✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Traore, Vertonghen da Diaby na shirin sauya sheka; Chelsea na neman dan wasan Barca

Yayinda ake kokarin dawowa wasanni a fadin nahiyar Turai, haka ma kasuwar cinikin ‘yan wasa ta fara kankama bayan da aka kwashe tsawon lokaci ana…

Yayinda ake kokarin dawowa wasanni a fadin nahiyar Turai, haka ma kasuwar cinikin ‘yan wasa ta fara kankama bayan da aka kwashe tsawon lokaci ana zaman gida saboda annobar coronavirus.

‘Yan wasa sun fara mayar da hankali a kan sauya sheka, ko sabunta kwantiragi yayin da masu horarwa da ma kungiyoyi suke zawarcin ‘yan wasa.

Adama Traore ka iya komawa United

Rahotanni daga Ingila sun nuna cewa kungiyar Manchester United ta baza komarta saboda ganin ta dauko dan wasan kungiyar Wolverhampton Wanderers, Adama Traore.

Jaridar Birmingham Mail ta rawaito cewa dan wasan gefen dan asalin kasar Spaniya ya haska sosai a wasannin da ya buga wa kungiyar ta Wolves a kakar bana inda ya jefa kwallaye shida ya taimaka aka ci kwallo sau 12 a cikin wasanni 43 a dukkan gasa.

Kungiyar Wolves din dai tana sa ran karbar tayi bayan an bude kakar sayen ‘yan wasa kuma tuni kungiyoyi da dama suka nuna aniyarsu ta dauko Traore din.

Chelsea na shirin daukar dan wasan Barcelona

Kungiyar Chelsea ce take kan gaba a kokarinta na dauko matashin dan wasan kungiyar Barcelona, Xavier Mbuyamba.

Yanayin taka ledar dan wasan mai shekaru 18 dan asalin kasar Holan ya sa ana kwatanta shi da dan wasan baya na kungiyar Liverpool Virgil van Dijk.

Shafin intanet na jaridar Daily Mail ya rawaito cewa dan wasan ya koma kungiyar Barcelona ne a kakar da ta wuce amma tuni mai kula da dan wasan, Carlos Barros, ya fara lalubar hanyar ficewarsa.

Barros ya fada wa jaridar Voetbal International cewa tuni manya-manyan kungiyoyi wadanda suka hada da Real Madrid da Juventus da Chelsea suka mika bukatunsu na dauko dan wasan.

Sane ba ya bukatar komawa Liverpool
Jaridar Sport Bild ta rawaito cewa matashin dan wasan Manchester City, Lorey Sane, ba shi da bukatar sauya sheka zuwa kungiyar Liverpool.

Rahotanni a Ingila sun ambato kungiyar ta Liverpool a karkashin jagorancin Jurgen Klop tana zawarcin dan wasan.

Liverpool za ta yi kokarin dauko dan wasan ne saboda kokarin da take yi na karfafa ‘yan wasanta na gaba.

Haaland ya ki amincewa da Juventus

Matashin dan wasan nan Erling Haaland wanda ya sauya sheka daga kungiyar RB Salzburg zuwa kungiyar Borussia Dortmund ya ki amincewa da tafiya kungiyar Juventus a kasuwar wasanni ta watan Janairu saboda kungiyar ta mika kudurin ajiye shi a gurbin ‘yan kasa da shekara 23.

Haaland, dan shekara 19, ya dauki hankalin manya-manyan kungiyoyi a nahiyar Turai saboda haskawa da ya yi wa kungiyar RB Salzburg. amma ya zabi ya sauya sheka zuwa kungiyar Borussia Dortmund a kan kudi Euro miliyan 18.

Hakan dai ya ba shi damar ci gaba da jan zarensa na cin kwallaye inda tuni ya jefa wa kungiyar kwallaye 12 a wasanni 13.

Ko Pochettino zai karbi jagorancin United?

Dan wasan kungiyar Tottenham wanda aka tura aro zuwa kungiyar Newcastle, Danny Rose, ya bayyana cewa tsohon mai horar da kungiyar ta Tottenham, Mauricio Pochettino, ka iya karbar aikin horarwa a Manchester United.

Tun dai da kungiyar ta Spurs ta sallame shi a watan Nuwamba bayan ya gaza kai ta ga nasara a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai da ta buga da Liverpool, Pochettino ya ci gaba da zama babu kungiya.

Kocin dan kasar Argentina bai bayyana  inda yake so ya koma ba duk da cewa ya gama hutun sallamar shi da Spurs din ta yi.

 Vertonghen zai duba yiwuwar sauya sheka

A nashi bangaren, dan wasan baya na kungiyar Spurs din Jan Vertonghen, yana duba yiwuwar karbar tayin da kungiyar Real Betis ta yi masa na komawa kasar Spaniya da taka leda.

Kwantiragin dan wasan zai kare a karshen kakar bana kuma ana sa ran zai bar kungiyar saboda tuni Spurs din ta shiga neman wanda zai maye gurbinsa.

Kungiyoyin Roma da Inter Milan da Valencia duk sun bayyana aniyarsu ta dauko dan wasan idan har kungiyar Spurs ba ta tsawaita yarjejeniyarsa ba.

Kungiyar Spaniya ta Real Betis ta yi hobbasa ta sha gaban sauran masu zawarcin dan wasan inda ta mika mishi kwantiragin shekaru biyu wanda tuni aka shiga tattaunawa da wakilinsa.

Arsenal na hangen Moussa Diaby

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shirya tsaf saboda dauko dan wasan Bayer Leverkusen, Moussa Diaby.

A ‘yan kwanakin nan dai tauraruwar dan wasan ta haska sosai a kungiyar, wanda hakan ya jawo hankalin manya-manyan kungiyoyi irin Arsenal.

Arsenal dai ta shahara wurin daukar matasan ‘yan wasa ta goge su kuma ta sayar.

Jaridar Le10sport ta rawaito cewa mai kula da dan wasan na Leverkusen yana da kyakkyawar alaka da hukumomin kungiyar ta Arsenal wanda hakan zai karfafa yiwuwar dauko dan wasan.

Kungiyar ta dauko Diaby ne bisa kudi Euro miliyan 15 a kakar 2019 wanda ake tunanin sai Arsenal ta yi kokarin ninka haka kafin ta shawo kan dan wasan.