✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin Ma’adanar Bayanai a kimiyyance (3)

Fallayen Faifan CD Mai karatu zai yi mamakin jin cewa kowane Faifan CD guda daya hadaka ne na fallaye guda biyar, wani a kan wani.…

Fallayen Faifan CD

Mai karatu zai yi mamakin jin cewa kowane Faifan CD guda daya hadaka ne na fallaye guda biyar, wani a kan wani. Kowanne daga cikin biyar din nan yana da aikinsa da siffarsa da kuma tsarinsa, wanda ya sha bamban da wanda yake sama ko kasa da shi. Kamar yadda mai karatu zai gani daga hoton da ke dauke da wadannan fallaye guda biyar, da zarar ka fede kowane Faifan CD, abin da za ka samu ke nan. Mu fara daga kasa zuwa sama mu gani. Bangaren farko (harafin “A”) shi ne bangaren da ke fuskantar idon lantarkin da ke sarrafa shi a jikin na’urar CD Player. A takaice dai shi ne cikin Faifan CD, wanda idan ya samu kwarzane ko datti ya cika shi, to sai an samu matsalar kallo ko sauraron abin da ke cikinsa. Wannan bangare na farko dai gasasshiyar roba ce nau’in Polycarbon, kuma ita ce ke taskance dukan bayanan haruffa ko wakoki ko hotunan da ke ciki, tsibi-tsibi (ko Bumps, kamar yadda Malaman Kimiyyar Sadarwa suke kiransa). Sai bangare na biyu (harafin “B”), wanda a siffar gilashi ko rariya yake. Aikinsa shi ne hasko dukan bayanan da ke tare a cikin bangaren farko da bayaninsa ya gabata. Sai bangare na uku (harafin “C”), wanda faifai ne mai dauke da sinadaran kimiyya nau’in Lackuer. Aikin wannan falle kuwa shi ne taimaka wa bangare na biyu yin aikinsa yadda ya kamata, ta hanyar tabbatar masa da tagomashin sinadaran da ke haskaka wadannan bayanai da ke fallen farko, kamar yadda bayanai suka gabata. Idan muka kara sama kadan za mu ci karo da bangare na hudu (harafin “D”), wato bangon da ke dauke da tambari ko sunan faifan ke nan daga saman faifan. Aikinsa shi ne daukar tsarin rubutu ko alamu da za a iya mannawa don sanya suna ko shaida. Har wayau, idan mai karatu bai mance ba, wannan bangare ne ke dauke da sinadaran ruwan tagulla da na nau’in Lackuer, don bayar da damar sanya tambarin.

Sai kuma bangare na karshe (harafin “E”), wato wurin karshe da ke gefen kowane Faifan CD, mai kyalli mai kuma kaifi. Mai karatu ya lura a duk sa’ar da ya dauki Faifan CD, zai ga tambarin da aka manna a bayansa bai lullube wannan bangare ko gargare siriri ba. Wannan bangare, idan ba a mance ba, shi ne wanda a baya muka kira Rim a Ingilishi, kuma yana dauke ne da sinadaran kimiyya na haske nau’in Laser. Har wayau, yana damfare ne da falle na biyu (harafin “B”).  Aikinsa shi ne yin amfani da wannan sinadaran haske na Laser don ya fito da hasken da ke samuwa a falle na biyu da muka yi bayani, wanda shi kuma ke hasko bayanan da ke cikin fallen farko (harafin “A”). Ma’ana, idan ka sanya Faifan CD a cikin na’urar da ke sarrafa shi, wato CD Player da zarar ya fara juyawa, idon hasken lantarki da ke cikin na’urar zai haskaka faifan, sai wannan bangare na biyar (da ke harafin “E”) ya yafito hasken, don cilla wannan haske zuwa falle na biyu, wanda kamar madubi ne ga fallen da ke dauke da bayanan da ke cikin faifan. Da wannan mai karatu zai fahimci cewa kowane Faifan CD na amfani ne da haske wajen fahimtar sakon da ke cikinsa da kuma jiyarwa ko nuna bayanan da ke ciki.  Wadannan fallaye biyar da bayaninsu ya gabata, su ne aka hade su waje daya a matsayin Faifan CD guda daya. Kuma shi ya sa a Ingilishi ake kiran kowane Faifai da suna: Compact Disc, ma’ana faifai mai dauke da wasu faya-fayen a cikinsa; wadanda aka hade su wuri guda.

