Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Tsawa ta kashe masu garkuwa da mutane 18

‘yan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Tsawa ta kashe masu garkuwa da mutane 18

‘Yan Sanda a jihar Adamawa sun tabbatar cewa tsawa ta kashe masu garkuwa 18 a Jamhuriyar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta tabbtar da hakan ne yayin karyata rahotannin da ke cewa tsawar ta kashe masu garkuwa da mutanen ne a Karamar Hukumar Tungo da ke jihar.

“Abin ya faru ne a jejin Pawati a Jamhuriyar Kamaru. Babu wani abu kamar haka da ya faru a fadin Tungo kamar yadda ake rade-radi”,  a cewar SDP Suleiman Yahaya Nguroje.

DSP Suleiman wanda shi ne Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda a Adamwa ya ce rufe iyaka da aka yi tsawon lokaci ya hana bata-gari tsallakowa zuwa jihar ta Adamawa.

Ya kuma bukaci jama’a su yi watsi da rahoton da ke cewa a Tungo tsawar ta kashe masu garkuwa da mutanen.

Karamar Hukumar Tungo da ke jihar Adamawa a Najeriya ta yi iyaka da Jamhuriyar Kamaru.