Da Dumi Dumi

Tsayar da 12 ga Yuni Ranar Dimokuradiyya ya dace – Bishir Yakubu

Bishir Yakubu
Bishir Yakubu

Daya daga cikin masu ruwa-da-tsaki a Jam’iyyar APC a Mazabar Wakilin Kudu I a Karamar Hukumar Katsina, Alhaji Bishir Yakubu ya ce tsayar da Ranar 12 ga Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya ta kasa ya dace da manufar jam’iyyar ta kara sa fahimtar juna a tsakanin al’ummar sassan Najeriya.

Kuma dan siyasar ya nuna gamsuwarsa kan yadda Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yake tafiyar da al’amuran siyasa da mulki, musamman yadda ya kawo sasanci da zaman lafiya a tsakanin mambobin Jam’iyyar APC a jihar baki daya.

Bishir ya bayyana haka ne a takardar sanarwar manema labarai da ya rattaba wa hannu, inda ya ce kyakkyawar akidar Gwamnatin APC a tarayya ta tafiya da kowa kafada-da-kafada daidai take da yadda Gwamna Aminu Masari ke jawo kowane dan siyasa daga kowane bangare na jihar domin tafiya tare da nufin ci gaban jihar da hada kan al’umma.

Ya ce kowane bangare na Najeriya yana da muhimmanci wajen kyautata ci gaban siyasar kasar nan ta fuskar samar da hadin kai da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali, domin ci gaban kasa.

Alhaji Bishir Yakubu ya ce kyakkyawan hangen nesan Gwamna Masari ne ya sanya ’yan siyasa daga kowace jam’iyya a Jihar Katsina suke ta canja sheka zuwa Jam’iyyar APC tun daga shekarar 2015 zuwa yau.

ADVERTISEMENT

“Ina kira ga ’ya’yan jam’iyyar da sauran ’yan Najeriya su ci gaba da yin addu’o’i, domin samun zaman lafiya mai dorewa da zai kawo ci gaban tattalin arziki da bunkasa harkar noma da kiwo da ilimi da tsaro da kuma samar da ababen more rayuwa,” inji shi.

Jigon na APC ya sha alwashin ci gaba da ba da gudummawa da goyon baya ga jam’iyyar a dukkan matakai, domin bunkasa rayuwar ’yan Najeriya da ci gaban kasa. Ya yi fatar cewa kwalliya za ta biya kudin sabulu ta fuskar kokarin da ake yi na inganta martabar kasar nan ta kowane fanni.

Share