✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tibi da Jukun: Yadda rikicin kabilanci ya addabi Kudancin Taraba

Yau shekara daya da rabi ke nan da Janar T.Y. Danjuma (mai ritaya) ya bai wa kananan kabilun kasar nan umarnin cewa su dauki makamai…

Yau shekara daya da rabi ke nan da Janar T.Y. Danjuma (mai ritaya) ya bai wa kananan kabilun kasar nan umarnin cewa su dauki makamai su kare kansu daga kisan kare-dange da yake zargin Fulani suna yi musu.

Janar Danjuma bai tsaya a nan ba, ya kuma ya yi zargin cewa sojojin kasar nan suna hada baki da ’yan ta’adda suna kashe kananan kabilu, wadanda akasarinsu masu bin addinin Kirista ne.

Shekara daya da wannan zargi da Janar Danjuma ya yi sai ga shi mummunan fadan kabilanci ya barke a tsakanin kabilun Tibi da na Jukun a Karamar Hukumar Wukari da ke Jihar Taraba.

Shi dai Janar Danjuma dan kabilar Jukun ne kuma wannan rigima ta kabilanci a tsakanin kabilun Tibi da Jukun an soma ta ce a wani gari da ake kira Kente da ke Karamar Hukumar Wukari. Garin na Kente yana kusa ne da kan iyakar jihohin Taraba da Binuwai.

An fara wannan rigimar ce a ranar 1 ga Afrilun bana  kuma har yanzu ba a shawo kan wannan fada ba.

Sojojin sa-kai dauke da manyan bindigogi daga kabilun Tibi da Jukun suna ci gaba da kai wa juna hari ba-dare-ba-rana, suna hallaka jama’arsu, wadanda zuwa yanzu ake zargin an kashe daruruwan mutane tare da kona garuruwa da kauyuka sama da 50.

Wurin da wannan fada ya shafa da farko shi ne Karamar Hukumar Wukari, inda kusan duk kauyukan Tibi da na Jukun suka fuskancin hare-hare daban-daban da suka tilasta wa kabilun biyu gudun hijira zuwa garin Wukari. Su kuma ’yan kabilar Tibi suka gudu zuwa Jihar Binuwai.

Daga nan ne sai rigimar ta fada Karamar Hukumar Takum, mahaifar Janar TY Danjuma, inda nan ma aka kai wa kusan daukacin garuruwan Tibi hari, aka kashe mutane masu yawan gaske tare da kone gidaje sama da 300.

A Karamar Hukumar Donga, Gara na Donga, wato Sarkin Donga, Dokta Danjuma Stephen Banyonga, wanda ya rasu a farkon wannan wata ya yi iyakar kokarinsa wajen hana rigimar shiga masarautarsa amma a ranar da ya rasu, wato 6 ga Agustan nan, sai ga shi fada ya tashi a tsakanin ’ya’yan kabilun Jukun da na Chamba da Tibi a Karamar Hukumar Donga.

Kamar yadda wakilinmu ya binciko, ya gano cewa a halin da ake ciki kananan hukumomin Wukari da Takum da Donga na fuskantar wannan matsala ta rashin zaman lafiya. ’Ya’yan kabilar Jukun suna zargin cewa ’yan kabilar Tibi ne ke haifar da rashin zaman lafiya ta hanyar amfani da sojojinsu na sa-kai suna kai wa garuruwan Jukunawa hari suna kashe al’ummarsu.

Shugaban Karamar Hukumar Wukari, Mista Adi Daniel ya shaida wa wakilinmu cewa ’ya’yan kabilar Tibi sun hallaka Jukunawa masu yawan gaske a garuruwan Jukunawa tare da kone musu gidaje. Ya kara da cewa mahara ’yan kabilar Tibi sun hana Jukunawa zuwa kasuwa da gona, domin duk wanda ya fita bayan gari Tibi suna kashe shi. A bangaren ’ya’yan kabilar Tibi suna zargin Janar T.Y. Danjuma da Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku da cewa su ne suka horar da mayakan sa-kai na ’ya’yan kabilar Jukun, suke hallaka ’ya’yan kabilar Tibi da ke Jihar Taraba.

Janar T.Y. Danjuma da Gwamna Darius Ishaku, dukkansu ’yan asalin garin Takum ne kuma ’yan kabilar Jukun, inda a yanzu haka hanyar zuwa Takum daga Wukari ba ta biyuwa saboda ayyukan sojojin sa-kai na kabilun biyu.

