✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta a kimiyyance

GabatarwaAl-Fazaaree, daya ne daga cikin sahabban Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi), wata rana ya dawo gida, sai ya…

Gabatarwa
Al-Fazaaree, daya ne daga cikin sahabban Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi), wata rana ya dawo gida, sai ya samu matarsa ta haifa masa jariri baki sidik!  Nan take hankalinsa ya tashi.  Domin Balarabe ne shi, farin Balarabe kuwa.  Haka ma matarsa.  Amma ta yaya aka yi ta haifa masa jariri baki sidik?  Nan take ya nannade wannan jariri a zanen goyo, ya kama hanya sai wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi).  Yana zuwa ya tarar da shi cikin sahabbansa kamar galibin lokuta.  Yana isowa wajensa, bayan ya masa sallama, sai ya nuna wa Manzon Allah wannan jariri, ya ce: “Dubi abin da ta haifa mini.”  Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya fahimci inda ya dosa nan take,  sai ya ce masa: “Kana da rakuma?” Sai ya ce: “Eh, ina da su.”  Sai Manzon Allah Ya sake ce masa: “Mene ne launinsu?”  Sai ya ce: “Jajaye ne.”  Sai Manzon Allah Ya sake ce masa: “Babu wani mai launin baki-baki daga cikinsu?” Sai wannan Balarabe ya ce: “Akwai,”   sai Manzon Allah (SAW) Ya sake tambayarsa: “Daga ina ya samo wannan launi (bayan iyayensa jajaye ne)?”  Sai Al-Fazaaree ya ce: “Watakila wata jijiyar (dabi’ar) halitta ce ya jawo (daga kakanninsa (Genetics).”  Sai Manzon Allah Ya ce:  “Haka shi ma wannan, ta yiwu wata jijiya ce (Genetics) ya jawo (daga kakanninsa).”
Wata rana Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yana zaune sai ga wani daga cikin mutanen Madina ya riko matarsa, rike da jariri baki sidik su ma, a kidime.  Suna zuwa wajensa, sai mutumin ya ce: “Ga abin da ta haifa.”  Sai matar ta yi caraf ta ce: “Na rantse da Wanda Ya aiko ka da gaskiya, a matsayin cikakkiyar budurwa ya aure ni, kuma ban tava shigo da wani gidansa ya haye kan tabarmarsa ba.”  Fadin haka ke da wuya, sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya nuna cewa lallai abin da ta fada gaskiya ne.  Domin daga ita har shi suna da dabi’un halitta wajen casa’in da tara ga kowanne, kuma kowanne daga cikinsu na yaduwa cikin jikinta ne a lokacin saduwa, yana rokon Allah da Ya sa jaririn da za a haifa ya zo da kama irin nashi.
Ummu Sulaim ita ce mahaifiyar Anas dan Maalik (Allah Ya kara musu yarda).  Wata rana ta shigo inda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yake zaune tare da sahabbansa, sai ta ce: “Ya Manzon Allah, hakika Allah ba Ya kunyar bayyana gaskiya,  shin, wanka ya wajaba ga mace idan ta yi mafarki (ana saduwa da ita)?”  Sai Manzon Allah nan take ya ce mata: “Na’am, muddin ta ga ruwa.” (Ma’ana ruwan maniyya ke nan).  Nan take sai Nana A’ishah ta ce: “Shin mace ma na fitar da wani ruwa ne?”  Sai Manzon Allah ya ji, kuma ya ba ta amsa da cewa: “Kayya, A’ishah! Ta yaya ake samun kamaiceceniya to, (tsakanin jariri da iyayensa)?”
Daidai lokacin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya shigo garin Madina lokacin hijira, sai Abdullahi ibn Salaam, daya daga cikin manyan Malaman Yahudawan Madina ya je ya same shi, ya ce masa: “Na zo ne in tambaye ka kan wasu abubuwa guda uku, wadanda babu wanda ya sansu sai Annabi…”  Daga cikin tambayoyin da ya yi masa akwai neman sanin dalilin da ke sa jariri ke yin kama da mahaifinsa ko mahaifiyarsa?  Sai Manzon Allah ya amsa masa cewa: “Idan ruwan (maniyyin) namiji ya riga na mace, to, (jaririn) zai yi kama da mahaifinsa.  Idan kuma ruwan (maniyyin) macen ne ya riga na namijin, to, (jaririn) zai yi kama da mahaifiyarsa.”  Daga nan sai Abdullahi ibn Salaam ya ce: “Na shaida, hakika, babu abin bautawa a bisa cancanta face Allah, kuma lallai kai Manzon Allah ne.”
Daga cikin nau’ukan ilmin kimiyyar halitta da rai a duniyar yau, akwai fannin da ke bincike kan dalilan samun kamaiceceniya tsakanin ’ya’ya da iyayensu ko kakanninsu, na kusa ne ko na nesa.  Da kuma kamaiceceniya ta dabi’ar jiki; da dabi’ar tunani; da dabi’ar juriya ko ragwanci; da dabi’ar kirar jiki; da dabi’ar tsawo da gajarta; da dabi’ar zati ko mutumtaka; da dabi’ar sanyi ko zafin zuciya; da dabi’ar karfi ko kudurar zuciya; da dabi’ar taushi ko kaushin hali da yanayi; da dabi’ar bambancin launin fata, ko launin gashin kai, ko yanayin farata da dai sauransu.  Har wa yau, me ya sa wasu ’ya’ya ke gadon cututtuka daga iyayensu?  Me ya sa wasu ke yin kama da dangin iyayensu ba da asalin iyayensu ba?  Me ya sa ake haihuwar ’ya’ya masu dauke da cututtukan da iyayensu ba su da su?  Me ya sa, musamman a yau, likitoci da ma Malaman addinin Musulunci ke shawartar samari da ’yan mata masu niyyar aure da su je don gunadar da binciken jini da kwayoyin halittar jikinsu kafin su yi aure?  Me ya sa jaririn da ake haifa wani ke zuwa namiji, wani kuma mace?  Dukkan wadannan nau’ukan al’amuran halitta, ana binciken yanayinsu ne karkashin wani sabon fannin ilmin likitanci mai suna “Genetics”, ko “Heredity”ko kuma “Genetic Inheritance”, a Turancin kimiyyar halitta da rai.
Hadisin farko da ke sama, Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi, tare da sauran malaman sunan, wato Abu Dawud da Tirmidhi da Nasaa’i da Ibn Majah.  Hadisi ne ingantacce. Hadisi na biyu kuma mursal ne, ba hadisi ba ne ingantacce, amma ma’anar da ke cikinsa daya ce da wadda ke cikin hadisin da ya gabace shi.  Wato hadisin farko ya karfafe shi wajen ma’ana ke nan.  Hadisi na uku ingantacce ne, domin Muslim ne ya ruwaito shi.  Sai hadisi na hudu, wato hadisin Abdullahi ibn Salaam, shi ma ingantacce ne, domin Bukhaari ne ya ruwaito shi. Dukkan al’amuran halitta da ke dunkule cikin wadannan hadisai da suka zo a sama, abubuwa ne masu ban mamaki da suka faru, wadanda a lokacin faruwarsu babu wanda zai iya gudanar da wani bincike a likitance, don gano sababbin faruwarsu, sai dai kawai a yi imani.  
A yau, Allah Ya kawo mu lokaci da zamani mai cike da yalwa wajen samuwar kayayyaki da fasahar binciken kimiyya da likitanci, cikin sauki.  Ganin irin tasirin da wannan tsarin bincike ke yi a sauran kasashen Turai na yau, musamman kasar Amurka, ya sa na ga dacewar gudanar da bincike na musamman don kosar da masu karatu, da yardar Allah, dangane da wannan sabon fannin bincike, duk da cewa dadadden ilmi ne.  Amma Malaman kimiyyar zamani ba su fara gudanar da bincike a cikinsa ba, sai cikin shekarar 1981.
Wannan kasida za ta gudanar da bincike ne kan asali da dalilan da ke haddasa wadancan al’amura.  Da farko bayanai za su zo kan ma’anonin kalmomin Turanci masu alaka da wannan bincike, wadanda mai karatu zai ta cin karo da su a halin karatunsa.  Sannan bayanai kan “kwayar Halitta” ko “Tubalin Halitta”, watau “Cell” su biyo baya.  A nan ne za mu fahimci tsarin wannan sinadari mai matukar muhimmanci da yanayinsa da muhallinsa da adadinsa da kuma abubuwan da ke kunshe a cikinsa, musamman irin su “Tantanin kwayar Halitta” ko ganuwarta, watau “Cell Membrane” da “Ruwan Rayuwa”, watau “Cytoplasm” da kuma “Asalin Sinadarin Halitta”, watau “Nucleus.”  A cikin sinadarin halitta ne al’amuran da suka shafi bincikenmu suke tattare.

