✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tawali’un Fafaroma da mutakabbirancin shugabannin Afirka

A ranar Alhamis din makon jiya ne Fafaroma Francis na 16 ya ba duniya mamaki lokacin da ya durkusa har kasa kamar mai sujuda ya sumbaci…

A ranar Alhamis din makon jiya ne Fafaroma Francis na 16 ya ba duniya mamaki lokacin da ya durkusa har kasa kamar mai sujuda ya sumbaci kafafuwan shugabannin Sudan ta Kudu a wani mataki na nuna tawali’u da kankan da kai yana rokon su kokarta su tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasarsu don ceto ta daga yakin rashin kan gado da suka jefa ta ciki shekara da shekaru.

Wannan mataki na Fafaroma Francis ya zo ne bayan wani taron tattaunawa da fadakarwa na wuni biyu da fadar Batican ta shirya wa shugabannin Afirka.

Fafaroma Francis ya roki Shugaban Sudan da shugaban ’yan adawa su ci gaba da aiki da yarjejeniyar zaman lafiya duk da zaman dar-dar da ake fuskanta a kasar. Duk wanda ke halarce lokacin da Fafaroma Francis mai shekara 82 wanda ke fama da ciwon kafa  da kyar ya iya durkusawa ya sumbaci kafafuwan wadannan shugabanni da sauran mutanen da suke dakin taron, ko wanda ya ga faifan bidiyo ko hoton da yake yin haka, zai kadu kan wannan saukin kai na Shugaban Addinin Kirista na Duniya a yau.

Da kyar ma’aikatansa suka taitaye shi ya durkusa don yin wanna nsumbata. Mutane da dama suna ganin wannan ita ce babbar girmamawar da Fafaroman ya yi ga wadansu shugabannin siyasa na wata kasa a duniya.

To amma abin da ya fi jan hankalina shi ne me ya jawo har Fafaroma ya dauki wannan mataki da ya ba duniya mamaki? Amsar daya ce, ita ce tsabagen son mulki na dan Afirka da ya gwammace ya hallaka jama’ar da zai yi wa mulki da a ce wani ne daban yake mulkin ba shi ba.

Lamarin ba ya shafi mutanen Sudan ta Kudu su kadai ba ne, akasarin shugabanninmu na Afirka da ’yan siyasarmu ba su dauki mulki ko shugabanci a matsayin amana wadda ko ba su yi imanin za a tambaye su a Lahira ba, mutuncinsu na iya zubewa a nan duniya in suka yi ba daidai ba.

Rashin daukar mulki da shugabanci a matsayin amana ce ke haifar da mutakabbiranci da girman kai da rashin imanin da suke kaiwa ga mayar da irin wadannan shugabanni na Afirka manyan barayin da duniya take shakkarsu.

Sudan ta Kudu tana samun ’yancin kai daga kasar Sudan ta tsunduma cikin Yakin Basasa, kuma ba komai ya kawo wannan yaki ba face kowa yana so ya isa kan madafun iko domin ya yi sata ta fitar hankali, satar da zai debi dukiyar da ba za ta amfani wanda ya tara ta ba.

Irin wannan tara kazamar dukiya ce ta sa tsohuwar Shugabar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Tu’annati (EFCC), Hajiya Farida Waziri ta ce ya kamata duk wanda zai nemi mulki a Najeriya a rika yi masa gwajin kwakwalwa saboda ta lura kazamar dukiyar da suke sata su tara ba ta da bambanci da tarkacen da mahaukata ke tarawa.

Tabbas wannan dabi’a ta satar duniyar talakawa ana tarawa fiye da bukatun mutum da zuriyarsa na daga cikin dalilan da ke sa akasarin masu neman mulki a Afirka suke haukacewa sai sun yi mulki ko da hakan zai haifar da asarar dimbin rayuka.

Mu dauki misali da Najeriya, rahotannin da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa suka rika bayarwa kan yadda wadansu kalilan din mutane da suka kai kan madafun iko suka sace dukiyar da za su dawo da ita asusun gwamnati za ta kai kasafin kudin kasar nan na akalla shekara biyar zuwa 10.

Wannan sata wadda ta zama ado a yanzu ta kai matsayin da abin da kawai ake so da kai, ka sato ka zo ka sammar da kadan ga jama’a, ko ka yi wani dan aiki da za a gani a fadi, shi ke nan ko nawa ka sata ko da satar za ta jawo asarar dimbin rayuka da rugujewar hanyoyin ci gaban kasa ba komai!

