✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Thierry Henry na daga cikin masu neman horar da Monaco

Tsohon dan kwallon Arsenal, Theirry Henry na daga cikin mutanen da suke zawarcin horar da kulob din Monaco na Faransa. Rahoton da jaridar The Mirror…

Tsohon dan kwallon Arsenal, Theirry Henry na daga cikin mutanen da suke zawarcin horar da kulob din Monaco na Faransa.

Rahoton da jaridar The Mirror ta Ingila ta ruwaito ya ce kulob din yana kokarin korar kocinsa na yanzu ne Leonardo Jardim saboda rashin kokari a kakar wasa ta bana.

Ya zuwa yanzu kulob din Monaco yana da maki 6 ne kacal daga cikin wasanni 9, al’amarin da ta sa kulob din yake kasan tebur a gasar Ligue 1 ta Faransa.

Theirry Henry ya taba taimakawa kulob din Monaco wajen lashe gasar rukunin Faransa (Ligue 1) a 1999 a lokacin da yake buga musu kwallo kafin ya canza sheka zuwa kulob din Arsenal na Ingila.

Koci Leonardo Jardim, tsohon kocin Sporting Lisbon na Fotugal, ya fara horar da Monaco ne a shekarar 2014 inda ya samu nasarar samar da ’yan kwallo irin su Kylian Mbappe na kulob din PSG na Faransa da Thomas Lemar na Atletico Madrid da kuma ’yan kwallon Manchester City na Ingila Bernando Silba da Benjamin Mendy.