✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tayar da kayar baya ba halin mutanen Zamfara ba ce – Tsohon Gwamna

Tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato da ta kunshi jihohin Sakkwato da Zamfara, Alhaji Yahaya Abdulkarim ya ce abubuwan da suke faruwa yanzu a Jihar Zamfara…

Tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato da ta kunshi jihohin Sakkwato da Zamfara, Alhaji Yahaya Abdulkarim ya ce abubuwan da suke faruwa yanzu a Jihar Zamfara na tayar da kayar baya ba halin mutanen jihar ba ne.

Tsohon Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Talata da ta gabata a wajen babban taron Daular Zamfara da Jami’ar Usman Dan Fodiyo ta shirya a karkashin kular Tsangayar Fasaha da IlImin Addinin Musulunci ta jami’ar.

Alhaji Abdulkarim wanda shi ne shugaban bikin ya  shaida wa mutane cewa ilimin tarihi abu ne da ya zama wajibi. “Matasanmu na da bukatar sanin tarihin gudunmawar da mazan jiya suka bayar wajen samun zaman lafiya da hadin kan Najeriya. Yadda suka sadaukar da jin dadinsu da jininsu kan hadin kan mutane,” inji shi.

Ya kara da cewa, “In dai har ba mu iya bunkasa ci gaban da suka kawo ba, kada mu tarwatsa shi.” Sannan ya yi kira ga masu son kawo cikas a kasar nan su adana kalamansu domin hadin kan kasa ba abin wasa ba ne.

A jawabin Sarkin Zamfaran Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Alhaji Attahiru Ahmad ya yi kira ga malamai a kasar nan musamman wadanda ke fannin iilmin nazarin tarihi su fito da shirye-shiryen da za su kara karfafa wa mutane so da bincike ilimin tarihi.

Farfesa Kabiru Suleiman Chafe na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya gabatar da makala kan yanayin al’umma da bunkasar siyasar yankin Zamfara tun daga karni na 16.

Shugaban Jami’ar Usman Dan Fodiyo Farfesa Lawal Bilbis ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara su bayar da gudunmawa ga jami’ar don ta wallafa wannnan bincike domin amfanar jama’a gaba daya.

Ya ce yana da tabbacin wannan zai taimaki al’umma da tattalin arzikin wadanda suka yi tunanin yin wannan babban taro na duniya.