Search
Subscribe
Tawali’u

Tawali’u

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah domin yawan kaunarSa mara karewa zuwa gare mu. Barkanmu da sake saduwa cikin wannan mako, inda za mu ga yadda mai bi ya kamata ya zamana yana cike da halin tawali’u a cikin zamaninmu na yanzu. Bari mu ga abin da Littafi Mai tsarki ya fadi cikin Galatiyawa 5:22,23.

Littafi Mai tsarki na cewa: “Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamun kai. Masu yin irin wadannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su.”

Tawali’u ba sabuwar kalma ba ce, tawali’u hali ne  na kaskantar da kanka domin nuna kauna ga mutane. Ita wannan kauna da muke nufi a nan kuwa ba kauna tsakanin mace da miji, ko uba da da ko ’ya da uwa ko  dan uwa ko ’yar uwa ba ce, amma kaunar Ubangiji Allah da Ya ba mu a zaman albarkarSa Ya kuma nuna mana ta wurin aiko da danSa Yesu Almasihu don mu nuna wa juna ba tare da zabe ko nuna bambanci b. Gama Allah ba Ya nuna bambanci gare mu bayinSa, kowa na cin moriyar arzikin rayuwa da Ya ba mu zuwa tsawon kwannakin da Ya bai wa kowa cikin duniya, shi ya sa yana da muhimmanci mu bi tafarkinSa da Ya ba mu cikin Littafi Mai tsarki wato maganarSa. Domin maganar Allah jagora ce ga rayuwarmu, takan jagoranci ayyukanmu na yau da kullum haka kuma a duk lokacin da muka fuskanci jarabobi musamman wajen nuna kauna da tawali’u ga juna.

Rashin hakuri ko saurin yin fushi kan haifar da rashin kauna da tawali’u a cikin rayuwar mutane.  A yau za ka ga mutane na saurin yin fushi har sukan furta kalaman da ba su dace ba don wani abu dan kalilan da bai gamshe su ba, idan ba a yi hankali ba sai ka ga fada ya barke har ta kai ga kisa, rashin tawali’u ke haifar da irin wannan.

Haka rashin tawali’u kan haifar da son kai, (Yakubu 3:16-18.) “A duk inda kishi da son kai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke. Amma hikimar nan ta sama da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mai kaifi daya, sahihiya kuma. Daga irin salama wadda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.” Misali, za ka ga cewa mutane da dama ba su da sha’awar bin tafarkin Ubangiji Allah, kowa na hanzarin mallakar kayan duniya ido a rufe kowa na bukatar yin kudi ta kowane hali, lallai yin haka na kai mutum ga jarabobi da hallaka amma idan muka dauki kaunar Ubangiji cikin zukatanmu muka kuma bi gurbin da Yesu Almasihu ya nuna mana za mu zama mutane ne cike da halin tawali’u, salihai kuma. Bari mu ga abin da Littafi Mai tsarki ke fadi a cikin 1 Timothy 6:9-11: “Masu dokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fada a cikin tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin wadanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Ai, son kudi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kudi kuwa wadansu mutane, har sun baude wa ban- gaskiya, sun jawo wa kansu bakin ciki iri-iri masu sukar rai. Amma, ya kai, bawan Allah! Ka guje wa wadannan abubuwa, ka dimanci aikin adalci da bin Allah da ban-gaskiya da kauna da jimiri da kuma tawali’u.” Sai mu yi lura kada mu fada wannan tarko na Ibilis, mu dimanci halin nuna kauna da tawali’u a cikin kowane hali ko cikin maganarmu, bari kalaman da muke furtawa su nuna matukar tawali’u kamar yadda Littafi Mai tsarki ke fadi: Karin Magana 15:1: “Amsa magana da tattausan harshe kan kwantar da hassala, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.”

Yakubu 1:19-21 “Ya ’yan uwana ƙaunatattu! Ku san wannan, wato, kowa ya yi hanzarin kasa kunne da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi, don fushin mutum ba ya aikata adalci. Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri-iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na’am da ita a cikin halin tawali’u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.”

Titus 3:2: “Kada su ci naman kowa, kada su yi husuma, sai dai su zama salihai, suna yi wa dukkan mutane matuƙar tawali’u.”

Sai lura, ko da wani ne ya fuskance mu da kakkausan harshe mu zama masa abin koyi da kuma hanyar tuba ta wurin nuna masa kaunar Allah da ke cikin zukatarmu.Mu nuna masa hasken Yesu Almasihu ta wurin jinkirin yin fushi da kuma halin tawali’u domin yin haka zai kashe kaifin fushinsa ya kuma kubutar da shi daga wannan hali. Kolosiyawa 4:5-6 “Ku tafiyar da al’amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matukar amfani da lokaci. A kullum maganarku ta zama mai kayatarwa, mai dadin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.”

Idan har kana kiran kanka mai bin Yesu Almasihu (Kirista) lallai ne ka guje wa halin son kai da girman kai da husuma ka nuna halin tawali’u domin ka ceto rayuka daga irin wannan hali. 2 Timoti 2:24-26 “Bawan Ubangiji kuwa lallai ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa, gwanin koyarwa, mai hakuri, mai sa abokan hamayyarsa a kan hanya da tawali’u, ko Allah zai sa su tuba, su kai ga sanin gaskiya, su kuɓuce wa tarkon Iblis, su bi nufin Allah, bayan da Iblis ya tsare su.”

Kolosiyawa 3:12-15: “Saboda haka, sai ku dauki halin tausayi da kirki da tawali’u da salihanci da hakuri, idan ku zababbu ne na Allah, tsarkaka, kaunatattu, kuna jure wa juna, in kuma wani  yana da kara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji Ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe. Fiye da wadannan duka, ku dau halin kauna, wadda dukan kammala take kulluwa a cikinta. Salamar Almasihu kuma ta mallaki zuciyarku, domin lallai ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.”

Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ikon nuna kaunarSa ga dukan duniya, amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin