✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya nada dan Najeriya a matsayin mai ba shi shawara

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nada dan Najeriya, Bayo Ogunlesi, a matsayin mamba a kwamitin da ke ba shi shawara kan tattalin arziki,…

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nada dan Najeriya, Bayo Ogunlesi, a matsayin mamba a kwamitin da ke ba shi shawara kan tattalin arziki, kamar yadda jaridar banguard ta ruwaito.

Tsohon Shugaban ’Yan Najeriya da ke zaune a Amurka Michael Adeniyi ya ce sun yi farin ciki da wannan nadi kuma abu ne da aka yi bisa cancanta, kamar yadda ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN).
“Mutum ne mai basira da kuma aiki tukuru. Ya samu nasara sosai a duk abin da ya sanya a gaba. Wannan nadin da aka yi masa, babbar nasara ce ga nahiyar Afirka da kuma Najeriya. Muna da yakinin cewa zai ba da kyakykyawar gudunmuwa a wannan sabon matsayi da aka ba shi,” inji Mista Adeniyi.
An haife Mista Bayo ne a ranar 20 ga watan Disambar shekarar 1953 (shekara 62 da suka wuce), a garin Shagamu mna Jihar Ogun.
Wani labarin kuma, a ranar Litinin ne Trump ya nada Ben Carson a matsayin Sakataren Kula da Gidaje da Raya Karkara. Mista Carson dai ya yi neman shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Republican, gabanin ya janye ya bar wa Mista Trump.
Akwai dimbin ’yan Najeriya a kasar Amurka, adadin da ya kai kaso daya cikin biyar na bakaken fatan da ke kasar.