Tsarin taskance bayanai

Tsarin taskance bayanai a Faifan CD ya sha bamban da tsarin taskancewa ko adana bayanai a kwamfuta a kimiyyance da fasahance. A fasahar taskance bayanai a kwamfuta, na’urar kwamfuta na karba tare da adana bayanan da ake shigar mata ne a tsarin lambobin “sifiri” da “daya”, wato zeros and ones (0 and 1).  Duk abin da aka shigar mata na bayanai, kowane iri ne, a irin wannan tsarin take taskance su. Hatta allon shigar da bayanai (Keyboard) da mai mu’amala da kwamfuta ke sarrafawa wajen shigar mata da bayanai, duk harafin da ya matsa, kwamfutar ba ta ganinsu, sai dai ta ga lambar sifiri (wato ‘0’) ko kuma daya (wato ‘1’).  Haka duk sa’ar da ka tashi nemo wadannan bayanan a cikin kwamfuta, da wadannan lambobi na “sifiri” da “daya” take gano inda ta ajiye maka su. To amma a tsarin Fasahar Faifan CD, ba haka abin yake ba.

Duk bayanan da aka shigar wa Faifan CD ta hanyar kwamfuta ne ko ta hanyar na’urar shigar da bayanai da kamfanoni ke amfani da ita wajen yin haka, bayanan na shiga ne tare da zama cikin faifan a wani tsari da ake kira Non-Return-to-Zero Inberterd (NRZI) Format.  Wannan tsari ne na shigar da bayanai da kuma sarrafa su ta hanyar kai-komo tsakanin “ramuka” da kuma “tuddan” da ke jikin Faifan CD, masu taskance bayanan.  Yadda tsarin yake kuwa shi ne, kowane Faifan CD na rike bayanai ko adana su ne a cikin wasu kananan “ramuka” da a Turancin Fasahar Sadarwa ake kira Pits da kuma tuddai (jam’in “tudu”) da ake kira Lands.  Dukan bayanan da ake shigarwa na cikin wadannan ramuka ne.  A yayin da kuma tuddan ke tsayawa a matsayin kariya ga wadannan bayanai da suke cikin ramukan.  Wadannan ramuka na jikin kowane Faifan CD ido ba ya riskarsu kai-tsaye, sai da taimakon na’urar fadada hoto, wato Magnifying Glass.  Amma haka kawai, ba za ka iya ganin abin da ke jikin shafin faifan ba na ramuka ko tudu.  Kowane rami na da zurfin nanomita dari ne (100nm) da fadin nanomita dari biyar (500nm) tsakanin kowane tudu da tudu ke nan.

Tsarin sarrafa bayanai

Bayan tsarin shigarwa ko taskance bayanai a Faifan CD, na san mai karatu zai so jin ta yaya na’urar CD ke sarrafa irin wadannan bayanai har ake iya ji ko gani ko kuma amfana da rubuce-rubucen da ke cikin kowane Faifan CD, idan mai dauke da kasidu ne ko makaloli? Wannan tambaya ce mai mahimmanci, kuma amsarta ba a nesa take ba. Mai karatu na iya sarrafa bayanan da ke cikin kowane Faifan CD ne ta hanyar shigar wa na’urar CD (CD Player) faifan, a kifa shi a saman idon na’urar (wato CD Lens). Da zarar ka sanya, ka kunna na’urar, akwai haske da ke bayyana, wanda ke haskaka wannan faifan, don karanto nau’in bayanan da ke ciki; idan na hoto ne, ta nuna su a matsayin hotuna – da launinsu da girmansu da ingancinsu da fadinsu da kuma yanayinsu. Idan na sauti ne, ta jiyar nan take, ta hanyar kididdige yawan wakokin da ke ciki da kuma jiyar da su daya-bayan-daya. Idan kuma hoto mai motsi ne (bideo), ta nuna nan take ta hanyar farawa daga farko, zuwa karshe.

