wa kurma kamar haka:

Dole da nit taba nit tashi nik kau,

Ina kallo na mamaki ga kurma.

Murna dai shikai na debe hannu,

Na sa mai ido shi dai ka sulma.

 

Daga nan ne Malam Maharazu Barmu Kwasare ya zuba wa kurma ido yana kallon yadda yake cin abinci ba tare da natsuwa ba. Kallon da ya yi wa kurma lokacin da yana cin abincin ya sanya shi fadin abubuwa kamar haka:

In ya debo loma wa mutum nan,

Awa mai gina zaure ya yi talma.

Shina wahala wajen hadiyar abinci,

Shina wasu runtse-runtse kamar shi suma.

Lishib shika yi awa shi an ka kai ma,

Bakinai awa an bude homa.

Zai diba kamar bai tamna loma,

Yadin fammi yadin ina’i kurma.

Kamar wada rakumi shika wa abinci,

Bakinai kaman an bude homa.

 

Malam Maharazu Barmu Kwasare ya siffanta yadda kurma ke cin abinci a cikin baitocin da aka kawo a sama kuma, shi ne dalilin da ya sa ya cire hannunsa ya bar wa kurma. Kai tsaye Malam Maharazu ya gane cewa kurma ba kammalallen mutum ba ne. A kan haka ga abin da Malam Maharzu Barmu Kwasare ya ce:

Mutum ba hankali kuma ya ji yunwa,

Ina kaka bas hi dama har ya ji ma?

 

Malam Maharazu ya kara da cewa, ya cire hannunsa saboda hana cin abinci da aka yi da wanda ba ya da natsuwa kuma, shi ya sa ya cire hannunsa ya bar wa kurma domin biyar shari’a in da ya ce:

An hana cin abinci da masunyuna,

Cikin Ta’alimi can aka bayyana ma.

 

Haka kuma, Malam Maharazu ya kara fayyace cewa kurma ba mutum ne mai ilimi ba balle ya san abin da ya dace ya yi da wanda bai dace ba balle ya bi ka’idar yin kowane aiki. Dangane da haka, ga abin da Malam Maharazu Kwasare ya fada:

Ba shi da sarmakandi bale shi duba,

Tsoron malmaa shika balgace ma.

Bai iya tsai da hannunai gabansa,

Ballanta shi buda miya ta zo ma.

 

Gano halin kurma da Malam Maharazu ya yi tun farko na daga cikin abin da ya taimaka masa kwarai da gaske da kurma ya ji masa inda bai cire hannunsa cikin kwanon abincin da aka kawo masa ba. Ga abin da Malam Maharazu ya ce dangane da haka:

Nan kuma arzikinka ya huda dutci,

Da kat taba ci kadan kab bar ma kurma.

Inda ka tsaya kun tara sudi,

Akaifu ag garai da sais hi ji ma.

 

Dano Balarabe Bunza, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo, Sakkwato.

danobunza@yahoo.com, danobunza@gmail.com