✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin malami da manomi, wa ya fi amfani ga al’umma?1

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman…

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu, wane ne ya fi amfani ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Malami ya fi manomi
– Yunusa Iliyasu

Yunusa Iliyasu: “Ni ina ganin malami ya fi manomi, tun da shi ne yake ilmintar da jama’a saboda idan ba ilimi mutane za su zama tamkar dabbobi. Shi kansa manomin ai malami ne ya koya masa yadda zai yi noma, idan ba malami babu yadda manomi zai san yadda ake noma har ya samu kayan amfanin mai albarka. Ai ilimi ya fi noma nesa ba kusa.”