Hakan kuwa na faruwa ne ta hanyar alakar da ke samuwa a tsakanin Faifan CD din da kuma na’urar da ke sarrafa shi, wanda wani haske mai kama da na sinadarin hasken Infra-red nau’in Laser ke hadawa a tsakaninsu. Tazarar da ke tsakanin wannan idon lantarki na haske da kuma faifan ya kai nanomita dari bakwai da tamanin (780nm); wato kasa da mita daya ke nan. Wannan hasken ne ke kwaso bayanan da ke cikin faifan, ta hanyar jele tsakanin “ramuka” da kuma “tuddan” da ke jikin faifan, tare da sarrafa shi, don jiyarwa ko nunawa ko kuma bayar da damar amfana da kasidu ko makalolin da ke cikin faifan, idan mai dauke da bayanai ne irin wannan. Har wa yau, daga cikin hikimar da ta sa kowane Faifan CD ya mallaki wadannan ramuka shi ne, don bai wa bayanan da ke cikinsa damar kauce wa datti ko kura da ka iya shafar fuskar faifan, a yayin da na’urar ke sarrafa shi. Tirkashi! Wata miyar sai a makwabta.

Tagomashi da Tsawon Rayuwa

A ka’idar da masu littafin Red Book suka bayar a farkon lamari, sun nuna cewa kowane Faifan CD na iya tsawon rayuwa, muddin ya samu wajen ajiya mai kyau, aka kuma kera shi da gasasshen roba mai inganci, tare da yin amfani da na’urar shigar da bayanai mai inganci. To amma da aka fara amfani da Faya-Fayen CD musamman masu dauke da bayanai da wakoki, bincike ya nuna cewa mafi tsawon rayuwar da Faya-Fayen CD ke yi ba su wuce wata goma sha takwas, wato shekara daya da rabi ke nan. Babban dalilin da ke haddasa wannan gajeren ajali da Faya-Fayen CD ke yi shi ne dayan abubuwa uku. Na farko, yawan amfani da shi a kai-a kai, babu kakkautawa. Muddin ana yawaita amfani da shi a kullum, to dole inganci da tagomashinsa za su ragu. Wannan ke sa ya kasa rayuwa tsawon lokaci.

Abu na biyu kuma shi ne samuwar datti musamman sanadiyyar wajen ajiya mara tsabta da ake ajiye shi a ciki.  Wannan shi ma yana tasiri wajen rage masa inganci da tsawon rayuwa.  Sai abu na uku, wato samuwar kwarzane ko karta ko kuma guga a fuskar faifan da ke dauke da bayanan. Wannan kwarzane ko karta na iya yin tasiri matuka wajen toshe wadannan “ramuka” da “tuddai” da ke dauke da bayanan, masu taimaka wa na’urar CD kaiwa gare su don sarrafa su. Samuwar sannan kwarzane ko karta shi ake kira CD Rot ko Laser Rot a Turancin fasaha.  Kuma wannan ke sa ka rika ganin Faifan CD na karairaya (Cracking) a yayin da na’urar ke sarrafa shi; ba ya nuna hoto ko jiyar da mai sauraro abin da ke ciki yadda ya kamata ko yake a lokacin da yake sabo.

Nau’ukan Faifan CD

Kamar yadda bayanai suka gabata a farko, akwai nau’ukan Faya-Fayen CD da dama, wadanda mai  karatu ya sani da ma wadanda bai san su ba. Shahararru daga cikinsu su ne nau’in Audio CDs, wadanda ke dauke da wakoki zalla. Kuma su ne asali dangane da abin da ya shafi Faifan CD a duniya. Ma’ana su aka fara kirkira, tare da yadawa a duniya. Su ne har wa yau suka kashe wa faya-fayen Garmaho kasuwa, saboda tasiri da kuma saukin mu’amalarsu. Amma, kamar yadda mai karatu ya gani a baya, bayyanar na’urar sauraron waka mai suna iPod, ko MP3 ya kashe wa wannan nau’in Faifan CD kasuwa shi ma. Hakan kuwa ya fi bayyana a kasashen Turai da sauran kasashen Yammacin duniya, inda sauraren waka ya zama ruwan dare; kamar cin abinci.

Nau’i na gaba shi ne nau’in Bideo CD, wanda ke dauke da hotuna masu motsi, ko fina-finai ko kuma laccoci da dai sauransu. Wannan nau’i ya yi tasiri sosai shi ma wajen kashe wa kaset-kaset na bidiyo (wato BHS) kasuwa a duniya, musamman kan abin da ya shafi fina-finai da wasannin kwaikwayo. Daga nan kuma sai nau’in CD-ROM, wanda ake amfani da shi wajen taskance manhajojin kwamfuta don sarrafa su a cikin kwamfutar; ko dai don sanya masarrafai ko kuma babbar manhajar kwamfuta ta Windows. Su ma musamman ake kero su tare da bayanan da suke dauke da su. Wannan nau’i ya samo asali ne daidai lokacin da harkar fasahar kwamfuta da sarrafa bayanai ke habaka a duniya. Idan aka shigar da bayanai cikinsu shi ke nan, ba a iya sauyawa ko goge abin da ke ciki don kari ko ragi. Wannan ya sa ake kiransu CD-ROM.  Ma’anar ROM a lafazance shi ne: Read Only Memory.

Akwai kuma nau’in Photo CD, wanda kamar albam ne; kunshe da hotuna a ciki. Akwai kanana da kuma matsakaita. Sai kuma nau’in CD-R, ko kuma CD Recordable, wanda asali yana zuwa holokonsa ne; babu komai a ciki. Ire-iren wadannan nau’ukan faya-fayen an kera su ne don taskance bayanai ko manhajojin kwamfuta a cikinsu, ta yadda idan aka shigar a karon farko, to ba a iya sauyawa ko kara wani abu kan abin da aka sa. CD-R nau’i ne na musamman da masana suka kiyasta cewa idan har aka adana su da kyau, ta hanyar da ta dace, suna iya yin shekara ashirin zuwa dari ana amfani da su. Amma idan ba su samu wannan gata ba, watanni goma sha takwas galibinsu ke yi ana amfani da su, sai su lalace sanadiyyar karta ko kwarzane da suke samu ko kuma kwayar cutar kwamfuta da ka iya bata nau’in bayanan da ke dauke cikinsu. Nau’i na karshe kuma su ne nau’in da ake iya sanya bayanai a cikinsu, a kuma goge, don sake zuba wani. Ma’ana, kana iya zuba bayanai iya gwargwadon hali, ka goge ko kuma kara wani abu a kai. Wannan nau’i shi ake kira CD-RW (CD Rewritable); akasin CD Recordable ke nan. Bincike ya nuna akwai bambancin tsari da sinadaran da ake lullube kowanne daga cikinsu da shi. Wannan kuwa a fili yake, musamman idan muka yi la’akari da irin bambancin da ke tsakanin faya-fayan biyu na abin da ya shafi tsarin shigar da bayanai ko fitarwa ko karawa. Faya-Fayen CD nau’ukan CD-R da CD-RW sun yi tasiri sosai wajen kashe wa ma’adanar bayanai nau’in Floppy Disk da Zip Diskette kasuwa a duniya. Domin an wayi gari kusan kashi tamanin cikin dari na masu amfani da kwamfuta sun koma amfani da su wajen taskance bayanai da manhajojin kwamfuta a cikinsu, saboda girman mizani da saukin farashi da suke da su. Duk da yake su ma kasuwarsu ta fara yin kwantai saboda samuwar ma’adanar bayanai nau’in Flash Disk da kuma Edternal Hard Dribe da suka dara su inganci da amanar rike bayanai ba tare da matsala ba, su ma a farashi mai sauki.

Idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, za mu shiga bayani kan abin da ya shafi nau’in Faifan DBD. A ci gaba da kasancewa tare da mu.