✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin malami da manomi, wa ya fi amfani ga al’umma?3

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman…

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu, wane ne ya fi amfani ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Malami ya fi muhimmanci ga al’umma – Adamu Tahir Sabongida

Adamu Tahir Sabongida: “Ni a ganina, malamin addini ya fi mahimmanci ga al’umma saboda wadannan hujjoji nawa guda uku. Na daya, malami yana ba da ilimi ga al’umma su fita daga jahilci. Na biyu, malami yana koya wa al’umma tarbiya don samun da’a tsakanin jama’a. Na uku, malami yana taka rawar gani wajen wayar da kan jama’a su zama masu dogaro da kai, ma’ana su kama sana’o’i; tunda ai noma ma sana’a ne.”