Ba na mancewa lokacin da ake fama da rikicin yankin Tekun Fasha a tsakanin Shugaba Saddam Hussein na Irak da shugabannin Amurka a wajejen 1990, muna dalibai sai muka rika kumfar baki muna la’antar abin da Amurka ke yi. Sai wani malaminmu Malam Dan’azumi Musa Tafawa Balewa ya shigo aji ya ce, “Ku ga yaki nan yana cinku a cikin gida amma kuna bata lokaci kuna ta surutai a kan yakin da ake yi a wata kasa.” Ya ci gaba da cewa: “Abin da ake yi wa Saddam ana rusa masa gine-gine da gadoji da sauran kayayyaki ne, wadanda a cikin shekara biyar zai iya gyarawa. Amma ku ana rusa zukatanku ne ana yakar tunaninku ana raba ku da imani, ana sanya muku son tara abin duniya ta halal da haram, ana raba ku da tarbiyya, wadanda sai kun dauki shekara 40 ko fiye ba ku iya gyarawa ba.”

Ya bayyana yadda ake kokarin mayar da cin hanci da rashawa da almundahana da dukiyar gwamnati a wancan lokaci da kamar ado, inda ya ce wannan aba kuwa muguwar cuta ce da za a dauki dogon lokaci ba a iya magance ta ba.

Ga shi kuwa muna ganin abin da ke faruwa a yau ke nan, duk mukamin da ka samu ba damuwar mutane yaya ka rike wannan amana ba, a’a me ka sato ka yi mana. Mun kai matsayin da idan ka gaza satar kudin gwamnati, sai a dauka ka sata ne don amfanin kanka da iyalinka. Wato yanzu a kasar babu wanda ba barawo ba!

Shi ya sa daga dawowar mulkin farar hula a 1999 zuwa yau, kashi 10 cikin 100 na dukiyar kasar nan ake zargin ta fada aljihun shugabannin da suka yi mulki  wato shugabannin kasa da ministoci da gwamnoni da kwamishinoni da ciyamomi da kansilol wadanda babban abin da suke kokarin gani shi ne su samu dukiyar da za su dada neman mukami na gaba su zama wadansu mutakabbirai masu juya jama’a yadda suka ga dama. Su kuma jama’ar da ake yi wa wannan muguwar sata saboda rashin sanin ciwon kai da rashin tunanin makomar ’ya’ya da jikokinsu sun aminta da wannan salo, ba damuwarsu halacci ko rashin halaccin dukiyar ba, a’a damuwarsu idan ka sata “ka sam mana!” Shi ya sa da za ka leka gidajen shugabanni tun daga kansila da masu iya magana ke cewa “Kansila masomin cuta,” zuwa shugabannin kananan hukumomi da ’yan majalisun jihohi da ta wakilai da sanatoci da ministoci da gwamnoni da duk wani mukarrabi mai tallafa wa wadancan shugabanni babu abin da akasarin ’yan Najeriya ke yi face sammakon zuwa don su ma a ba su ‘nasu rabon’ na dukiyar da shugabannin suka karkatar zuwa bukatun kansu.

Wannan ya sa akasarin dan Afirka ba yana yin mulki don ya bauta wa kasa ko yi wa jama’arsa hidima, a’a yana yi ne don ya tara wa kansa dukiyar da za ta sa kowa ya zo ya rusuna masa ya zama tamkar wani ubangijin mutane, dukiyar da zai ci gaba da amfani da ita wajen karfafa daularsa ta kama-karya da danne sauran jama’a!

Kuma wannan shi ne silar duk wata zubar da jini da kashe-kashe da suke faruwa a kasashen Afirka inda da gangan ake haddasa yake-yaken basasa ko rikice-rikicen kabilanci da na addini da sauran miyagun ayyuka.

A tunanina lokacin da Fafaroma Francis ya durkusa kasa yana sumbatar kafafun wadancan shugabanni zan ga dukkansu su fashe da kuka domin yin nadamar barnar da suka tafka wadda ta jawo zubar da jinin al’ummarsu. Amma abin takaici saboda mutakabbiranci da girman kai da rashin sanin ya kamata sai kawai suka yi kasake suna kallon Fafaroman yana sumbatar kafafunsu. Da sun san ya kamata a lokacin da Fafaroma yake kokarin isa kasa don sumbatar kafafunsu sai su tafi kasan tare da shi don nuna sun yi nadamar abin da suka aikata, amma  sai suka tsaya kawai suna kallonsa babu wanda ya yi kuka babu wanda ya zubar da hawaye!

Shin bai dace a ce kafin Fafaroma ya dago daga sumbatar kafar mutum na farko sauran shugabannin su shelanta ajiye dukan bukatunsu kashin kansu ba? Shin bai kamata a ce nan take sun shelanta yafe wa juna da neman gafarar al’ummar kasarsu ba? Shin bai kamata take su ce sun hakura da duk wani abu da suke nema ba, wani ya hakura ya bar wa wani mulkin don amfanin al’ummarsu?

Gaskiya ya kamata shugabannin Afirka su fahimci mulki amana ce  kuma su daina jefa jama’arsu cikin tashe-tashen hankula ana zubar da jini don kawai suna son su yi mulki.