✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin lema da tsintsiya (1)

Bari na fara da wannan bayanin kamar yadda na saba a duk lokacin da nake nazari ko tsokaci ko sharhi game da al’amurran siyasar kasar…

Bari na fara da wannan bayanin kamar yadda na saba a duk lokacin da nake nazari ko tsokaci ko sharhi game da al’amurran siyasar kasar nan. Ni dai ba dan siyasa ba ne, amma kuma da yake Allah Ya yi ni dan Adam, wanda ko yana so ko ba ya so, dole siyasa ta yi masa tasiri, ko dai mai alfanu ko kuma jagwalgwalalla, dole ta sa wata sa’a nake cewa kanzil game da irin wannan damalmala ta siyasa a duk lokacin da hakan ya taso.
Na san wasu za su ce, ai ita da ma siyasa haka ta gada, kwamacala, rashin kan gado, barna da lalaci da lalatawa. Wasu ma iya cewa ai rashin madafa shi ne siyasa ko kuma munafinci da almundahana da rashin sanin makoma. Amma a duk lokacin da mutum ya natsu, ya yi nazari, ya kuma fuskanci yadda wasu al’ummomi a wadansu kasashe ke gudanar da siyasar da yadda can kwamacalar da kwadon siyasa mai ciwowa ne, ba na yarda wa ba, sai ya kara natsuwa cikin aminci da cewa, kila dai siyasar Najeriya ba ta da kan gado ne. Kila ‘yan siyasar Najeriya ne ba su san yadda ake zuba tuwon siyasa, kabaki-kabaki a cikin kwarya ba. Kila kasar Najeriya ce ba ta iya shuka iri a tata gonar siyasar ba ko kuma ba ta da irin na kwarai, kamar yadda ake shuka shi a wadansu kasashe, ba tare da an sa masa takin zamani ba!
Me ya sa na ce haka? Ba komi ya jawo hankalina ga haka ba face irin yadda na ga siyasar Najeriya a cikin ‘yan watannin nan ta rikice, ta balbalce, ta shiga cikin hayagaga, musamman ganin yadda jam’iyyar nan mai Lema ta shiga cikin rudu da neman wargajewa, sa’annan kuma wasu na ta murna cewa ai gara Shegiyar Uwa ta mutu, a share ta da Tsintsiya. Wane irin tunani ne wannan? Alhali kuma a duk lokacin da ake sharewa da kwashewa sai na ga ana sake zuba dattin a cikin dakuna ko falon jam’iyyar Tsintsiya. Ni kuwa a nawa tunanin, kai ko yaro dan shekara takwas ka tambaya zai bayyana maka haka, cewa, duk inda aka yi amfani da Tsintsiya aka yi shara, dattin nan, kwandon shara ko bola ake zuba shi, ba wai a kai shi cikin uwar daki ba, ana yi masa goma sha tara ta arziki, kamar yadda muke gani a halin yanzu!
To wai mene ne asasi? Me ya jawo wannan tabargaza a siyasarmu? Me ya sa mu kullum muke shiga cikin daki ido rufe? Me ya sa za a sharo dattin lalatattar Lema da Tsintsiya, amma a sake zuba dattin a dakin mai shara? Zan dawo kan wannan batun nan gaba!
Domin mu fahimci inda aka fito bari mu koma baya cikin tarihi, mu ga shin haka ake yi a wasu sassa na duniya dangane da siyasa da tsarin dimokuradiyya ko kuwa dai mu ne muke wa kanmu wuji-wuji gano gabas, amma mu kare muna kallon sama a matsayin gabas din?
Bari na soma da misalai guda biyu kawai na yadda siyasa da tsarin dimokuradiyya ke wakana a wasu kasashe, ciki har da wadanda muka ko muke kwaikwayo a tamu tafiyar. Kila bisa wannan fasali mu amince tamu siyasar, ba siyasa ba ce, sayayya ce da rana kiri-kiri.
