✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin lema da tsintsiya (2)

Abin la’akari da tsarin jam’iyyun da ake da su a wasu sassa na duniya da kuma dangantakarsu da al’ummar da ke cikinsu, ba irin ta…

Abin la’akari da tsarin jam’iyyun da ake da su a wasu sassa na duniya da kuma dangantakarsu da al’ummar da ke cikinsu, ba irin ta auren zobe ba ce, ga wasu, auren mutu-ka-raba ne. Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin wadanda ke cikin wadannan jam’iyyun sun yi amanna da tsare-tsare da manufofi da sauran lamurran gudanar da siyasa, suna kuma tokabo da su. Koda kuwa a cikin babban tsari na kasa da akidojin gudanar da mulki a cikin kasar duk siffa guda ke gare su. Misali, ’yan Democrats na Amurka ba masu bin gurguzu ko kwaminasanci ba ne, a’a, ’yan tsaka-tsaki ne, abin da suke kire da Liberals. Duk da cewa babbar manufar kasar da tsarin gudanar da ita saiti daya gare shi, wato tsarin Jari-Hujja, wanda shi ne akidar tattalin arzikin da gudanar da lamurran kasa, amma sun amince da akwai masu rauni don haka ya dace a samar da mafi karancin albashi ga al’umma, sa’annan kuma a maka wa masu tarin dukiya harajin gani da fada. Wannan kuwa ya yi hannun riga da daya jam’iyyar siyasar wato ta ’yan Republicans, wadanda suke ganin tsarin tattalin arzikin kasa kamata ya yi, ya bar kowa ya ji a jikinsa, ke nan bai dace ba a tsara wani abu wai shi mafi karancin albashi, sa’annan ba su amince da zabga haraji ga mai karfi ko mara karfi ba, domin a nasu tunanin dukiya jarin mai ita ce.
Wadannan akidu ne da ’yan wadannan jam’iyyun siyasa suka amince da su, da su ake gudanar da rayuwa, ba ciri ba coge, sai inda ba a rasa ba. Shi ya sa alamun jam’iyyun ma yake dauke da wannan tunani, JAKI, shi ne alamar ’yan Democrats, alhali GIWA ce alama ga ’yan Republicans. A duk lokacin da ka ga ana yakin neman zabe a Amurka bisa wannan tunani ake yi, duk kuwa da dodoridon tsarin kasa da ke boye da kowannen ya amince da shi.
Haka wannan batu yake a Biritaniya ko Ingila, jam’iyyu biyu ne suke amayar da amonsu, ko dai Labour ko kuma Conserbatibes. ’Yan Labour su ne masu tattare da ‘talakawa’ su kuwa Conserbatibes, masu ‘ra’ayin rikau’ ne, ’yan mazan jiya, wadanda ba su yarda da rarraba dukiya ko tattalarta domin wasu gungun al’umma ba, a bar kowa ya yi kurme cikin tekun tattalin arziki, kuma iya ruwa, fidda-kai ne a tunaninsu, wanda ya sha bamban da na ’yan Labour. Inda ake samun dan canji shi ne, a Ingila akwai Liberals, wadanda su kuma ba sa bin hagun baki daya, sa’annan ba sa zaune daram a damar, a cikin tsarin siyasar ta Jari-Hujja.
Mun dauki wannan dogon lokaci muna wannan bayani saboda a fahimci cewa komai da tsari ya fi armashi koda kuwa cikin babban tsarin na kasa ana samun lauje a cikin hula. A kasashe kamar Amurka da Ingila, a tsawon shekaru jama’a sun kama turba guda, cikin wannan turba suke tafiya, ’ya’ya da jikoki, wasu har zuwa ga tattaba-kunne. Muhimmancin irin wannan tsari yana da dangantaka ne da dora kasa bisa alkiblar da ta dace, ba wai kallon mutane da ke cikin jam’iyyun ba, ko wadanda ke shugabancin jam’iyyar siyasa ba. Manufa ita ce abin kula, ba wai jam’iyyar siyasar ba.
Idan muka auna ko kwatanta wannan da abin da ke faruwa a cikin kasar nan, a halin yanzu za mu ga cewa tsarin namu a shiririce yake, inda ma ake da shi ke nan. Wata sa’a kuma kana iya cewa ba tsarin balle a yi godo da shi. Yanzu duk wanda ka tambaya mene ne tsari ko manufar Jam’iyyar Tsintsiya ko kuma Jam’iyyar Lema da ta dade tana mulki da wuya ka samu mai iya tabbatar maka da su. Idan ka ce ai Jam’iyyar Lema ce kadai ta kasance mai fuska daya daga cikin sauran jam’iyyun da ake da su (idan ban da kila Jam’iyyar Makulli ta Balarabe Musa) ba za a ce ka shara ta ba, shi ma ba wani abu ya jawo haka ba, sai ganin don suna bisa gadon mulki na tsawon kusan shekara 15, kuma da yake lagwadar siyasa da dimokuradiyya suna tattare da mulki kodai a matakin karamar hukuma ko jiha ko tarayya, musamman a Najeriya da wuya irin wannan jam’iyya ta canja salo cikin kankanen lokaci.
Amma ita kanta Jam’iyyar Tsintsiyar da aka samar a shekarar 2013, idan ka hankada labulen dakin nata abubuwan da za ka iske a cikin dakin suna da yawan gaske. Nan ne aka samar da hadakar ACN, wadda kafin nan ita ce ake ce da AC, sa’annan ta taba zama AD (ita kuma AD ai hadaka ce tsakanin Jam’iyyar Justice da ACD da wasu da dama) tun daga 2006. A cikin Tsintsiyar kuma yau akwai Jam’iyyar CPC, gyauron wadansu jam’iyyun na baya. Akwai ANPP da APGA, dukkansu gyauro ne na wadansu jam’iyyun ko kuma wasu ’yan gudun hijirar da suka baro wasu jam’iyyun da a da ba su ji dadin zama ciki ba. Irin wannan hadaka ta mabambantan ra’ayoyi da manufofi da akidoji da yawa ita ce ta kasance Tsintsiya daurarra, ko ba komai hannayen da za su kama domin yin sharar suna da yawa, sa’annan ga kowane da irin dattin ko sharar da yake fatar ya kai gare ta, jayayya a irin wannan hali, abu ne da ba za a rasa ba, ana so ko ba a so.
To amma ni ba wannan ne ya fi damuna ba, ina kallon batun ne ta fuskar yadda Najeriya za ta karu da wannan haduwa ta Tsintsiya idan har ta fice daga yagaggar Lema. Me ya sa na ce haka? Ba abin dulmiya tunani irin yadda sharar da Tsintsiya ke shirin yi ke neman komawa irin tsayuwar mai shika tana fuskantar inda iska ke bugawa, a maimakon ta ba bugun iskar baya, ta yadda kaikayin ke komawa jikin mai shikar.
Don Allah ina amfanin gwamnatin Tsintsiyar da ke tafe da sharar dakin Lema da karikitanta, kila ma ana ji ana gani mai doki yana iya komawa kan kuturi tun daga mazaba har zuwa fadar ASO, wannan tsari shi ne ci gaba, shi ne mafita?

Za mu ci gaba.