✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi

Ko shakka babu ci gaba da yi wa juna kallon hadarin kaji da a tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi, sam bai dace ba, kuma…

Ko shakka babu ci gaba da yi wa juna kallon hadarin kaji da a tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi, sam bai dace ba, kuma ba zai haifar wa Jihar Kano da Arewacin Najeriya da mai ido ba. Na farko dai Gwamna Ganduje ya kamata ka bi a hankali domin hanyar jirgi daban ta mota daban, domin komai tsananin tsawon wa’adin mulki ba zai wuce shekara hudu ba a nan gaba. Shi kuma Sarki Sanusi za ka iya fada mana ko shekaru nawa suka rage masa a nasa wa’adin mulkin?

Gwamna Ganduje a matsayina na mai gidanka Bazamfare ina ba ka shawara cewa giyar mulki ta daina dibarka kana cin mutuncin Sarki mai daraja a idon duniya. Duk da cewa Sarki ya yi kuskuren nuna bambancin siyasa a lokacin zabe, to, amma bai dace ba, don Allah Ya ba ka nasara ka dauko makaman yaki ka ce sai ka rama wa kura aniyarta. Ko a addini an ce idan mutum ya bi ka da sharri, to, kai ka bi shi da alheri. Allah Yana son masu yafiya. Tun farko da ka samu mashawarta nagari kamata ya yi su ba ka shawarar da za ka kyale shi da abin da ya yi. Saboda shi mulki na Allah ne Shi Ya ba ka kuma zai iya kwace shi duk lokacin da Ya ga dama ko da ba ka shirya ba.

A karshe ina addu’ar Allah Ya kawo fahimtar juna a tsakaninku, Ya kawar da duk wasu shaidanun gefen kowane daga cikinku domin suke rura wutar rikici a tsakaninku.

Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan-Ɓaure (Dan kishin talaka) Jihar Zamfara. 07086868025.

Kira ga gwamnatin Jihar Jigawa

Assalamu Edita, ina so ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar Talamiz da ya duba girman Allah ya duba yankin Unguwar Jibrin.

Daga Yakubu Hamza U/Jibrin, 09092489097.

Kan zubar da jini a Zamfara

Assalam Amintacciyar jaridar Hausa. Jinjina gare ku, don Allah ina so ku taimake ni da isar da wannan korafi nawa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa ya sake waiwayar matsalar da Zamfara take ciki. Domin wallahi ba ranar da za ta fito ta fadi ba a zubar da jinin dan Adam ba a jihar. A karshe ina rokon Allah Ya sa wannan korafi nawa ya isa inda ya dace, allahumma amin.

Daga Mai duba jaridarku kowane mako Ibrahim Hassan Bazamfare. 07066485299.

Adalci muke so a Najeriya

Salam Edita. Ina son ka isar mini da sakona a kan irin namijin kokarin da Kotun Kolin Najeriya ta yi dangane da hukuncin da matsalar zaben Jihar Zamfara. Gaskiya na gamsu kuma na yaba muddin ana haka to ’yan siyasa za su shiga taitayinsu za su bi doka da oda. Fatarmu Allah Ya taimaki Najeriya.

Daga Musty Sakkwato 08034068363.

Rashin ruwan sama a Sakkwato!

Kira ga ’yan uwana jama’ar Jihar Sakkwato domin rashin saukar ruwan sama ba karamin tashin hankali ba ne. Ya dace kowa ya san abin da yake yi tsakaninsa da Ubangijji kuma ya yi kokarin gyarawa. Haka kuma ya dace mu ziyarci kaburburan ’yan uwanmu a makabarta domin gyaransu, Allah Ya ba da ikon aikata hakan amin.

Daga Elfarouk Maisaje Sakkwato 08022068895.

Sababbin Masarautun Kano

tada kura ne

Assalam Edita. A ba ni fili kadan domin fadin albarkacin bakina game da kirkiro masarautu a Kano. Bayan tada kura ne kuma a cire siyasa ba don ci gaban talakawa ba ne, idan ma an yi to da zarar an kafa wata gwamnati za ta rushe tsarin, ana yaudarar Kanawa ne.

Daga  Musa Haruna Chancerlor A Makarantar FUT Minna Jihar Neja, 08064949450.

Kirkiro masarautu a Kano ba alheri ba ne

Salam Edita barka da aiki. Don Allah a taimaka min da dan fili in yi murna ga Mai Martaba Sarkin Kano Malam Sanusi II da aikin alhakin da gwamnatin Kano ta rage masa na daukar dawainiyar al’umma. Ta bangaren gwamnati kuma, ta dauko hanyar wargaza mu. Kirkiro wadannan masarautu ba alheri ba ne. Bai kamata gabar siyasa ta shafi sarauta ba. Turawan mulkin mallaka ma sun mutunta masarautunmu.Ya kamata gwamnatin Kano ta sake tunani. Shi fa Gwamna ba ya wuce shekara 8. Amma sarauta gadonta ake yi daga iyaye da kakanni.

Daga Hamza A. Gombe. 0806160 1195.

Jihohi a yi koyi da Gwamnatin Katsina

Assalam Editan Aminiya, amitacciyar jaridarmu. Da fatar za ka mika mini sakona zuwa ga jihohinmu na Arewa cewa su dauki irin matakin da Gwamnatin Jihar Katsina ta dauka na yanke hukuncin kisa a kan duk wanda aka kama da laifin yin garkuwa da mutane ko satar shanu, sai kuma daurin rai da rai, hadi da tara ga masu laifin fyade. Wannan hukunci ya yi daidai. Idan sauran jihohinmu suka dauki irin wannan mataki to muna sa ran masu aikata laifuffuka za su shiga taitayinsu. Da fatar wadanda nauyin haka ya rataya a kansu za su kula da dokar da aiwatar da ita yadda take. Allah Ya sa hakan ya zamo silar samun zaman lafiya a Arewa.

