✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin Najeriya ya yi faduwa mafi muni a shekara 10

Durkushewan tattalin arzikin Najeriya na 2020 shi ne mafi muni a cikin shekara 10

A wani yanayi mai kama da kwan-gaba-kwan-baya, wani rahoto ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya kara tabarbarewa da kashi 6.10 cikin 100 a watanni shidan farkon 2020.

Wannan dai shine koma-baya mafi muni da kasar ta fuskanta a banageraren tun shekara ta 2010.

Alkaluman rahoton wanda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa raguwar kayan da ake samarwa na cikin gida (GDP) na nufin tsaiko a tagomashin da kasar ta dan samu tun bayan farfadowa daga masassarar tattalin arziki a 2016/2017.

Kazalika, rahoton na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani rahoton ya nuna cewa sama da mutane miliyan 21.7 ne ke fama da rashin aikin yi a kasar.

NBS ta ta’allaka koma bayan da annobar COVID-19 da ta shafi kusan dukkan harkokin jama’a ta hanyar da dakatar da tafiye-tafiye, rufe kasuwanni da makarantu da sauransu, wanda hakan ya shafi cinikayyar cikin gida da ma ta kasa da kasa.

Bincikenmu ya nuna cewa idan an kwatanta da shekara ta 2019 lokacin da ya ke ci gaba a matakin 2.12%, tattalin arzikin a bana ya sauka da kimanin kaso 8.22%.

Sannan an samu raguwa da maki 7.97% idan aka kwatanta da watanni ukun farkon wannan shekara. GDP kuma ya sauka da kashi 5.04% sabanin wata ukun farkon shekarar.

– A wani wurin ba laifi

Duk da haka bangarori 13 sun samu ci gaba idan an kwatanta da 30 din da su ka samu a wadan can watannin.

Duk da wannan koma bayan da aka fuskanta, bangaren Fasahar Sadarwar (ICT) ya samu tagomashi da kimanin kashi 17.83% a ma’aunin GDP.

Hakan na nufin bangaren ya karu da kaso 20.54 cikin 100 a gudunmuwarsa ga tattalin arzikin in an kwatanta da shekarar 2019.

Da ya ke tsokaci a kan ci gaban, Ministan Harkokin Tattalin Arzikin Fasahar Sadarwa, Isa Ali Pantami ya ce tagomashin abin a yaba ne.

– Masna tattalin arziki sun ce…

Sai dai masana tattalin arzikin sun ce rahoton bai zo musu da ba-zata ba musamman duba da muguwar illar da COVID-19 ta yi a bana.

A cewar wani masani, Mista Tope Fasua, hatta Naira biliyan biyu da miliyan 300 da Gwamnatin Tarayya ta saka don ceto tattalin arzikin ya yi kadan musamman idan an kwatanta da GDP din Najeriya da yawansa ya kai kusan Naira tiriliyan 160.

Ya ce tallafin bai wuce kaso 1.4 cikin 100 na GDP din ba.

Mista Tope ya ce kasashen da suka ci gaba da dama sun ware kusan kaso 10 cikin 100 na GDP a matsayin tallafin annobar; ko da yake ya ce su ma watakila don ba su cika fuskantar matsin tattalin arzikin ba ne.

“Kamata ya yi a ce mun ware akalla kaso 10% na GDP domin tallafa wa muhimman bangarori irinsu manyan ayyuka, noma, ilimi, wutar lantarki, samar da gidaje da dai sauransu”, inji masanin.