✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Toshewar mafitsara ga yara maza

Wace matsala ce ga yara maza kan sa toshewar fitsari, su zo yin fitsari su yi ta kugi saboda zafi mara ta cika? Ko akwai…

Wace matsala ce ga yara maza kan sa toshewar fitsari, su zo yin fitsari su yi ta kugi saboda zafi mara ta cika? Ko akwai wani taimakon gaggawa da za a iya bai wa wadannan yara kafin a kai asibiti musamman idan suna nesa da asibiti?

 

Amsa: Eh, akwai abin da yakan iya toshe hanyar fitsari a yara maza kamar yadda hanyar za ta iya toshewa a manya maza. Yawanci a yara maza wani tsiro ne da mukan kira posterior urethral balbe kan toshe wa yaran hanyar fitsari, sabanin a manya inda ciwon sanyi da kumburin prostate ke toshe musu hanyar fitsarin. Shi wannan tsiro wani irin tsiro ne da kan fito a wasu mafitsarar yara maza da suka yi rashin sa’a tun a ciki.

Yara maza kadai matsalar kan shafa ba ta shafar mata. Sai dai ita matsalar toshewar hanyar fitsari ba kamar irin waccan tambayar da ka yi ba ta farfadiya wadda kowa zai iya yin taimakon gaggawa kafin a kai ga asibiti, ita wannan matsala taimakon da take bukata na gaggawa dole ne sai ma’aikacin lafiya ne zai yi, ba kowa ne zai yi ba. Taimakon kuwa shi ne na zura robar fitsari a mafitsara domin fitsarin ya gangaro yaron ya dan samu sauki kafin a garzaya asibiti. Idan aka je asibiti za a rubuta gwaje-gwaje da hotuna domin su nuna ko tsiron ne a mafitsarar ko akasin haka. Idan aka ga tabbas irin wannan tsiron ne sai an yi tiyata an gyara wurin.

 

Ko da gaske ne maganin kashe zogi na feldene yana iya lalata wa mata mahaifa?

Daga Asiyatu Ansar

 

Amsa: A’a ba kanshin gaskiya a wannan batu. Mata da dama masu samun ciwon mara na al’ada na yawan shan wannan magani amma ba ya lalata musu mahaifa. Abin da kawai aka danganta maganin da shi shi ne jawo ciwon olsa idan aka nace masa.

 

Ni kuma al’adata ce take yi mini wasa, sai ta tafi ta dawo, ta tafi ta dawo. Sai ta yi wata hudu ba ta dawo ba a wasu lokutan. To ko wannan matsala ce, kuma za ta iya hana ni daukar juna biyu idan na yi aure?

Daga Habiba M.

 

Amsa: Eh, tabbas wannan a likitance matsala ce da idan ba ki je an duba dalili ba an yi magani za ta iya jawo miki matsalar rashin iya daukar juna biyu idan kika yi aure.