Daga Babangida Jikan Mani Sabo Yaba Legas. 09031366660.

Jagororin APC a Zamfara  sai

a yi hattara!

Son rai ne ya sa Jam’iyyar APC a Zamfara ta rasa dukkan madafun ikon jagorancin jihar. Kuma muddin son ran ya ci gaba da wahala jam’iyyar ta kara tasiri a Zamfara. Don haka jagororin APC sai a yi hattara!

Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi, Tashar Bagu Gusau. 08069807496.

Jinjina ga Aminiya 

Salam Edita. Ka ba ni dama in mika sakon jinjina ga ma’aikatan jaridar Aminiya tare da fatar Allah Ya saka muku da alheri.

Daga Anisa Abdullahi Adamu Daura, 07067716102. 

Ta’aziya ga kasar Masar

Ina amfani da wannan dama wajen mika sakon ta’aziyyata ga iyalai da ’yan uwa da dukkan al’ummar kasar Masar a kan rashin wannan gwarzo, wato Shugaba Mohammad Mursi. Muna fata Allah Ya jikansa da rahama Ya bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020.

Muna neman agajin gaggawa

a Bauchi

Assalamu alaikum Edita. muna kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi a karkashin jagoranci sabon Gwamna Bala Muhammad (Kauran Bauchi) kan ta gaggauta kawo mana dauki a garuruwan: Cheledi, Bulakko, Ribar, Garmu, Kirfin Sama, Sindigawo. Domin ruwan sama yana mana barna sosai da zarar ya sauka wanda hakan ya sa ruwa yake yi mana kutse a gidajenmu. Da fatan gwamnatin za ta kawo mana dauki cikin kankanen lokaci domin kawo karshen fargabar da muke fuskanta a kullum.

Daga Alhaji Abbas Baffah, Cheledi Jihar Bauchi. 08120304020.

Albashin ma’aikata: Kira ga Gwamnatin Zamfara

Muna kira ga gwamnatin jiharmu ta Zamfara ta binciki dalilin da ya sa har yanzu ma’aikatan Hukumar Kula da Yaki da Jahilci (Mass Education) ba su samu albashinsu na watan Mayu ba, duk da cewa, watan Yuni na gab da karewa. Idan kuma gwamnatin na sane da rashin biyan wadannan ma’aikata albashinsu, to ya kamata ta gaggauta biyansu hakkinsu, ganin yadda wadansu daga cikinsu suka soma shiga wani hali.

Daga Mahmud Salihu Kaura Namoda, Zamfara. 09079551996

Fatan alheri ga sabuwar  Majalisar Tarayya

Assalamu’alaikum Aminiya. Muna fata sababbin shugabannin majalisun dattawa da na wakilai da ke jagorantar sabuwar majalisa za ta tuna bayan komawar kasar a kan turbar dimokuradiyya. Muna fata su zamo masu kishi da zuciyar kawo sauyi ga kasarmu.  Muna fata Allah Ya sa an bude majalisa ta tara a cikin sa’a, tare da kawo sauye-sauye masu ma’ana da kuma za su yi tasiri ga ci gaban kasa da al’umarta baki daya. Amin.

Daga Injiniya Shamsuddeen Abdullahi Rijau, Jihar Neja da Abubakar Ahmadu Nafada, Jihar Gombe. 07081235949.

Hukuncin kotu kan takarar Abba

Assalamu alaikum Edita. Don Allah Ka ba ni dama in bayyana ra’ayina a wannan filin mai albarka. Hakika hukuncin da alkalan Kotun Kolin suka tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Kaduna wacce ta yi watsi da bukatar Ibrahim Al’amin (Little) cewa PDP ba ta yi zaben fitar-da-gwani ba, wannan abin farin ciki ne gare mu. Muna fata a shari’ar Gwamna Allah Ya bai wa PDP nasara a Jihar Kano domin Abba ya zamo Gwamnan Jihar Kano, amin.

Daga Arbiyu Muhammad Gidan Madi A Sakkwato. 08067873852.

Ga ’yan Najeriya

Edita don Allah a ba ni fili in taya ‘yan Najeriya murnar ganin karshen zangon mulki na 2015-2019. Muna gode wa Allah sosai kan nasarorin da gwamnati ta samu. Allah Ya kara ba ta nasara a zango mai zuwa na 2019- 2023. Godiya ta musamman ga Alhaji Lawal Buhari Daura Shugaban Ilimin Bai-daya ta Jihar Katsina kan kokarinsa na ba yara ingantaccen ilimi a Jihar Katsina. Mun gode, Allah Ya saka da alheri, Allah ya kara kai likafa gaba.

Daga Amiru Isah Bakori. 07068147933.

Jama’ar Getso na godiya

 ga Ganduje

Don Allah Edita, ka ba ni dama in mika sakon godiya a madadin daukacin al’ummar garin Getso ga Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje kan yadda ya gwangwaje dan asalin Getso da Sakataren Ma’aikata wato Malam Tukur Makaman Getso. Tabbas  Gwamna ba abin da za mu ce da kai sai godiya bisa yadda kake tafiyar da   ’ya’yan yankinmu kuma suke rike maka amana. Tabbas sanadinka mun ga yadda asibitoci suka inganta karkashin jagorancin dan wannan yankin namu. Allah Ya kara taimakonka.

Daga Shehu Mansur Sule Getso 08037520051.