✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsige Trump: Lauyoyinsa sun gama gabatar da hujjojinsu

Lauyoyin da ke kare Shugaban Amurka Donald Trump, sun kammala gabatar da hujjojinsu, a zaman sauraron batun tsige Shugaban na Amurka da ake yi a…

Lauyoyin da ke kare Shugaban Amurka Donald Trump, sun kammala gabatar da hujjojinsu, a zaman sauraron batun tsige Shugaban na Amurka da ake yi a Majalisar Dattawan kasar.

Hakan na zuwa ne yayin da batun da ko za a yarda a saurari bahasin shaidu a yayin wannan zama ke dada karfi.

Ayarin lauyoyin da ke kare Shugaba Trump, ya kwashe tsawon lokaci yana ta zargin ’yan Jam’iyyar Democrat da amfani da tsigewa, a matsayin wani makami na kawar da wani Shugaban Kasa da ba sa kauna.

Kenneth Starr, wani dan ayarin lauyoyin da ke kare Shugaban Kasar, ya ce tsigewa ta zama tamkar makamin siyasa da jam’iyyu ke amfani da shi kan juna.

Ya ce ’ya’yan Jam’iyyar Democrat a Majalisar Wakilai sun tsige Trump ba tare da goyon bayan dukkan bangarori ba.

Starr lauya ne mai zaman kansa, wanda binciken da ya yi ya kai ga tsige Shugaba Bill Clinton a 1998 saboda karyar da ya shara wa masu taya alkali yanke hukunci a batun lalatarsa.

A wani labarin kuma Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta karyata wani labarin da Jaridar New York Times ta wallafa cewa tsohon mai bayar da shawara kan tsaro John Bolton da Attoni Janar William Barr sun nuna damuwa game da yanayin Shugaba Trump da kuma alamomin da ke nuna cewa yana alfarma wa shugabannin China da Turkiyya.

“Sam babu wata tattaunawar da aka yi game da ‘alfarma ga wani’ ko ‘kokarin sa baki,’ a binciken da ake yi, kuma babu inda Attoni Janar Barr ya ce tattaunawar da Shugaban Kasa ke yi da shugabannin kasashen waje bai dace ba,” inji mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’ar, Kerri Kupec a wani sakon Twitter da ya tura.

Jaridar Times ta kafa hujjar labarinta ce da bayanan da wadansu mutane suka yi kan abin da littafin da Bolton ke shirin kaddamar wa ya kunsa.