✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump na ci gaba da kare shiga tsakani kan shari’ar wani sojan ruwan Amurka

A farkon makon nan ne, Shugaban Amurka Donald Trump, ya sake bayar da wani jawabi da ya saba da abin da aka yi na yin…

A farkon makon nan ne, Shugaban Amurka Donald Trump, ya sake bayar da wani jawabi da ya saba da abin da aka yi na yin canji a shugabanci a Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon.

Trump ya yi jawabin ne yayin da yake kare matakin da ya dauka a madadin wani sojan ruwan Amurka da aka yanke wa hukunci kan aikata ba daidai ba a lokacin yakin da kungiyar ’yan ta’adda ta IS a Iraki.

A lokacin da aka tambaye shi kan korar Sakataren Sojojin Ruwan Amurka, wanda farar hula ne, Richard Spencer, sai Trump ya fada wa manema labarai a fadar White House cewa, “Mun jima muna tunanin daukar wannan mataki. Amma hakan ba ta faru ba,” sannan a lokacin da ya bayyana a ofishin Shugaban Kasa tare da Firayi Ministan Bulgeriya ya kara da cewa, “Dole in kare mayakan da suka yi yaki.”

Shugaba Trump ya kuma kare umarnin da ya ba wa Sakataren Tsaron Amurka, Mark Esper, a karshen mako da ya soke shawarwarin da hukumar daraktoci da ta saurari kara kan Edward Gallagher.