Tsarin siyasa da gudanar al’amurran dimokuradiyya a ko’ina ya samu tsayuwa da gudanawa, abubuwa biyu ne suka assasa da tabbatar da shi. Na farko tsarin jam’iyya da mutanen da ke shiga cikin jam’iyyar. Na biyu kuwa fasalce-fasalcen tsarin shugabancin jami’iyyar da tsaren-tsaren da ta gindaya don ciyar da kasa da kuma al’umma gaba. Shi ya sa a wasu sassa na duniya za a tarar da jam’iyya daya ce ke godon mulki, ita kuma din da tsare-tsarenta da manufofinta da kuma hanyoyin aiwatar da su. Wata sa’a saboda kila rashin gudanar da al’amurra yadda ya dace ko kuma saboda gajiya da tsohon tsarin da wannan jam’iya take gabatarwa, sai a ga an samu jam’iyya mai adawa da wannan da ta yi dattin hula, ko kuma a samu wata da sauran jama’ar kasa ke ganin tsari da manufofinta sun fi wanda aka dade ana damawa da ita. Ta haka ne ake samun jam’iyya biyu ko uku suna tashe a cikin kasa domin a samar da zabi ga wadanda suka gaji da lamin wata siyasa.
Idan muka yi la’akari da irin wannan tsari sai mu ga cewa, kenan idan an ga hayayyafar jam’iyyun siyasa a cikin tsarin gudanar da dimokuradiyya to ba wai alamun ci gaba ba ne, ni a tawa fahimta, alamun rarrabuwa ce da sukurkucewa da lalacewa. Wani na iya cewa amma ai tsarin dimokuradiyya ne ya bayar da wannan dama, domin tsari ne na gwamnatin jama’a don samar da ribar dimokuradiyya ga jama’ar. Amma idan muka natsu sosai za mu ga cewa kasashe kamar su Amurka da Rasha da Ingila da sauran irin su, ai suna sane da wannan tunanin, amma suka takaita ko suka kasance sun zaba wa al’ummar su jam’iyyu biyu, manya, masu gudanar da mulki domin jama’arsu. Duk da haka ba su bari komi ya tabarbare ko zuguguce ba. A tuna, ba zama suka yi suka ce lallai ilau jam’iyyu biyu za su kasance a cikin kasar ba, a’a, sun tabbatar da cewa ai dan Adam fuska biyu ce gare shi, ko dai mai ra’ayin rikau ko mai son kawo sauyi, ko da kuwa a cikin tsari na kwaminisanci ne ko na jari hujja. Ko da kuma a cikin tsari ne na gargajiya ko na sarauta ko kuma na gado. Haka kum ko da  a cikin tsari ne na addini, sai an samu irin wannan rarrabuwa. Saboda haka, biyu ta fi daya, ta kuma fi uku ko barkatai, in dai gaskiya ake bukata.  Kenan ana iya cewa Amurkawa ko Rashawa ko Biritaniyawa ko Larabawa ko Asiyawa da makantan su, sun yi haka, ni a tawa fahimta saboda sun yi amanna cewa dan Adam fasali biyu ke gare shi, wato ko dai wanda ake dannewa ko wadanda ke dannewa! In abubuwa sun yi kamari ne ake samun ‘yan tsaka-tsaki ko ‘yan ba-ruwanmu, wadanda su ba su amince da daya daga cikin wadannnan tsare-tsare ba.
Shi ya sa a Amurka tsarin siyasarta da dimokuradiyyarta ya kasance jam’iyyu biyu ne manya, su ne kuma ake ta fafatawa da su cikin tsawon shekara 200. Ko dai jam’iyyar Democrats ko kuma Rebuplicans, a kuma kula, ba wai haka nan wadannan jam’iyyu suka wanzu da karfin gwamnati ba, ‘a’a tsari ne na gudanuwar al’umma a tsawon lokaci.
 Za mu ci gaba