Search
Subscribe
Taya murna ga sababbin kantomomin Bauchi

Taya murna ga sababbin kantomomin Bauchi

Assalamu alaikum Edita. Ka ba ni dama in taya daukacin sababbin kantomomin rikon kwarya na kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi, ciki har da na Karamar Hukumarmu ta Dambam, Mai girma Ahmad Garba Shattiman Dambam  murna, wadanda Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir Kauran Bauchi, ya nada kwanakin baya.Allah Ya taya su riko Amin. Sannan a hannu guda muna kira gare su cewa su yi kokarin kwatanta gaskiya da adalci tare da kawo ci gaba mai ma’ana kamar samar da famfunan ruwan sha, inganta wutar lantarki, daukar ma’aikata don rage zaman banza da kuma zagayawa cikin gari da kauyuka don gane wa idonsu halin da talakawa ke ciki don kai musu dauki. Wannan kira bai tsaya ga kantomomi ba, har da ’yan majalisar jiha da na tarayya da ke jiharmu ta Bauchi. Allah Ya albarkaci kasarmu Najeriya, amin summa amin.

Daga Hussaini Abba Dambam, Karamar Hukumar Dambam Jihar Bauchi. 08020814173

Godiya ga Allah kan na’imomi da Ya yi wa kasata Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi godiya ga Allah da irin ni’imomin da Ya yi mini. Allah ka ba kasarmu zaman lafiya, Ka shiryar da shugabanimu, Ka taimaki Musulunci da Musulmi, Ka kaskatar da shirika da mushirikai, amin.

Daga Abdullahi Angon Nabeela Giro, Kebbi, 08032624432

Buhari ka kori gurbatattun ma’aikata

Muna kira ga Shugaba Buhari ya kori wadansu gurbatattun mutane a cikin gwamnatinsa wadanda suke hana ruwa gudu. Duk da cewa Malam Garba Shehu ya musanta haka amma ba mu yarda da maganarsa ba.

Daga 08134983491.

Fatan alheri ga Aminiya

Assalam AMINIYA. Ina yi muku fatan alheri, Allah Ya kara basira.

Daga Mai muku fatan alheri, Jazulin Durumin Maigarke Zaria City, 08035134636

A bai wa yaran shago hakkinsu

Salam. An ce akwai dokar kayyade farashin kaya. To me ya sa babu dokar da ke kula da yadda masu gida ke danne hakkin yaransu, masu sayar musu da kaya. Sai yaro ya shekara yana tara musu kudi amma wai shi yaro ba ya da komai ina adalci a nan.

Daga 08139293913.

Sakon godiya ga Gwamnan Katsina

Salam don Allah jaridar Aminiya mai albarka, ku ba ni fili domin in yi godiya ga Gwamnan Jihar Katsina kan ayyukan da yake yi a jiharmu ta Katsina. Muna godiya da irin ci gaban da muke gani a jiharmu ta Katsina, muna godiya da fatan alheri ga gwamnatin Baba Masari Allah Ya yi jagora, amin.

Daga Sagir Saminu Kaita, 08133522467.

Bukatar saka lokutan salloli

Salam Edita. Ina so na ba da shawara a cikin shafukan wannan jarida tamu mai albarka a rika saka lokutan salloli na manyan biranan kasar nan, kamar yadda takwararta ta Turanci ke yi. Saboda mafi yawancinmu masu karanta ta duk mako Musulmi mun fi yawa. Ina fatan za a kalli wannan shawara tawa.

Daga Jamilu M. Adam 07011201971.

Kira ga Shugaban Kasa

Assalam Edita. Da fatan kana lafiya kai da daukacin ma’aikatan wannan jarida da masoyan wannan jarida mai albarka, Allah Ya sa haka amin. Don Allah ina so in yi kira ga Shugaban Kasa a kan bin wasu shawarwari kafin ya yi wani abu wanda shi a tunaninsa zai iya kawo ci gaban kasa.

Daga Bara’u Liman, 08062862191.

Jinjina ga Gwamnan Jihar Adamawa 

Assalamu alaikum Edita. Don Allah ku ba ni dama in jinjina wa Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri da kuma mamba na Mazabar Jimeta a Adamawa kan yadda suka dauki matakin dakile ’yan kwace (’Yan Shila) a jihar. Abin ya yi daidai da sauran takwarorinsa za su dauka da an samu sauki a kasar nan.

Daga Sadik J.M.T. Suleja, Jihar Neja. 07012115752.

