Aminiya

Tsangayar ‘yan jarida ta jihar Yobe ta jinjinawa Gwamna Buni

Shugaban tsangayar ‘yan jarida ta jihar Yobe Muhammad Abubakar, a madadin mambobin sa sun jinjinawa gwamnan jihar Mai Mala Buni, bisa kyautar mota sabuwa kirar bas mai kujeru 18 ga tsangayar wato ‘correspondent chapel of NUJ’.

Muhammad Abubakar, ya ce daukacin ‘yan jarida da ke jihar da ma mambobin tsangayar sun yaba wa gwamnan na yadda ya basu motar dan sauwake musu zirga-zirga wajen gudanar da ayyukan su na yau da kullum wajen shiga lungu da sakon jihar dan nemo labarai.

ADVERTISEMENT

Shugaban tsangayar ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya aikewa manema labarai mai dauke da sanya hannun sa, inda ya ce wannan motar wata hanya ce ta samun saukin zirga-zirgar su musamman wajen shiga yankunan karkara. Sanann ya nuna matukar godiyar su ga gwamnan na yadda ya gane suna taka rawar gani sosai a harkar watsa labarai a jihar da har yaji kukan su ya basu sabuwar mota.

Motar da ka bai wa ‘yan jaridar
ADVERTISEMENT