✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin malami da manomi, wa ya fi amfani ga al’umma?4

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman…

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu, wane ne ya fi amfani ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Malami ya fi manomi – Ustaz Aminu

Ustaz Aminu Abubakar: “Gaskiya malamai sun fi, domin malamai ke karantar da su yadda za su yi noman. Domin Malami yana da tasiri sosai saboda shi kansa noman akwai yadda Musulunci ya koyar a yi. Lokacin da aka girbe akwai zakka da manomi zai bayar wadda kamar hakki ne na Allah daga cikin amfanin gonar. Wannan ya sa malami ke da tasiri a kan manomi. Shi manomi dama aikinsa ne kawai ya noma a ci. Amma ita kuma rayuwa ta zuciya fa? Malami ne ke raya ta. Wannan ya sa na ce malami ya fi amfanar da al’umma.”