✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsananin bashi ya sa Ba’Indiye ya kona iyalinsa da gidansu

’Yan sanda sun kama mai bayar da bashi da ruwa bayan da ya tursasa wa wani Ba’indiye lebura da yake bi bashi, har ta kai…

’Yan sanda sun kama mai bayar da bashi da ruwa bayan da ya tursasa wa wani Ba’indiye lebura da yake bi bashi, har ta kai ga ya kona gidansu da iyalansa, inda matarsa da ’ya’yansa biyu suka mutu.

Mutumin dai yana kwance cikin mawuyacin hali, inda a ranar Litinin din da ta gabata aka bayar da sanarwar daga ofishin gwamnatin Tamil Nadu da ke Kudancin Indiya

Sandeep Nandurri wani babban jami’in hukuma da ke gundumar Tirunelbeti, ya ce mutumin ya karbi rancen Rupees dubu 142 (daidai da Dala dubu biyu da 150) a farkon wannan shekarar don fara harkokin kasuwanci, amma sai aka tursashi ya biya kudin ruwa tsagwagwa.

Wannan lebura da ya karbi rancen mai suna Esakimuthu ya biya kusan rubi biyun bashin da ya karba, amma mai bayar da bashin ya tsananta da neman karin wata Dala dubu uku.

Nanduri ya ce mutumin ana zargin tursasawar ce da ’yan sanda suka yi masa ya biya karin kudin, har ta kai sshi ga afkawa cikin bala’i.

“Mun fara bincike kan zarge-zargen cewa ’yan sanda da jami’an hukuma ba su taimaka wa mutumin ba,” a cewar Naduri kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Afp.

“Tuni aka sake wa wani jami’in dan sanda wajen aiki, kuma ana binciken rawar da ya taka a lamarin.”

Tuni dai aka kama mai bayar da bashi da ruwan, inda ake tuhumarsa da keta doka wajen ingiza mutum ya halaka kansa, a cewar Nuduri.

Dubban masu karamin karfi a Indiya, wadanda mafi yawansu manoma ne, bankuna na hanasu bashi, don haka suka dogara ga ,masu bayar da bashi da ruwa da ke bayarwa cikin hanzari.

Wadannan masu bayar da bashi da ruwan kan tsuga kudin ruwansu ya kai kashi 50 cikin 100, inda suke dabaibaye wadanda suka karbi basussukansu. Mafi yawansu kan yi amfani da barazana da tursasawa don a biya su basussukansu da aka karba.

daruruwan manoman da bashi ya yi musu katutu sun halaka kansu a shekarun bayan nan, musamman a Jihar Tamil Nadu, inda aka yi fama da matsanancin fari, al’amarin da ya haifar wa matalautan iyalai asarar dukiya.

Kimanin kashi 48 cikin 100 na manoman da ke Indiya suna karbar bashi daga masu karbar ruwa ba bisda ka’idar da doka ta shimfida ba. Irin wadannan masu bayar da bashi da ruwa da masu bayar da haya, a cewar wani rahoto da aka tattara a wajen bincike cikin shekarar 2012 ya tattaro daukacin binciken bashin Indiyawa da dimbin jarin da suka zuba a hada-hadar kasuwanci, wanda a Ingilishi aka yi wa lakabi da “All India Debt and Inbestment Surbey.”