Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Tsangaya ta koya wa almajirai 277 sana’o’i

Hajiya Maryam Isa Mele tana mika wa xaya daga cikin matan da suka koyi sana’ar Hoto Rabilu Abubakar
Hajiya Maryam Isa Mele tana mika wa xaya daga cikin matan da suka koyi sana’ar Hoto Rabilu Abubakar

Tsangayar Malam Muhammadu Basakkwace ta Darul Huda Islamiyya da ke Unguwar Malam Inna a garin Gombe ta koya wa almajirai da yara ’yan islamiyya 277 sana’oi’n hannu saboda su samu hanyar dogaro da kansu.

A lokacin gudanar da bikin yaye almajiran da aka koya wa sana’a, mai ba Gwamnan Gombe shawara kan harkokin walwala Hajiya Maryam Isa Mele jinjina wa tsangayar ta yi bisa bullo da shirin na samar wa almajirai hanyar dogaro da kansu.

ADVERTISEMENT

Hajiya Maryam Mele ta yi kira ga daidaikun mutane da su rika sayen irin wadannan kayayyakin da almajiran suka yi don a karfafa musu gwiwa wajen hana su yin bara, “amma muddin suna yi ba a saya dole su ga cewa wannan sana’ar ba za ta taimake su ba sai ka ga sun bari sun sake komawa barace-baracen da ba a so.”

Ta kuma yi kira ga gwamnati da ta shigo don karfafa wa wannan shirin na almaijirai saboda a samu karin almajirai da suke da sana’a wanda yin hakan zai taimaka sosai wajen rage yawan barace-barace.

ADVERTISEMENT

A lokacin koyar da wannan sana’a ta dauki nauyin yara ashirin maza goma mata goma, ta kuma ce nan gaba za ta kara yawan wadanda za ta dauki nauyin nasu.

Shi kuwa shugaban Hukumar Samar Ilimi na Bai Daya na Jihar Gombe SUBEB Farfesa Muhammad Gurama Dukku, wanda Malam Ibrahim Buraima ya wakilta cewa ya yi ana da makarantun tsangaya guda biyu ne a jihar Gombe daya a garin Bajoga daya kuma ita ce wannar ta Darul Huda.

Farfesa Gurama ya kara da cewa Darul Huda ita ce ta farko da ta fara irin wannan shiri kuma wannan shi ne karo na biyu da almajirai suka ci gajiyar shirin.

Sannan sai ya gode wa Hukumar Makarantar Tsangayar ta Darul Huda da suka yi hadaka da cibiyar koyon sana’oi ta Yidi Skills Ackuisition Centre da ke Kasuwar Mata don horar da daliban hanyar dogaro da kansu a rayuwa.

Shi ma Shugaban tsangayar, Khalifa Malam Muhammad Danlami ya bayyana dalilan da suka sa aka bullo da wannan shiri na koya wa almajirai sana’ao’i, inda ya ce duk wani almajiri da ke karatu ya samu hanyar dogara da kansa ya bar bara.

Cikin wadanda suka koyi sana’ar, Fatima Musthapha daga bangaren islamiyya wacce ta koyi dinki ta bayyana jin dadinta matuka gami da jinjina wa shugabannin makarantar Darul Huda, sannan ta ce yanzu ta samu hanyar dogara da kanta har zuwa karshen rayuwarta.

Muhammad Nyako Salisu, wanda ya koyi yadda ake gyaran dandalin taro wato decoration bayyana farin cikin sa ya yi na yadda wannan tsangaya ta su ta bullo musu da wannan shiri sannan sai ya gode wa wadanda suka koya musu sana’ar.

Sana’o’in da aka koya wa almajiran sun hada da saka da dinki da yin jakakkuna da takalma da hada turare da sauransu.