Da Dumi Dumi

Tsakanin Buhari, APC da kuma wadanda suka baibaiye shi

A wannan yanayi da muke ciki, idan ka duba siyasar kasar nan, akwai Muhammadu Buhari daban, akwai kuma ’yan siyasa daban. A hannu daya, Buhari na son ganin ’yan siyasa sun zama kamarsa, a daya hannun kuma ’yan siyasa na son ganin Muhammadu Buhari ya zama kamarsu, shi kuwa sam bai yi kama da su ba. Shi kansa Buhari, so yake duniya ta rika kallonsa a matsayin dan siyasa, duk kuwa da cewa bambancinsa da ’yan siyasa a bayyane yake karara. Rayuwarsa dai ta ta’allaka ne ga dabi’ar soja, haka ya ginu kuma ya rayu, daga bisani ne guggubin siyasa ke neman kutsa kai cikin rayuwar tasa.
Mafi yawan masu kaunar Buhari, suna son sa ne a matsayinsa na janar, suna nuna alamar haka ne ta yadda suke lillika hotunansa yana cikin khakin soja.  Kuma ba wani abu ke jawo wa Buhari masoya ba sai tsantsar gaskiyarsa da kyakkyawar dabi’arsa, amma ba wai tsantsar iya kalami ba. Kalaman ’yan siyasa suna fitowa ne daga kwakwalwarsu, domin kuwa abin da suke fadi, ba shi suke nufi ba, amma shi Buhari, maganarsa tana fitowa ne kai tsaye daga zuciyarsa, domin kuwa abin da yake fada, shi ke fassara tunaninsa da yadda yake kallon duniya. A yayin da dan siyasa zai iya shara karya da gangan, ya bar gaskiya idan ya san karyar nan za ta jawo masa magoya baya, shi kuwa Buhari ba zai iya yin haka ba. Shi tsaye yake kikam kamar falwaya bisa kalami daya, ra’ayi daya. Idan ya ce ‘e’ to haka take, idan ya ce ‘a’a’ haka take babu sabani, babu gudu babu ja da baya. Wannan hali kuwa ba na dan siyasar Najeriya ba ne.
A yau, ’yan siyasa sai tururuwa suke suna baibaye Buhari, kamar yadda kudan zuma ke baibaiye fulawa. Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne, domin kuwa masana halayyar dan Adam sun bayyana cewa, kishiyoyin juna sun fi daukar hankalin juna. Marar kyau ya fi neman mai kyau, fakiri ya fi neman mai dukiya, baki ya fi neman fari, daidai sauransu. Janar Buhari ya san cewa, a matsayinsa na mai neman kuri’un jama’a, dole sai ya sassauto da ra’ayinsa. Dalili ke nan ake ganin yana amincewa da kowane irin tarkace suna baibaiye shi. Buhari da aka sani na can baya, babu shakka ba zai iya shan inuwa daya da mafi yawan wadanda ke tururuwa a bayansa ba. Muna sane da cewa mafi yawan masu tururuwa bayansa, suna yi ne kawai saboda su dan haska, su samu wani dan mutunci, domin kuwa sun zubar da nasu mutuncin tun da dadewa a can baya. Irin wadannan mutane, idan ba bayan Buhari suka tsaya ba, babu wanda ma zai kalle su, balle ma ya kula su. Irin wadannan ’yan siyasa, idan a ce za su tsaya zabe kuma a ce zaben na gaskiya da gaskiya za a yi, hatta ’yan uwansu na jini da iyalansu ba za su zabe su ba.
’Yan siyasar nan da suka yi kaurin suna, suka samu daukaka ta hanyar karfa-karfa da tsageranci, suna fakewa ne a turakar CPC, ko kuma yanzu APC za mu ce? Kuma suna da babban dalilinsu na yin haka, domin kuwa a can baya sun yi wa inuwar da za ta amfane su kashi, don haka dole ne su shiga APC domin boye wa zafin ranar da ka iya narkar da su. Suna rakube ne tare da Buhari, domin gudun bacin rana, saboda su samu nasarar ci gaba da boye kazamar dukiyar da suka tara a wajen aikinsu da suka tafka a can baya.
Za ka ji suna kiran kansu da tsoffin gwamnoni ko tsoffin ministoci, ko… ko… amma dai sun kasance tamkar kaska, bi-mai-jini-ki- koshi. Shedan kansa zai yi shakkar ya yi tare da su, domin yana ganin sun fi shi karkacewa. Ba su da wata madafa idan ba bayan Buhari suka rakube ba. Suna tsoron cewa, madamar suka tsaya da kafafunsu, to idan lokacin shara da kakkaba ta zo, ba za su kai labari ba. Za ka ji suna kiran “Canji! Canji!!” a fili amma a zuciyarsu suna addu’ar Allah kada Ya kawo wannan canji.
APC, maganin da ke warkar da kowane laulayi – babu shakka shigowarsa wata babbar tsumagiya ce da ke hana muggan kuma azzaluman masu mulkin kasar nan barci. Da a ce kududdufin siyasar kasar nan bai dagule ya koma dagwalo ba, kila da ta hanyar APC an samu sa’ida. Irin yadda jam’iyya PDP ke ta walagigi da al’umma tsawon shekara 14, babu shakka muna bukatar ingantaccen canji. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, irin kurayen da ke baibaye da APC, ko za su iya canja halayensu zuwa nagari kuwa? Irin kuma yadda aka raba kan talakawa da wutar kabilanci da bangaranci da addinanci, ko za su iya kai bantensu a zaben 2015?
Babu shakka APC na da bukatar ta jajirce, ta yi aiki wurjanjan, ta kakkabe tsutsotsin da suka baibaye ta, ta kasance ’ya’yanta masu hadin kai da tsayin daka bisa gaskiya. Ta haka ne kawai nasara za ta kasance tare da su!

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya