Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Tsaro: Jami’an DSS sun kama Malami akan ya soki Gwamnati a Katsina

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kama malamin addinin musulumci a Katsina Malam Aminu Usman wanda aka fi sani da `Abu Amar` da ke tafsir a Masallaci cikin garin Katsina a jiya Talata.

Wasu rahotanni na cewa kamun malamin da jami’an DSS suka nada nasaba da hudubar sallar Jumu’ar da ya gabatar ya yi, inda ya kalubalanci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari akan matsalar tabarbarewar tsaro a wannan lokacin na mulkinsa.

ADVERTISEMENT

Jami’an sun kira malamin ne zuwa ofishin su na jihar, inda yaje ofishin tare da abokinsa Malam Shamsu ana gab da shan ruwa a jiya Talata.

Bayan zuwansu tare a ofishin sai jami’an DSS suka ce wa Malam Shamsu ya kama gabansa, sai suka tsare Malam Aminu Usman a cikin ofis

ADVERTISEMENT