Kira ga Sanata Wamakko

Assalam Aminiya. Ku ba ni dama in yi kira ga Sanatanmu mai wakiltar Sakkwato ta Tsakiya Dokta Aliyu Magatakarda Wamakko da ya ji tsoron Allah Ya daina jefa mutane cikin hadari ta yadda yake bin titi yana watsi da kudi, bayin Allah suna faduwa suna samun raunuka. Wani lokaci har da rai ake rasawa. Allah Ya sa sakon ya kai inda ake nufi.

Daga Ahmad Muhammad Wamakko, 07068039968.

Kira ga Shugaba Buhari

Assalam Edita. Ina kira ga Shugaba Buhari ya kawo Hamid Ali Hukumar EFCC, saboda namijin kokarin da ya yi wa kasar nan. Ya tara mata kudi masu yawa a bangaren Kwastam shi zai yi aiki ba sani ba sabo a Hukumar EFCC.

Daga Sufiyanu Aliyu Addan Yabo Sakkwato, 08083446684.

Kira ga Gwamnatin Kano

Salam Editan Aminiya, don Allah ka mika min kirana ga gwamnati Jihar Kano kan ta yi wa Allah ta kalli al’ummar Kogo a Karamar Hukumar Kiru ta taimaka a  gyara masallacinmu. Allah Ya sa a dace.

Daga Mai A.C. Kogo. Kofar Kudu 09030466517.

Kira ga Gwamnan Borno

Ma’aikatar Aminiya ina yi muku fatan alheri da fatan kuna lafiya. Don girman Allah ina so ku isar min da sakona ga Mai girma Gwamnanmu na Jihar Borno, Babagana Umara. Gwamna dama kai muke so ka zama Gwamnanmu a Borno kuma Allah da ikonSa Ya ba ka nasara ka taimaka wa kauyukanmu.

Daga 09069158247.

Shirin Ruga: Kira ga Shugaba Buhari

Salam Edita, ina son ka ba ni fili a wannan jarida mai albarka, wato AMINIYA in yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya fita batun masu sukar shirin Ruga, a ci gaba da shirin a jihohin da suka amince. Kuma ina gayar da dukkan ma’akaitan wannan jarida mai farin jini.

Daga Nasiru Sani Gusau, 07064340675.

Gaisuwa ga ma’aikatan Aminiya

Assalmu alaikum ma’aikatan jaridar Aminiya mai albarka. Don Allah ina so ku mika min sakon gaisuwata ga Edita, Allah Ya sa ka masa da alheri.

Daga Sanusi Musa Police, Gusau Jihar Zamfara 08139005478.

Kira ga Baba Buhari

Assalam Edita. Ina yi muku fatan alheri. Don Allah, ka ba ni dama in yi kira ga Shugaban Kasa Baba Buhari ya bai wa gwamnoni dama a kan maganar gyaran filayen jiragen sama, hakan zai gina Arewa saboda, ba aikin yi ba tsaro, ba ilimi. Kuma a bai wa shugabannin kananan hukumomin Najeriya ’yanci.

Daga Ali Muhammad Mustapha Kano 09032518719.

Gyaran hanya: Kira ga Gwamnan Jigawa

Muna kira ga Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya taimaka ya sa baki game da aikin hanyar Auyo zuwa Zubarau. Hanya ce da daruruwan jama’a mazauna karkara ke bi don zuwa wurin neman na sawa a baka. Hanya ce da ba ta wuce kilomita biyu ba, kuma wannan hanya an sha yi mana alkawarinta a zamanin Saminu Turaki da Sule Lamido, alkawarin da ba a cika ba har gwamnatocin suka shude. A shekarar 2015, an yi alkawari amma ba a cika ba, an fara yin hanyar gabanin zabe, amma yanzu shiru kake ji, hanyar tana da hadari musamman a lokacin damina.

Daga Ahmed Garba Zubarau G/Gabar Auyo, 09070608002.

Najeriya na bukatar ministoci masu kishi

Assalamu alaikum. Kira ga Shugaban Kasa a kan nada ministoci. Da yake a baya an ga irin rawar da suka taka yanzu ya rage ga Shugaban Kasa ya nada mutane masu kishin kasa, in aka duba za a ga al’ummar Najeriya suna fama da talauci da rashin aikin yi.

Daga Tjjani Ibrahim Kano Fagge 08128489186.

Neman afuwa gaGwamnatin Ganduje

Kira ga gwamnatin Ganduje a kan hukuncin da ta dauka kan ’yan matan da suka yi rashin da’a ga gwamnatinsa. Muna neman afuwa gare su da a yafe musu bisa adalcin da gwamnatin ke da shi.

Daga Yusuf Kano (Abban Khadija)

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin