✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin Ma’adanar Bayanai a Kimiyyance (1)

Mabudin Kunnuwa Rayuwar dan Adam a yau tana gudanuwa ne cikin wani tsari mai ban al’ajabi musamman a bangaren sadarwa.  Kusan duk wani abin da…

Mabudin Kunnuwa

Rayuwar dan Adam a yau tana gudanuwa ne cikin wani tsari mai ban al’ajabi musamman a bangaren sadarwa.  Kusan duk wani abin da mutum zai iya tunawa a zamanin baya a fannin sadarwa, a halin yanzu sun canja; canji mai cike da ci gaba mai ban mamaki, wanda shi kansa dan Adam bai taba tunanin faruwar hakan ba. Ginshikin da ke tabbatar da gudanuwar tsarin rayuwa ta fannin sadarwa a yau kuwa shi ne “gurbin” da ake iya adana wadannan bayanai da ake musayarsu a tsakanin jama’a, da kasashe – ta amfani da hanyoyi da kuma na’urorin sadarwa na zamani.

Daga kwakwalwa (Brain) har zuwa tsarin taskance bayanai na tafi-da-gidanka (Cloud Storage) da ake amfani da su a wannan lokaci da muke ciki (2018), dan Adam bai gushe ba wajen neman hanya mafi inganci don taskance bayanan da yake rubutawa ko musayarsu a tsakaninsa da sauran abokan hulda, wajen zamantakewa da kasuwanci da siyasa da ilimi da sauran fannonin rayuwa.

Daga wannan mako, cikin dacewar Ubangiji, za mu fara gudanar da bincike tare da sabunta bayanai, kan abin da ya shafi asali da samuwar ma’adanar bayanai a tarihin duniyar wannan zamani da muke ciki. Da farko dai za mu bibiyi tarihi don sanin wace hanya ce dan Adam ya fara amfani da ita wajen taskance bayanai a rayuwarsa?  Sannan wadanne hanyoyi ko fasahohi ne ya yi amfani da su a baya?  Bayan haka, mene ne dalilin da ya sa yake ta sauya hanyar taskance bayanansa? Bayani a kan hanyoyi ko fasahar da dan Adam ya yi ko yake amfani da su wajen taskance bayanai zai zo ne a fadade, don bai wa mai karatu damar fahimtar irin baiwa da ni’imar da Allah Ya yi masa, wacce ta samar da ci gaban da yake gani a yau a fannin sadarwa na zamani da kere-kere. A karshe kuma wannan kasida za ta bibiyi hanyoyin da suka dace mai karatu ya bi don taskance bayanansa a rayuwarsa gaba daya.

A halin yanzu dai ga takaitaccen tarihi nan kan yadda dan Adam ya samo asalin hanyar taskance bayanai a rayuwarsa ta yau da kullum.

Farkon Al’amari

Dan Adam bai gushe ba a matsayinsa na halitta mai rai, mai kai-komo, mai irada da kokarin ganin ya cimma manufofinsa a wannan doron kasa, wajen taskancewa ko adana bayanan da suke kunshe da manufofin da ya cimmawa a baya, da wadanda yake kan aiwatar da su da kuma wadanda a nan gaba yake son aiwatarwa. A farkon al’amari, dan Adam ya siffantu ne da dabi’ar taskance bayanai ta hanyar haddace su a kwakwalwarsa kai-tsaye. Duk abin da zai iya tunawa, to, shi ne bayanin da yake da iko a kansa. Wadanda ya mance su kuma sun tafi ke nan. Idan ba tuna su ya yi ba sa’ar da yake da bukatarsu, to sai dai wani lokaci. Wannan tsari, ne mai inganci matuka, musamman ganin cewa idan har haddar ta kai makura, da wahala a iya mance abin da aka taskance a kwakwalwa. Sai dai kuma yanayin tsufa da tabin hankali kan sa wannan ma’adana ta samu rauni.

Da tafiya ta yi nisa, sai zamani ya sauya. Shagulgula suka dabaibaye dan Adam har ta kai ga ya fara gajiya wajen dogaro da kwakwalwarsa kadai wajen adanawa da taskance bayanan da yake bukata don tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum. Wannan ya sa cikin hikimar da Allah Ya ba shi na tunani, ya kirkiri hanyar alamanta bayanansa kan abubuwan da ke muhallinsa. Misali, idan yana bukatar tunatar da kansa kan wani abu, sai ya yi alama mai nasaba da wannan abin da yake son tunawa a jikin dutse ko tafin hannunsa ko jikinsa ko kuma fatar dabbobi da bawon itatuwan da ke kewaye da shi. Har wa yau, wadannan alamu da yake yi ba su takaitu ga abubuwan da ke muhallinsa kadai ba, hatta a jikinsa yana yi, don tunawa da dangi ko dan uwansa. Mun sha samun labarai kan abin da ya shafi asalin zane da mutane ke yi. Da dama aka ce ya samo asali ne daga alama da dangi ke yi wa ’yan uwansu, don gane su, ko kuma wadanda fataken bayi ke yi wa bayin da suka saya, don hana su cakuduwa da na wadansu fataken daban.

Wannan zamani shi ma bai gushe ba sai da dan Adam ya samu fikira wajen iya rubutu da kuma karanta abin da ya rubuta. Nan take sai ya sauya hanya da ma’adanar taskance bayanansa; daga zane ko alama da yake yi a saman karikitan da ya ci karo da su, zuwa amfani da fasahar rubutu a kan duwatsu ko fatu ko makamantansu. Wannan tsari na rubutu da ya kirkira shi ma ya taimaka masa sosai wajen kawo masa ci gaba. Domin daga nan ne ya fara taskance fasahar yin abubuwa da tarihi da tsarin tafiyar da rayuwa a irin muhallin da yake, da sauran hanyoyin ci gaba.

Bai tabbata a kan haka ba sai da Allah Ya sake hankaltar da shi wata hanyar daban. Hakan kuwa ya faru ne bayan wasu karnoni, sa’ar da ya kirkiri fasahar rubutu da karatu a kan takarda tare da tara su waje daya a matsayin littafi, don ci gaba da tafiyar da rayuwa yadda ta kamata. Wannan hanya ta dada saukake hanyoyin da dan Adam yake bi wajen taskance ilimi da tafiyar da rayuwarsa, sama da hanyoyin baya. Domin tana cikin hanyoyin da suka fi kowace dadewa yana amfani da ita wajen taskance ilimi har zuwa wannan zamani da muke ciki. Domin ta hanyar littattafai ne ya ci gaba da taskance ilimin kimiyya da fasaha da tarihi da hanyoyin mulki. Har wa yau, bai tsaya a nan ba, a littattafai ne yake taskance wakokinsa da hotunansa da taswirorinsa, da duk wata alama da ke iya taimaka masa wajen tafiyar da rayuwarsa a ilimance.

Duniyar Yau

Tsakanin karni na 18 zuwa karni 19, sai ya fara samo wasu hanyoyi da ya fara bi wajen taskance wasu nau’ukan bayanai na musamman, maimakon littafi da yake amfani da shi a baya.  Misali, ya kikkiri wasu nau’o’in fasahar taskance wakoki ko sauti ko murya ta yadda zai rika sauraronsu a duk lokacin da ya bukace su, ba sai ya rera su da kansa ba; sabanin yadda abin yake inda a rubuce suke a littafi. Haka kuma ya kirkiri fasahar da yake amfani da ita wajen samar da hotuna da taswira, sabanin lokutan baya da yake amfani da yatsun hannunsa wajen zana su ko yin tambarinsu a kan littattafai ko shafin takarda.

Sannan da tafiya ta yi nisa, sai ya kirkiri fasahar taskance hotuna masu motsi, wato na bidiyo ke nan, tare da hanyar yin hakan a aikace, wato fasahar aikin talabijin ke nan.  A yau cikin taimakon Allah, dan Adam ya wayi gari da wasu fasahohi masu dimbin tasiri wajen taskance masa dukan abin da ya kirkira na bayanai, daga rubutu da hotuna masu motsi da daskararru, zuwa zane da taswira (maps), duk yana iya taskance su cikin ma’adana guda daya, mai daukar bayanai masu dimbin yawa, mai kuma amfani da wutar lantarki. Wannan ma’adana mai wannan tsari ita ake kira “Digital Storage System.”

Wadannan nau’o’in kayayyakin fasahar ma’adana da dan Adam ya kirkira dai sun hada da faya-fayen garmaho (Gramophone Records) da kaset na rediyo da bidiyo da faya-fayen CD da na DBD, zuwa ma’adanar Floppy Disks da Zip Disk da Flash Dribe da Memory Card da kuma uwa uba Hard Disk Dribe, wato babbar ma’adanar kwamfuta ke nan, wacce ke taskance dukan manhajojin da ke dauke cikin kwamfuta, a kunne take ko a kashe. Wadannan hanyoyin taskance bayanai da a yau galibinsu ke kai-komo a hannayenmu, na da hannu wajen haddasa ci gaban da aka samu ta hanyar ilimi da saukin samunsa da haddasa kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sauran nau’o’in ilimi. Kuma dukan wannan kokari, kamar yadda za mu karanta nan gaba, dan Adam ya yi su ne sanadiyyar wayewa da yake samu ta hanyar sauyin zamani da kuma darasi da yake dauka wajen amfani da abubuwan da ya kirkira a baya: shin suna biyan bukata ko ba su biya? Sannan ya sauya musu siffa ko yanayi, har aka kawo ga zamanin yau. A karshe, hakan ya dada haddasa masa ci gaba mai girma da tasiri a rayuwarsa, ta yadda ya wayi gari babu abin da ke masa hidima sai wadannan kayayyakin fasaha.

Idan mai karatu na biye da mu a wannan shafi mai albarka, zai samu bayanai filla-filla kan kowanne daga cikin nau’o’in ma’adanan da sunayensu ya gabata a sama. Da wannan, zai ga irin ci gaban da aka samu da irin yadda fasahar sadarwa da kere-kere ke tasiri a rayuwar dan Adam wajen haddasa kirkire-kirkire a fannoni da dama. Wannan har wa yau ke nuna cewa dan Adam halitta ne mai dauke da dimbin tunanin ci gaba da wayewa da kuma kirkire-kirkire. Amma kuma babu abin da ke jawo masa wadannan siffofi sai neman ilimi da kuma kwatanta abin da ya koya a aikace, wato aiki da ilimin ke nan. Duk al’ummar da ta bi wannan hanya na daukar ilimi da kwatanta shi, za ta ci gaba. Wacce kuma ta karanta kadai ba ta kwatanta ba, ko kuma ta ma ki karatun gaba daya, sai dai kallo. Allah kiyashe mu!

A ci gaba da kasancewa tare da mu.