✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tom Cruise na shirin kara aure

Jarumin nan da ya dade yana nuna bajinta a fina-finan Amurka, Tom Cruise ya tada kabarar kara aure. Alamar haka ta tabbata ne a makon…

Jarumin nan da ya dade yana nuna bajinta a fina-finan Amurka, Tom Cruise ya tada kabarar kara aure. Alamar haka ta tabbata ne a makon da ya gabata, inda aka gan shi yana yawo da wata mata a kan babur, wacce ba a tabbatar da ko ita wace ce ba.
dan wasan, wanda a bana ya cika shekara 50 da haihuwa, ya kwana biyu yana rayuwar gwagwarci, tun bayan rabuwarsa da matarsa, Katie Holmes. Kamar yadda jaridar ‘Huffington Post’ ta ruwaito, an dauki hoton jarumi Tom ne tare da sabuwar masoyiyar tasa a maraicen Alhamis ta makon jiya, inda take zaune a bayan babur tana boye fuskarta.
Wannan mataki da dan wasan ya dauka, ya kara tabbatar da cewa shi da tsohuwar matarsa tuni kowa ya kama sha’anin gabansa, domin kuwa a yayin da ita Katie aka ga tana soyayya da dan fim Luke Kirby, shi kuwa ya samu sabuwar masoyiyar da ake ganin cewa nan ba da dadewa ba zai angwance.