✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya sallami Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami Shugaban Sashin Leken Asiri na kasar, wanda shi ne sashin da ke kare shi, da iyalinsa da kuma shugabannin…

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami Shugaban Sashin Leken Asiri na kasar, wanda shi ne sashin da ke kare shi, da iyalinsa da kuma shugabannin Amurka na da.

Kafafen watsa labaran Amurka da dama sun bayar da rahoton cewa, Shugaba Trump ya umurci Mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Fadar White House Mick Mulbaney da ya sallami Randolph Alles.

Shugaba Trump ne ya nada Alles, kuma ya kasance a kan wannan matsayi na tsawon shekara biyu. Babu wani bayani ga jama’a kan dalilin sallamarsa.

“Ya yi aiki sosai a wannan sashin a tsawon shekara biyu, kuma Shugaban Kasa yana cike da godiya gare shi saboda tsawon shekara 40 da ya kwashe yana bauta wa kasar. Nan gaba kadan zai bar ofis,” inji Kakakin Fadar White House, Sarah Sanders kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Ta kara da cewa, Trump ya gabatar da sunan James Murray, wanda dadadden dan sanda ne, a matsayin wanda zai zama sabon shugaban sashin daga watan gobe.