✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tatsuniya ce cewa karfin arzikin Najeriya ne mafi inganci

A ‘yan kwanakin da suka shige ne aka fitar da wata sanarwa mai ban takaici da dariya a lokaci guda kuma ta yi kama da…

A ‘yan kwanakin da suka shige ne aka fitar da wata sanarwa mai ban takaici da dariya a lokaci guda kuma ta yi kama da almara ko tatsuniyar gizo da koki, inda Ofishin Kididdige na Najeriya ya bayyana cewa karfin arzikin Najeriya da ake fi sani da Gross Domestic Product (GDP) shi ne mafi karfi a duk nahiyar Afirka, sannan na ashirin da shida a duniya.
Tattalin arziki na habakane  ta hanyar samun dawwamanman zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma, da kan ba su damar gudanar da harkokin kasuwanci da kai koma cikin natsuwa.
 A yau a Nijeriya kowa cike yake da tsoro da fargaba, sakamakon halin da muka samu kanmu na kashe– kashen mutane ba gaira ba dalili. Sai a tarar da mutane a gidajensu a garuruwansu a kashe na kashewa, a raunata wadansu, a kone gidajensu da dukiyoyinsu, su fantsama gudun hijira domin tsira da rayukansu. Ta yaya al’ummar da ba ta cikin aminci, ta zauce, ba ta cikin hayyacinta sanadiyyar tashe tashen hankula, a ce tattalin arzikinta na habaka, idan ba yaudarar kai bai!
Wutar lantarki na taka muhimmiyar rawa a duniya wurin bunkasa tattalin arzikin kasa. A halin da muka tsinci kanmu a yanzu na rashin wuta da makamashi ya janyo durkushewar masana’antunmu da kamfanoni.
Duk da miliyoyin daloli da gwamnotoci suka yi ta narkarwa domin ingantawa da samar da wadataccen  wutar lantarki amma al’amarin ya gagara.
 Ilimi shi ne kashin bayan ci gaban dukkan manyan kasashen duniya, da ilimi al’umma take daukaka ta kai dukkan wani matsayi da kololuwar daraja a rayuwa. kasar nan ilimi ya fada cikin mawuyacin
hali sanadiyyar rikon sakainar kashi da hukumomi suka yi wa bangaren.
Rashin kayan aiki da kwararrun malamai da kuma yajin aikin da ya zama ruwan dare sun kassara harkokin iliminmu.
A watannin da suka wuce ne aka fitar da wata sanarwa mai kunshe da bayanin miliyoyin yaran da
Ba sa zuwa makarantar firamari a Nageriya. Ta wace hanya al’umma za ta gina kasa har tattalin arzikinta ya habaka, alhalin tana cikin duhun jahilci?
Abin tambaya shi ne, wadanne alkalumma ne aka yi amfani da su wurin gudanar da kididdigar? Ba na tsammani an bi ta kan talakawan kasar nan d ake dandanar bala’in matsi da kangin bakin talauncin da ya mamaye musu rayuwa.
A kididdigar da babban bankin duniya ya fitar, ya nuna cewa Najeriya ce kasa ta biyu daga cikin kasashe biyar da talakawa suka fi tagayyara a duniya. Inda talakan kasar nan ke rayuwa a kasa da Dala daya a kullum! Ka bi kan tituna ka ga yadda mutane suke ta gararamamba da karakaina domin samun abin sakawa a bakin salati. Dubi abin da ya faru a jarabawar daukar sabbin ma’aikata a hukumar shige da fice, inda dubban daruruwan matasa suka halarta, alhali guraben mutum dubu hudu da dari biyar ne kadai. Wannan alama ce da ke nunar da yadda talauci da rashin aikin yi ya mamaye al’umma. Fashi da makami, sata da zamba da kuma garkuwa da jama’a sun zama ruwan dare a kasar nan. Cin hanci da rashawa tuni suka samu gindin zama a kusan dukkan ma’aikatun gwamnati sun zama abin alfahari da ado a kasar nan, kuma a ce tattalin arzikinta na bunkasa, lalle abin akwai ban dariya.
Har ya zuwa yanzu a kasar nan akwai masu shan ruwan rafi, korama ko tafukka. Ka shiga karkara ka ga yadda suke rayuwa. Duk tsawon lokacin da aka dauka da  komawa mulkin dimokuradiyya, mun kasa samun ababen more rayuwa. Kullum sai dai alkawuran karya da shaci fadi.
 Mu talakawan kasar nan abin da za mu ce a nan shi ne, lallai tattalin arzikin ‘yan  tsirarun mutane ya habaka, tun da mun ga suna gasar sayen jirage da motocin alfarma masu sulke. Da kuma masu sace mana danyen mai da masu watandar baitulmalin al’umma domin  azurta kansu.
Allah Ya kiyashe mu da irin wannan bunkasar tattalin arzikin, inda mu talakawa ke fama da wahalar rayuwa, amma wai an ce kasarmu ce ta farko a karfin arziki a Afirka.
Injiniya Jibril Abdul Daura
08038997861 |