Aminiya

Tibi da Jukun: An kashe matasan Jukun 5 a Taraba

Matasan kabilar Jukun a jihar Taraba sun sanar da cewa, harin da aka kaiwa kabilar ya yi sanadiyyar kone wasu matasa kurmus inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar matasa 5 a Karamar Hukumar Takum da ke jihar.

Matasan da suka aikata hakan sun yi ta rali akan babura suna murna dauke da kawunan gawarwakin da suka kashe.

ADVERTISEMENT

Mazauna garin Takum sun yi Allah Wadai da wannan mummunan harin da matasan suka kaiwa kabilar Jukun a yankin.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar David Misal, ya tabbatar da aukuwar kai harin ya kuma tabbatar da kisan mutum biyar.

ADVERTISEMENT