 

Jaje…
Salamun alaikum Baban Sadik, ina yi maka addu’a da Allah Ya kiyaye gaba, Ya sa kaffara ne, abin da aka rasa. Kuma Allah Ya mayar da mafi alheri.  Su kuma Allah Ya shirye su, idan masu shiryuwa ne, idan ba masu shiryuwa ba ne, Allah Ya tona asirinsu, amin. Daga

Assalaamu alaikum Baban Sadik, Allah Ya mayar da mafi alheri na abin da aka rasa, Ya kuma kare gaba.  Daga: 08032079425

Assalaamu alaikum Baban Sadik, na samu labari varayi sun shiga gidanka su maka satar kwamfuta, to, ina maka jaje.  Allah kiyaye gaba, Ya kuma mayar da mafi alheri.  Su kuma Allah Ya tona musu asiri.  Daga: Ali Garba Okene: 08066369653

Ina mika godiyata ga daukacin masu karatun wannan shafi, musamman wadanda suka aiko mini da sakonnin nuna alhini da jajen satar da varayi suka yi mini. Mutanen kuwa sun hada da Sadik Nasidi Sa’al, Kano: 08060302454 da Musa Muhammad ’Yan Kaba, Bakin Dogo, Kano: 08104001040 da Mu’azzam Suleiman Kano: 08179705299 da Sunusi Sani Dala: 08036800241 da A’isha Ibrahim Zariya. tare da daukacin wadanda ba su  ga sunayensu ba.

Ma’aiktan Aminiya ma suna mika jajensu ga Baban Sadik kan wannan jarrabawa. Allah Ya kiyaye gaba, Ya kuma mayar da alkhairi, amin.