Da Dumi Dumi

Tsaro ya ci gaba da samun kaso mafi tsoka a kasafi •Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan 4.9

Sashin tsaro ya sake samun kaso mafi tsoka a kasafin kudin badi kamar yadda yake kunshe as cikin kasafin da Gwamnatin Tarayya ta mika wa majalisar a ranar Alhamis din makon jiya.
Wannan ne shekara ta uku a jeri da tsaro ke samun kaso mafi tsoka a kasafin kudin kasar nan.
Ministar Kudi Ngozi Okonjo-Iweala ce ta gabatar ga zaure biyu na Majalisar Dokoki ta kasa a madadin Shugaban kasa wanda bai bayyana dalilin rashin kai kasafin da kansa ba.
Kimanin Naira tiriliyan daya da biliyan 100 da ke wakiltar kashi 27 cikin 100 na kasafin za su tafi ga manyan ayyuka ne yayin Naira tiriliyan biyu da biliyan 430 za su tafi wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.
Sauran za su tafi ne ga biyan basussuka, ya yi da aka yi kiyasin za a kashe  Naira biliyan 268 da miliyan 400 kan shirin rage radadin karin kudin mai (SURE-P).
Gwamnatin tana sa ran samun kudin shiga da ya kai Naira tirilyan uku da biliyan 730, yayin da gibin da za a samu a kasafin ya tsaya kan kashi daya da digo tara inda ya gusa gaba kadan daga kashi daya da digo takwas.
Bisa kiyasain da Ministar ta gabatar kason harkokin yau da kullum na sashin tsaro (da ya kunshi sojan kasa da na sama da na ruwa) ya samu Naira biliyan 306, yayin da na ’yan sanda ya kai Naira biliyan 286, sai ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Naira biliyan 67, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida Naira biliyan 145 sai Ma’aikatar Harkokin ’Yan sanda Naira biliyan hudu da rabi. Sannan akwai Naira biliyan 36 da za a kashe kan wasu ayyukan gaggawa da na cikin gidan soja.
 bangaren ilimi ne ya zo na biyu a kasafin na bana inda a bangaren ayyukan yau da kullum ya samu Naira biliyan 373 da miliyan 400. Sai Ma’aikata Ayyuka Naira biliyan 28 da rabi; Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur Naira biliyyan 55 da miliyan 700, Kimiyya da kere-kere Naira biliyan 24, Wutar Lantarki Naira biliyan uku da miliyan 900 yayin da ta Shari’a ta tashi da Naira biliyan 19 da miliyan 400.
Sauran su ne Ma’aikatar Watsa Labarai Naira biliyan 22 da miliyan 400, sai ta Harkokin Waje Naira biliyan 46 da rabi, Aikin Gona Naira biliyan 31 da miliyan 400  Ma’aikatar Ruwa Naiar biliyan bakwai da miliyan 700 sai ta bunkasa jin dadin matasa Naira biliyan 75 da miliyan 900.
Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya an kasafta masa Naira biliyan 45 da miliyan 200, sai Ma’aikatar kasa da Gidaje Naira biliyan biyar da miliyan 600, sai ta Makamashi da karafa Naira biliyan 10 da miliyan 600 ta Sufurin Jiragen Sama Naira biliyan shida ta Kudi Naira biliyan 216 da miliyan 400.
Fadar Shugababn kasa za ta kashe Naira biliyan 25, Taron kasa da za a gudanar zai lashe Naiar biliyan 7, kula da tsofaffin ’yan ta’addan Neja-Delta dubu 30 zai lashe Naira biliyan 35.
Da take magana da manema labarai bayan mikka kasafin mai taken: “Kasafin Ayyuka da Ci gaba.” Minista Iweala ta ce kasafin zai kara bunkasa aikin gonad a kara azama ga harkokin samar da gidaje domin kara samar da ayyukan yi, kuma an tsara shi yadda zai karfafa gwiwar masana’antu saboda za a samar da ayyukan yi a wurin.
Ministar Kudin ta samu rakiyyar takwarorinta ministoci da suka hada da Labaran Maku (Labarai) da Idris Umar (Sufuri) da Sarah Ochekpe (Albarkatun Ruwa) da Omobola Johnson (Sadarwa) da Chinedu Nebo (Wutar Lantarki) da Olajumoke Akinjide (Minista a Birnin Tarayya) da Darakta Janar na ofishin kasafi Brigth Okogwu.
Ana sa ran ‘’yan majalisun biyu su yi amfani da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara wajen nazartar kasafin inda za su fara daddale shi bayan dawowa daga hutun a ranar 14 ga Janairu mai zuwa.

Share