Search
Subscribe
Tsige Trump: Jami’in diflomasiyyar Amurka ya bayar da shaida a majalisa

Tsige Trump: Jami’in diflomasiyyar Amurka ya bayar da shaida a majalisa

Wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka a Ukraine, ya fada wa ’yan Majalisar Wakilan kasar cewa, an sanar da shi cewa fadar gwamnatin Amurka ta White House, ba za ta saki wasu kudaden tallafin kayayyakin soji ga kasar Ukraine ba, har sai ita Ukraine din ta fito fili ta yi alkawarin cewa za ta binciki ’ya’yan Jam’iyyar Democrat da iyalan tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden.

Mukaddashin Jakadan Amurka a Ukraine, Ambasada William B. Taylor, ya bayyana haka ne yayin da yake ba da shaida cikin sirri a zaman binciken da majalisar ke yi, wanda ke duba yiwuwar tsige Shugaba Trump, shaidar da ta yi karo da ikirarin da Shugaba Trump ya yi cewa, babu batun cude-ni-in-cude-ka a tsakaninsa da Ukraine.

Taylor ya kara nanata matsayinsa cewa, ‘babu hankali’ a matakin da aka dauka na rike kudaden tallafin, wanda Ukraine ke matukar bukata.

Shi dai Shugaba Trump ya musanta aikata ba daidai ba kan zarginsa da ake yi cewa ya nemi Ukraine ta binciki abokan hamayyarsa musamman Hunter Biden, dan tsohon Mataimakin Shugaban Amurka kan rawar da ya taka a wani kamfani da ya yi aiki da shi mai suna Burisma a kasar  Ukraine.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin