Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Tattaunawa kan yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (2)

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar a tsakiya a wajen wani taron Musulunci a Abuja a bara

Wannan wata tattaunawa ce mai muhimmanci da aka gudanar a shekarar 2014, inda Malam Kabiru Danladi Lawanti, malami a Jami’ar Ahmadu Zariya ya bude a shafinsa na Facebook, inda kuma wadansu masana suka tofa albarkacin bakunansu. Mun kawo kashi na farko na tattaunawar a makon jiya, yau ga ci gaba:

Malam Salihu Ishak Makera, shi ma ya shiga tattaunawar, inda ya ce: “Wannan ne dalilin da ya sa a kwanakin baya na yanko wani bangare na wakar marigayi Malam Sa’adu Zungur mai cewa: ‘Komai na Arewa da bambanci da na al’ummomi sun fi dari…’ Yanzu ne lokacin da ya kamata mu yi wa kanmu fada. Tabbas tafiyar da muke yi akwai babbar matsala. Musulmin Kudu sun yi mana nisa wajen tafiya da zamani. Jami’o’in Musuluncin da suka kafa sun kusan jami’o’i mallakar jihohin da Musulmi suka fi yawa a Arewa. Mu kuwa har yau ba kungiyar addini ta Arewa da take da ginanniyar babbar kwaleji da za a gani a fada. Amma wajen zagi da bata juna mu ne lamba wan!”

ADVERTISEMENT

Sai kuma Abubakar Saddikue Adam ya biyo da cewa: “A gaskiya malaman Izala suna matukar kokari wurin ganin cewa an taimaka wa gajiyayyu da marayu. Akwai asusu da ke kula da wannan bangaren. Gina makarantu kuwa abu ne mai kamar wuya, domin tafiyarwa da gudanarwa zai yi matukar wuya, lura da cewa akwai makarantu da yawa da Islamiyyu har ma da boko…sai dai asibiti, wannan kuwa yana da matukar muhimmanci. Kuma kai, kamar wajibi ne ma shi.”

Kabiru Danladi ya dawo da cewa: “Wadanda suke kusa da malaman nan dole su gaya musu.”

ADVERTISEMENT

Bai kai ga rufe baki ba sai Shehu Mustapha Chaji ya mayar masa da martanin cewa: Kabiru Danladi Lawanti, ku daina fakewa da wasu dalilai kuna ci wa malaman addinin Musulinci fuska! Da irin wadannan maganganu naka wani ke cewa ana kashe kudade zuwa Saudiyya hawan duwatsu alhali ga su a Jos! Komai da muhallinsa, zuwa taro daban gina makarantu daban. Kuma kowa da alkiblarsa! Wani yawon bin Buhari kamfen wani kuma kallon kwallo har Turai da sauransu. Ku tambayi masana su kara ganar da ku amfanonin gangami a tallata manufofi da akidu.”

Kabiru bai numfasa ba ya kalubalanci Chaji da cewa: “Shehu Mustapha Chaji, abin lura a nan shi ne, me tarurrukan suka kara mana a matsayin al’umma?”

Daga nan ne Bashir Yahuza Malumfashi ya shigo batun, yana cewa: “Shehu Chaji, don Allah ka yi wa batun nan adalci. Mu jefar da batun ra’ayi, shin da irin wannan abin za mu gina addini nagartacce? Na san ka san cewa ba haka al’amarin yake a kasashen duniyar Musulunci ba kuma ba za mu iya ci gaba ba idan muka ci gaba da haka. Allah Ya sawwake!”

Shehu ya sake ba Kabiru amsar cewa: “Kabiru Danladi Lawanti, abubuwa da dama! Wani a zatonsa Bahaushe ne kadai Musulmi amma in ya je tarurrukan addini sai ya fahimci ba haka ba ne. Jama’a na tattaunawa da juna, suna sanin matsalolinsu da shawo kansu. Hakan na cikin haduwar al’ummar Musulmi ranakun Juma’a da aikin Hajji. Mene ne hikimar haka?”

Shehu ya juya kan Malumfashi, ya ce masa: “Bashir Yahuza Malumfashi, a kasashen Musulmi ana tarurrukan gangami kan manufofi daban-daban. Matsalarmu a nan ita ce, mu ba da shawarar fitar da bayanai da za su kawo ci gaba da hadin kai a tsakanin al’umma ga baki daya. Sannan zamanantar da yadda kungiyoyin ke tafi da al’amurransu. Mutum nawa ne a nan da ke ware wasu kudade duk wata don taimaka wa “foundations” din addini, don yada ilimi da lafiya da sauransu?”

