✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin tarbiyyar ‘ya mace da da namiji wanne ta fi wahala?

A wannan makon, mun juyar da akalar muhawaramu ce zuwa batun tarbiyya kasancewar ana bukatar iyaye su kara kaimi wajen tarbiyyantar da ’ya’yansu. An dade…

A wannan makon, mun juyar da akalar muhawaramu ce zuwa batun tarbiyya kasancewar ana bukatar iyaye su kara kaimi wajen tarbiyyantar da ’ya’yansu. An dade ana tafka muhawara kan wahalar tarbiyya. Wannan ne ya sa muka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan tsakanin tarbiyyar ’ya mace da da namiji wanne ne ya fi wahala? Ga abin da suke cewaa:

 

Duk daya ne – Hajiya Maryam Sallau

Daga Abba Dalibi, Legas

Hajiya Maryam Sallau: “Ni a ganina tarbiyyar ’ya mace da namiji babu bambanci duk kusan abu daya ne, tarbiyyar ’ya’ya ta danganta ce daga iyaye. Shi yaro yana tasowa ne ya rayu a kan turbar da aka dora shi a kai, alal misali Allah Ya arzurta ni da ’ya’ya hudu mata biyu maza biyu na ba su kyakkyawar tarbiyya har suka girma kuma yanzu dukansu ne ke daukar dawainiyata. Bayan su kuma na rike ’ya’yan ’yan uwana da na ’yan uwan mijina su ma su hudu namiji daya mata uku don haka ni bisa fahimtata tarbiyyar ’ya’ya mata da maza duk abu guda ne. Kulawa da karatunsu na boko da na addini, sanya ido a kansu yadda ya kamata da hana su abokai barkatai da dora su a kan kyakkyawar turba, sannan uwa uba Hausawa sun ce itace tun yana danye ake tankwara shi.”

 

Tarbiyyar mace ta fi wuyar sha’ani– Ja’afar Muhammad Daga Adam Umar, Abuja

Ja’afar Muhammad:  “Tarbiyyar ’ya mace ta fi wuyar sha’ani fiye da na da namiji saboda larurorin da suke tattare da ita. Mace na bukatar tarairaya a daukacin rayuwarta sabanin namiji da zai iya kula da kansa har ya taimaki iyayensa a wajen nema tun daga kamar shekara 9 idan an sa shi a kan hanya. Ayyuka kanana kamar na gona idan kai manomi ne ko kiwo ko zaman shago idan kai dan kasuwa ne. Ita kuwa ’ya mace sai dai a yi mata kawai idan an sa ta a sana’a ce wadda za ta dace da ita ko idan ta ta samu aiki a girmanta, to a nan ma sai an hada da sa ido sosai saboda raunin da Allah Ya yi mata.”

 

Tarbiyar mace tafi wahala– Shamsu Kabir

Daga Ahmed K. Sararin Kuka, Katsina

Shamsu Kabir: “Tarbiyyar ’ya mace ya fi wahala fiye da ta namiji bisa wadannan dalilai; ita mace ana yi mata tarbiyya ce daga wurare biyu. tarbiyyar gida wadda take fara samu, sannan sai tarbiyyar gidan miji. Wadannan dalilin ne ma ke sa wa a lokacin bayar da auren ake cewa, ciyar da  ita da shanta da tarbiyyarta sun koma kan mijin. Sannan daga wajenta ne yara ke fara koyon tarbiyya. A kan wadannan dalilan da wasu ya sa koyar da mace tarbiyya ya fi wahala.”

 

Mace ta fi wahala – Alhaji Adamu Umar Katagum

Daga Abba Dalibi, Legas

Alhaji Adamu Umar Katagum: “Ni a tawa fahimtar tarbiyyar ’ya mace ta fi ta namiji wahala lura da raunin ’ya’ya mata da Allah Ya halicce su da shi. ’Ya mace na bukatar kulawa ta musamman wajen tarbiyya da gina rayuwarta fiye da da namiji. Don haka ne ma Allah Ya yi wa iyaye alkawari na musamman ga duk wanda Allah Ya ba shi ’ya’ya mata ya kula da tarbiyyarsu yadda ya kamata har zuwa aurar da su to ka ga daga nan za ka gane tarbiyyar ’ya mace ta fi na da namiji wahala.”

 

Akwai sarkakiya a tarbiyyar mace – Hajiya Edar Shettima

Daga Adam Umar, Abuja

Hajiya Edar Shetima Mustafa: “Tarbiyyar ’ya mace na tattare da sarkakiya ga kuma bukatar sassauci da lallami fiye da wanda ake yi wa da namiji. Dole ka sa ido a kanta sosai tare da bincike a kan lafiyar jikinta na boye lokaci bayan lokaci da kuma kula da wadanda take wasa da su a lokacin da take karama. Sannan idan ta kai shekarun farko na balaga ka san su wane ne kawayenta da sa ido a kan abin da take iya samu na kyaututtuka sabanin da namiji da bai fuskantar wannan barazana daga wajen mata in ban da yanzu da matsalar luwadi na yara da ake cewa ta shigo. Sai kuma abin da ya shafi sha’anin kwaya irin su taramol ko kodin da dukan jinsi na iya dauka daga wajen kawaye ko abokai. Idan ka yi iya kokarinka sai ka hada da addu’a ka bar wa Allah saura.”

 

Namiji ya fi wahalar tarbiyya –Happiness Igwe

Daga Ahmed K. Sararin Kuka, Katsina

Happiness Igwe: “Kowane lokaci tunanin namiji yawa yake yi a tsakanin abubuwa da yawa na rayuwar yau da kullum. Mafi yawa an fi tunanin namiji ya fita waje fiye da cikin gida. Kuma duk irin yadda za a nuna masa ko koya masa abu ba ya saurin dauka saboda yana ganin ya wuce ko ya fi karfin tsayawa ya saurara. Hasali ma, tun yana karami za a ga bai cika tsayawa ko wasa da uwa yana yi ba. Kokarinsa kawai ya nemi wani abu can shi da kansa ya yi.”