’Ya’yan kabilar Tibi a ’yan kwanakin nan sun gudanar da wani taron manema labarai, inda suka zargi Janar Danjuma da Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku cewa su ne suke horar da mayakan sa-kai na Jukun, suna ba su kudi da makamai, suna gudanar da ayyukan ta’addanci, musamnan wajen yi wa ’yan kabilar Tibi kisan kare-dangi.

Amma Babban Mai bai wa Gwamnan Jihar Taraba Shawara ta fuskar Watsa Labarai, Mista Bala Dan Abu ya yi watsi da wannan zargi, inda ya ce kazafi ne ake yi wa mai gidansa Darius da Janar Danjuma.

Bala Dan Abu ya kara kara da cewa ba irin matakai da hanyoyin da Gwamnan Jihar Taraba bai dauka ba, wajen ganin an kawo karshen wannan fada amma abin ya ci tura. Ya ce Gwamnan da takwaransa na Jihar Binuwai, Gwamna Samuel Ortom sun dauki matakai masu yawan gaske tare da hada tarurruka a tsakanin masu ruwa-da-tsaki na kabilan Tibi da nufin kawo karshen wannan matsala amma har yanzu hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Ana cikin haka ne sai ga shi matasan yankin Kudancin Taraba, wadanda mafi yawansu Jukunawa ne suka gudanar da taron maneman labarai, inda suka bai wa ’yan kabilar Tibi wa’adin kwana bakwai su bude hanyoyin mota a yankunan kananan hukumomin da wannan fada ke aukuwa ko kuma su fuskanci fushinsu.

Da yake jawabi a madadin matasan Kudancin Taraba, Mista Dodo Dan’azumi ya yi zargin cewa sojojin sa-kai na kabilar Tibi sun hana jama’a walwala a hanyoyi mota a yankunan, inda suke farautar ’ya’yan kabilar Jukun suna hallaka su tare da yi musu fashi.

Su ma a martaninsu ’ya’yan kabilar Tibi da Shugaban Al’ummar Tibi a Jihar Taraba, Mista Goodman Dahida ya yi magana a madadinsu, watsi ya yi da wannan zargi, inda ya ce su al’ummar Tibi ya kamata su yi wannan korafi domin su ne sojojin sa- kai na kabilar Jukun suke farauta suna kashewa.

Dahida ya cewa su ’ya’yan kabilar Tibi ’yan Jihar Taraba ne amma Jukunawa sun ce su baki ne, wanda shi ya sa suke hallaka su tare da kone garuruwansu da kauyukansu. Ya ce Jukunawa ne ba sa son zaman lafiya, domin a baya-bayan nan Gwamnan Jihar ya tara su a gidan gwamnati a garin Jalingo don yi masu sulhu amma a daidai wannan lokacin da Gwamna ke taro da su, a can kuma Jukunawa suna ta kashewa da kone gidajen Tibi a Karamar Hukumar Takum mahaifar Gwamna Darius.

Binciken da wakilinmu ya gudanar, ya gano cewa wannan rigimar tana da tsohon tarihi a tsakanin kabilun Tibi da Jukun, inda aka faro ta tun 1950. Kuma daga 1950 zuwa yanzu, an samu aukuwar irin wannan fada fiye da sau 15, sai dai wanda ake yi yanzu ya fi muni ta fuskar asarar rayuka da barnata dukiya tare da dadewa ba a shawo kansa ba.

Yankin Kudancin Taraba ya sha fama da rigingimun kabilanci da na addini. Cikin wadannan rigingimu har da mummunan fadan kabilanci a tsakanin ’yan kabilun Jukun da Kuteb da ya faru a 1999, sai kuma fadace-fadace a tsakainin ’yan kabilun Tibi da Jukun da kuma fadan addini a tsakanin Musulmi a garuwan Wukari da Ibbi, su ma tsakanin Jukunawa Kiristoci da Musulmi Jukunawa da Hausawa da sauran kabilu Musulmi, a shekarun 2000 da 2013.

A cewar wani mazaunin yankin mai suna Alhaji Musa Bello, ya ce irin wadannan rigingimu da suke aukuwa a yankunan Kudancin Taraba suna haifar da asarar dubban rayuka da salwantar miliyoyin Naira. Ya kara da cewa babbar matsalar ita ce, har zuwa maganar da ake yi ba taba kama ko daya daga cikin masu tayar da rigingimu a yankin ba balle a hukunta shi, wanda hakan ne ya sa da wuya a iya kawo karshen wannan matsala a yankin.