Shi ma Malumfashi ya biyo da amsa: “Chaji, yauwa, ka fara kama hanyar tunaninmu. Malaman nan na kungiyoyin dai, su za su share hanyar zamanantar da tsarin, su za su ja ra’ayin attajiranmu su rika fitar da zakka yadda ya dace, su za su kafa ‘foundations’ din da kuma gudanar da su, maimakon yawace-yawacen terere da la’antar juna.”

Malama Safiya Ibrahim ta shigo da cewa: “Amin, Malam Kabiru duniya ta tafi ta bar mu a baya, ba su farga ba (wa’azi yanzu kana daki ma sai ka yi duniya ta saurara). Allah Ya kyauta.”

Sai kuma Salihu Ishak Makera ya sake cewa: “Fada wa kanmu gaskiya ya zama wajibi a wannan lokaci. Ba wai maganar cin zarafin malamai ba ne kuma ba cewa aka yi alhakin canja salon tafiyar Musulmin Arewa na malaman addini ne kawai ba. Aiki ne da ke kan dukkanmu, attajirai da dalibai da malamai da sarakuna da almajirai da matan aure da kowa da kowa. Tilas mu sauya salon tafiyarmu mu mutanen Arewa, musamman mu Musulmi. Addininmu ba bakauyen addini ba ne, addini ne daidai da kowane zamani.”

Bayan karanta kashin farko na wannan tattaunawa, Malam Muhammad Sani Garba ya aiko da nasa tsokacin ta I-mel dinsa na abufatimat@gmail.com yana cewa:

“Na karanta bayanan ’yan uwa masu girma suka yi game da wannan mas’ala a wannan jarida ta Aminiya. Kuma a gaskiya na karu matuka. Ra’ayoyinsu sun wayar mini da kai bisa wasu al’amurra, hasali ma sun zaburar da ni domin ni ma in ba da gudunmawata daidai abin da na sani.

Shi dai addinin Musulunci na Allah ne kuma ya zama wajibi a kanmu mu ba da gudunmawarmu wajen gina shi, da yada shi da kuma kare shi daidai gwargwadon hali.

Na farko, kamar yadda yawanci na fahimci ra’ayin ’yan uwa na tarurrukan wa’azi ba su ne masu muhimmanci ba kan gina al’umma ta hanyar gina kamar makarantu da Islamiyoyi da sauran abubuwa masu kama da su. Alal hakika ban ziyarci Jos ba don in gani da idona amma na ga wata mujalla a laburaren Foliteknik ta Kaduna wadda Kungiyar Izala ta kawo. A nan ne na karanta cewa suna da makarantu na sakandare wadanda suke gwamatse da addini da boko sannan suna da cibiyoyin ilimi don raya al’umma.

Bugu da kari, ga shi sun kafa wata katafariyar tashar talabijin mai suna ‘Sunnah TB’. Gaskiya Kuma na lura mutane na amfana da wannan tasha mai watsa sakon shugabanmu Annabi Muhammadu (saw). Na karanta ko a jaridar Daily Trust ko jaridar Aminiya, cewa kungiyar tana shirin kafa jami’a insha Allahu. Bugu da kari daga cikin wa’azozinsu, ba inda ba su tabowa. Ina da faifan CD masu yawa na tarurrukansu da wa’azozinsu da sauran tarurruka wadanda suka tabo Ilimin Tauhidi da Nahawu da Mu’amala da sauransu.

Na biyu, ina kyautata zaton magabatan wadannan kungiyoyin na karanta Aminiya. Ina fatan za su gyara inda aka gaza kuma da fatan za a kara inda aka dace. Muna rokon Allah Ya sa dukkanmu mu dage wajen raya Musulunci da dukiyarmu da jikunanmu, amin. Sannan kuma daidaikunmu ya kamata mu taimaka wajen gina Musulunci ta hanyoyin: taimaka wa marayu su yi karatu da yi masu sutura da saya masu abinci da gina gidaje na wakafi da gina dakunan karatu da gina wajen kula da lafiya da fitar da zakkah yadda ya kamata. Allah Ya kara daukaka Musulunci da Musulmi. Amin.”

Za mu ci gaba